← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 190

Sashe 96

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Murmusa tana Fadin"Nine baka san gani Imrana..! Jin muryan Daada yasa ya Dago kanta yana kallonta karaf suka Hada ido da Inteesar dake kallonsa Ido Cikin ido. Lamgwabe kanta tayi kamar zatayimai kuka Saurin dauke kansa yayi Lokaci Daya yana Mike Zaune yana Fadin"Daada..! Kafin Daada Tace wani abu Inteesar Tayi Saurin cewa"Daada ta damu baka ci komai ba Shine tazo da kanta..! Kura mata ido yayi yana kallonta Daga sama Har kasa sanye take da Doguwar riga mai Ruwan kasa Kirar Armani mai Roba ta dan manne mata ajiki sai ta saka Vail din Rigar ta yane kanta dashi Zuciyarsa taji tana Bugawa yasa yayi Saurin kauda kansa Kafin ya Zuro fararan kafafuwansa kasa ya Sauko Daga kan gadon ya isa ga Daada yana Fadin"Daada ai ba sai kin taso ba..bana jin cin komai shiyasa..! Daada tace"a"a kana jin yunwa sai dai in bazaka ci ba..Ko Tuwon ne baka so sai Maryama gatanan ta dafa maka wani abu ammh ai zama da yunwa bai da wani amfani Imrana..! Imran yasa mezai ce Inteesar ya kallah ta Dagamai gira Hararanta yayi kafin yace"Daada..! Bata bari yace wani abu ba tace"In baka son zama cikin mu sai ta kawo maka nan Dakin ba shikenan Damuwar ba..! Kansa ya shafa kafin yace"Zan ci muje Saboda ke Daada..! Taji dadin haka ta shafa kanshi Tana Fadin"Allah yayi maka albarka..! Ya amsa da Ameen yana kallon Inteesar dake danne Dariyarta Hade rai yayi yana Fadin"Ke..Dariya kikemin ko..? Yarinyar nan kin rainani saboda banta Sauya miki kamanni bane shiyasa..! Daada Tayi gaba bata jisu ba Inteesar tayi Raurau da ido kafin tace"Am sorry badakai nake yi ba..! Bai tsaya ce mata wani abu ba ya Nuna mata Hanya da Hannunsa Dole ta wuce sum sum shi kuma yabiyo bayanta Duk Takunta yana Kallonta kamar kuma da Zuciyarsa take Tafiya Har zuwa Falon Daada. Suna Fitowa kowa ya Dago yana kallonsa Shifa ya Tsani kallo wani Lokaci Fuskar nan ya Hade ba Fara"a su Abba kadai yace ma sannunku sai Inna Maimunatu Inna Bintalo baima Lura da ita ba yasa bai gaisheta ba Yana Shirin karisawa Kusa da Daada ya Zauna yaji Tana Fadin"Ni kuma Kashi nayi maka agado da ko sannun bansamu ba..! Shifa bai ma zata dashi take ba yazauna kusa Daada yana dan Wurga Idanuwansa,Yaji Abba yace"Imran ka gaida Goggonka Binta gatanan..! Yafada yana nunata Sai Lokacin ya Dago yama kalleta Wani Kallo ta sakarmai shi kuma yayo mata kallon Kyahuwa..,? Irin to me ya Hadasu da zata mai wannan kallon Dakyar ya iya ce mata Sannu goggo..! Ta Bude baki zatayi mgana Daddy ya Dakatar da ita da Fadin"Badai ya gaisheki ba..? Ku rika kama Girmamku Binta wadanan yaran fa Kamar ya"yanku suke..!. Jim haka yasa tayi Shuru bata da tacewa Shiko Imran ko ajikinsa. Daada tace munari ta sakamai Tuwon bai yi mgana ba ya Nannade Hannun Jallabiyan Jikinsa ya saka Hannun a Filet din Daada ya Debo Tuwon yakai Bakinsa da Bismillah kowa da mamaki yake kallonsa barin ma Abba da Ya Yusuf da Sagir da Munari da Inteesar sai dai bamai San sunayi ba Ya hade ransa ya cigaba da cin Tuwonsa Daada Ranta Fes tana kallonsa Tana Sakin Mirmishi Aranta Imran in ya Gutsiro Tuwon sai ya Tura gaban Daada kamar wata yarinya haka ya dinga mata sai dai ta Dauka tace cikin Taruwar Hawaye tace"Allah yayi maka albarka Allah ya jikan Zuwaira..Kullum kukanta Daada Yaushe Imu zai sauyane..? Yayi kaza yayi kaza Baya son zama cikin yan"uwa yau data na Raye data zo ta ga Imranu yana cin Abinci kwano Daya Dani yana Gutsiromin Tuwo saboda yasan na Tsufa baya so na Wahala..,! Da karfi Tayi mganan dayasa kowa yajita sai aka koma ana kallonsu Cike da mamaki Abba Farinciki ya cikasa shi da Ya Yusuf Imran kuma baima Kalli kowa ba bai wani ci mai yawa ba ya Zare Hannunsa ya Mike Daada ta Kallesa Tana fadin"Har ka koshi kenan..? Kai ya gyada mata bai yi mgana ba ya Wuce zuwa Kitchen ya wanke hannu ya Dauko Ruwa Gora guda Daya yazo ya wuce ya koma Daki abunsa batare Dayace ma Kowa komai ba Daada sai Mirmishi take ita Kadai Mami Asma"u na Binta da Harara kasa kasa itafa bata Kaunar taga Daada na nuna ma wani Jika so da kulawa in ba ya"yanta ba akomai tafi so su kasance sune kan gaba da kowa.
Chapter 96 · 0% Book details