Sashe 34
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko nace ya afku ga gidanmu kaddaran Da bamu isa mu guje mata ba,..Gaddaran Datayi Sanadin da muka Rasa komai namu Kaddaran Dayasa muka bar komai namu muka zo nan muna Rayuwa inda bamu da kowa.. Watarana ce da Zukata da gangar Jiki bazata Taba Mantawa Dashi ba,Baffa Kabiru ne ya samu Hatsari Daga Garin Abuja zai je Dukku bai ma yi Nisa ba saosai al"amarin ya Faru aka Dawo Dashi Specialist Dake Abuja aka Bashi Taimakon gaggawa Jikin nashi Da Sauki ba karaya sai dai Yaji Ciwo Kadan kadan Motarsa ne tayi Dameji bama Zata taahi ba Hankalu suka Tashi Kwarai Abba da Anni Ranar basu Iya barci ba Abba Sai Mtsawa yake a samu Buking din Jirgi Zuwa Abuja,Allahu akbar Allah Sarki Rayuwa Nura Shi yaje Filin Jirgi yayi Cuku Cukun komai,Allah ya Rubuta Lokacin Abba aduniya Bai kare ba wani Taron Malamai ya Tsaidashi,Ni kuma A wajen aiki ba"a barni ba Imran kuma Bama wanda yabi ta kansa Sanin Halinsa Ganin haka yasa Abba yace Nura da Anni da Salima da Asma"u su Farayin gaba Kafin mu muzo Daga Baya Tunda Lokacin Munari suna Jarabawa a makaranta,Abba kuma Zai Tsaya Taron su na Malamai sai Zuwa Gobe in sun gama Ni dashi Zamu Bi Jirgi zuwa Abuja muje mu Duba Baffa Kabiru Tunda Duka yan"uwa sun isa Chan Abuja. Har yau bazan manta da wannan Ranar ba Imran Tun bakwai na Safe ya Fita Zuwa Wajen aikinsa Munari na makaranta Ni Abba yasa na kai Su Anni da Nura da Asma"u da Salima Filin Jirgi na Murtala Muhammed ban kuma bar Wajen ba sai da Jirgin su ya Tashi ya Lula Sararin Samaniya. Na Dade tsaye Afilin jirgin bayan Tashinsy Na kasa Shiga Mota na koma Wajen aikina Haka kurum nake jin kaina wani iri kamar Wani abu Zai Faru Dani ashe ashe kuwa hakane Na koma Office na kasa Tabuka komai ko Cikakken Minti Talatin banyi ba Wayar Abba ta Shigomin ina Dagawa Naji Abba Cikij karaji yana Tambayana Jirgin su Anni ne ya tashi Minti Talatin da yawuce..!? Ni kaina na Rude bansan ina kaina yake ba Cikin Rudewa nace ma Abba Eh Sune Daganan ban ji komai ba sai karar Faduwar Abu naji Da Hayaniya Daganan naji Shuru Hankalina ya Tashi na Fito Jikina narawa anan naji Labarin Dayayi barazanar Tafiya da Numfashina Wai Jirgin Airic Daya Tashi Daga Filin Jirgin Murtala Muhammed Daga Lagos Zuwa Abuja Minti Talatin da suka Wuce ya Fadi a wani Daji Bayan ya bar Lagos. News na gani a Tv Dake ma"ikatan mu...! Yusuf yana kawo nan ya Saki kuka mai karfi Safiya ma Tuni Ta Fashe da kukan Cikin kukan Take Fadin"innalillahi Wa"inna Ilaihirraju"un..Daman yan Gidan ku na Cikin wannan Hadarin Jirgin Daya Cinye Rayuwanka Yan arewa Da yawa..!? Yusuf na Kuka yace"Da yan gidanmu Safiya..Da Anni da Nura da Salima da Asma"u Sun konee kurmus ko gawansu bamu gani ba kawai nidai na Farkane na ganni a asibiti Imran na Gefena yana ta kuka Kukan Da Tunda nake dashi ban Taba ganinsa yayi kuka ba,ina mikewa na Fara Tambayansa ina Abba sai dai bai min mgana ba ya Nunamin Abba Dake gefena Kwance Shima anamai karin Ruwa,Safiya bazan Tsaya baki Labaein Irin Tashin Hankalin da Muka Tsinci kanmu aciki,Abba ya Farka yana kuka yana Fizge Fizge yana Kiran sunan Anni da Nura da Asma"u da Salima Likitoci sun kasa Controlling dinsa Bamu da wani kwarin Gwiwa Domin Rashin da mukayi Babba ne wanda Babu Wani Abunda zai iya maida wannan Gibin. Ni da kaina na kira Wayar Baffa Mustpaha na Sanar dashi ina kuka Chan ma Hankula suka taahi Domin Gabadaya Hadarin Jirgi a Karade kasa Tunda Yawanci Duk yan arewa ne da Wasu manya a gwannati. Dagani Har Imran bamu kwana agidanmu ba Ni naje makaranrar su Munari na Daukota muka Koma asibiti muka Hada kai mu uku muna kuka Tun Munari bata gane Har ta Fahimta nan muka kwana da Abba asibiti,washegari kuma Baffa Mustpha da Baffa Kabiru Da ciwon da komai ya tashi ya Taho,sun same mu Cikin Wani Hali,Abbanmu kuma ya Fara Fita Daga Hayyacinsa Batare da Shawara damu ba suka Gama Cuku Cukunsu sukayimana Bukking din Flight Bayan sun karbi Report din Abba na asibiti din Abba Suka Tarkatamu Zuwa Gida muka Debo kayanmi Harda na Abba Dana munari Suka Tasamu agaba Sai Filin Jirgi Duk da Tsorata da Hawa Jirgi daya shiga Ranmu Hakanan muka Shiga bazan manta ba sai da Imran ya Suma Saboda Firgita. Daga Lagos Gombe muka Sauka Mijin Goggo Bintalo yazo ya kwashemu sai Dukku Gidan Daada koda muka isa Gida ya Cika da Dangi ana ta Koke koke Daada Tayi kuka kamar Idanuwanta Zasu Makamce,anan akayi karban Gaisuwa Har akayi Sadakan Bakwai Abba Baya Cikin Hankakinsa sai sambatu da Surutai,Mukan mu gamu nan kawai ammh Komai ya Fita kanmu da Rayuwarmu Gabadaya Bama da Wani Tunani sai abunda aka Fadamana Tunanin mu da komai ya Tsaya Cak.Har gwarani akan Imran da Munari ana ganin kamar bai Damu da Danginsa ba Ashe ashe abun sai yafi Tabasa Fiye da kowa. Saboda Halin da Abba yake Ciki yasa bamy koma Gida ba muna Dukku gaban Daada sai dai duk Sati Baffa Kabiru da Baffa Mustpaha suna Hanyar Zuwa ganin Abba ya Kamu da Cutar nan ta Depression yasa Suka Daukesa suka kaisa asibiti aka Dubasa aka bashi mgunguna da Shawarwari da Farko Abun kamar yayi aiki Daga Baya sai Abba ya Kara Rikicewa Bawanda zai Fahimci Halin da Abbanmu ke Ciki sai mu da muka Dandanin Zafin Abun,Shiyasa cikin Yan"uwan Abba suka kasa mai Uzuri Ballatana su Fahimci Wani Hali yake Ciki basu Taba Dadanin Zafin Rashin Daya Dandana bane Shiyasa suka Fara ganin Laifinsa suna Fadin bai da Takwalli ne Dagashi har mu da kullum bamu da aiki sai mu tasaahi muna kuka ai ba kanmu Farau Mutuwa da Rashi ba Anni da Asma"u da Salima da Nura Sun Tafi kenan har Abada bazasu Taba Dawowa ba..Daada ce Kadai ta Fahimci Halin da Abbanmu da mu kanmu muke Ciki Baffa Kabiru yafi kowa Daukan Zafi Daga Karshe sai ya Zare hannunsa kan Abbanmu Tunda Likita yace Mgani baya aiki Tunda Abba bai Rage Damuwa ba kuma yaki ya manta da Abunda ya Faru Dashi..? taya zamu manta da wannan Rashin..? Ai har Abada Gidanmu ya Shiga kuncin da Bazamu Taba Fita acikinsa ba. Tun bamu gane ba Har muka gane irin Yadda yan"uwan Abba ke kallonsa a Saboda Rashin Takwalli Ya koma Mahaukaci bashi da aiki sai Sambatu,Mukuma ya"yansa mu Bar komai nami mun dawo muna Rayuwar kawai Saboda Baffa Kabiru yayi yayi Dani da Imran mu koma Lagos Saboda aikin mu muka ki..Imran ya Nunamai Aduniya Bamu da wani abunda ya Ragemana Bayan Abba Saboda Haka ba inda Zamu muna Tare Dashi Dalilin haka yasa muka kusa Wata Shidda a Dukku,ayyukan mu Duka sun Tsaya an gaji da kiranmu an kyalemu,Munari Tuni Karatunta ya Tsaya Cak itama Bata da wani Sauran abunda Zata Dora. Ni ban yi Tunanin Dauke Abba mu bar Dukku ba Imu ne ya kawo mana Wannan Tunanin Tun Lokacin Daya iske su Baffa Kabiru sun Tarun ma Abba suna ta mai Fadan yaki ya yarda da Kaddara ya Dawo Daidai ya Zauna yana Biyemana yana kwana kuka Mutuwa ce Dayace kuma wanda ya Mutu baya Dawowa Abba na kuka bayacewa komai Domin alokacin basu san Dacin Dayake ji ba Daada ma kukan Take ammh sun kasa Fahimtarsa,Suna cewa ya zama Mahaukacin karfi Dayaji kamar ba Musulmi ba,Baffa Mustapha baya mgana sai Baffa Kabiru yafi kowa Zakewa wannan Dalili yasa Imran ya mtsamin kan muce Zamu Tafi da Abba Lagos muje Chan muka Cigaba da aikin mu muna kula Dashi..Abun mamaki da muka Furta Daada ce kadai tayi musu ammh Banda Sauran yan"uwan Abba nan da suka amince acewarsu kila zai fi Samun Sauki batare da Rakiyan kowa ba Muka bar Dukku Zuwa Lagos,a mota muka Yi Tafiyar Domin Tun Abunda ya Faru Har Abada muka Tsani Jirgi. Mun Dawo Gidanmu na Lagos da Zama sai dai Babu abunda ya Sauya Nidai ban koma bakin aikina ba Hakama Imran,Ballatana mu kokarta mu maida Munari makaranta Duk wani Farincikin Gidanmu sai ya Gushe sai kunci da Bakinciki Abba koda yaushe yana Daki yana kuka yana Samabtu mu kanmu bamu da Wata natsuwa. Bayan Dawowarmu da Wata Daya Baffa Kabiru ya zo ganin mu Cikin Wannan Halin ya kara Bata ransa yayi ta Zaginmu yana mana Fada Abbanmu kuwa kamar ya Dakesa Daga karshe yace yaje yayi ta Haukansa In ya Haukace ni da Imran sai mu kaisa Gidan Mahaukata ko Zama bai yi ba ya Juya shima zuwan da yayi Daada ce ta matsamai yazo ya Dubamu. Awannan Ranar Ran Imu ya baci ya Fita,Fitan da bai Dawo ba sai da ya kwana Biyu yana Dawowa na gansa ya iya Busa Sigari,shi kuma ya ce Dole ne muyi Nisa da Komai namu in muna so mu Cigaba da Zama Lafiya Inda ba wanda yasan Labarin Gidanmu Ballatana akira Abbanmu da Mahaukaci muyi nisa da komai nanu asali,Nasaba Dukiya aiki da Komai na Rayuwa Ni kuma na amince Domin Lokacin na Fara Tsorata da komai kada Imu ya Fada wani Hanyar Banza. Bamu saida komai namu ba Gida Motoci Duka suna Lagos sai dai mun kai Takardan Barin aiki Daga Ma"aikatanmu da Muke aiki sai muka Tattara kudi Katin bankin mu Dana Abba dana Nura dana Asma"u da Takardun makarantarmu Dana Munari sai kayan sawanmu,muka Diba iya wanda Zamu iya muka Baro Lagos Bayan mun Sallami mai Gadi mun kulle Gidanmu bamu ma Tunanin Zamu Dwo Watarana ba sai Domin yin hakan Shine Mafitarmu Mun Taho da Abba Kano bai Cikin Hayyacinsa a Hotel muka Sauka Ni na Fita Na Bincikamana Gida Cikin kwana Biyu muka kara mallakan Wani gidan,Shine wanda muke Ciki,Muka Tattaro muka Dawo Domin Gina wata Sabuwar Rayuwa Bayan mun bar Duka Layukan mu da Wayoyim mu a Lagos Da komai inda Za"a Same mu saboda bama Bukatar Taimaakon kowa Tunda ankasa Fahimtar,Radadin Dake Cikin Babban Rashin da mukayi. Ganin in na Zauna Haka Rayuwar Gidanmu Zata kara Lalacewa Cikin kunci,Sai na yanke Shawaran Fita Neman aiki Duk da bamu rasa komai ba Muna da Kudi,ammh ban Zauna ba Cikin ikon