← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 190

Sashe 61

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washegari sai 10am suka shiga makaranta Shiyasa Ya Yusuf ya tafi ya barsu sai da suka fito Daga Lecture suna Hanya zasu masallaci Munari ta Kalli Inteesar data ganta Yau wanu iri bata da Kuzari kamar ko yaushe tace"Besty wai duk fushin ne... ? Am Sorry..Wlh am just kidding..!
Inteesar ta kalleta kawai batace komai ba Sai Munari Taji wani iri Riko Hannun Inteesar tayi yasa suka Dakata da Tafiya Munari ta kalleta Tana Fadin"Meke damun ki ne..?
Inteesar ta Saki Mirmishi kafin tace"Bafa komai..Kece wai kika bani mamaki kina wani ban hakuri..? To miye na ban hakuri..?
Munari tace"Ai naga jiya baki ji Dadin nganata bace kuma..!
Manta kawai..!
Inteesar ta Katseta Lokaci Daya tana jan Hannunta suka Cigaba da Tafiya Munari dai sai kallonta take tana Naxarinta ta Tabbata wani abu na Damun Inteesar Ta san ta Tana da Sakin jiki da wanda suka saba kuma Tana da Kuzari da kazar kazar ba kamar yau data ganta sai a Hankali ba
Ganin yadda Tayi ne yasa bata kara Tambayanta ba ammh Haka suka Wuni acikin makaranta Inteesar bata da Kuzari sai chan ne na ta Dan saki suka Fara Hira,
Abunda Munari bata gane bane Inteesar Tunanin Abunda ya Faru jiya yaki wucewa acikin Ranta,itama Har mafarkin abun ta Sake yi,wai gata Rumgume ajikin Imran sai abun ya Dameta sosai Tana ganin ya gama da ita ne Tunda ya Rumgumeta kuma abun da bata saba dashi ba Shiyaasa duk ya Sakarmata Jiki da kwarin zuciya.
Sai dai ta saka aranta bazata Kara yarda su hadu da Imran ba Domin ai Tunda ya Rungumeta yaji Tudun Nonuwanta ya gama da ita Har Abada.
Tun kuma Daga Ranar Inteesar ta Yanke duk wani Hanyar Haduwarta da Imran ta Rage shiga gidansu in zata Shiga kuma sai ta Tabbatar da Baya gida,In kuma ta Hangesa sai ta Boye kanta saboda Bata so ya ganta.
Imran daya Daina ganinta bai Damu ba Sai Daga baya sai ya fara jin ya Damu Saboda ya daina ganinta agidan kuma bazai tambayan Munari ba,Yana Tsoron kada ace ta Koma Gidansu ne,Ya ma rasa Dalilinsa na Wannan tsorom Ranar har kiran Sagir yayi yana Tambayansa Wannan yarinyar fa..?
Daman Sagir na jin Haushinsa a Gadarance yace mai"Wata yarinya kuma..!Rainin Wayau ne baya so Shiyasa ya Datse Kiran yana kara jin Haushin kansa me ye hadin da ita..! Da zai ji ya Damu Domin ya Daina ganinta da wannan Tunanin ya Watsar da komai shi kuma Sagir bai maida kai kan mganar Imran ba yana Tunanin wani Wulakancin nashi ne ya Tashi kan Inteesar shiyasa ya Nunamai bai ma Fahimcesa ba.
Sai dai mai Imran yaji Duk Duniya Fuskar Inteesar yake son gani Duk da ya gama Haddace Fuskarta Inda ya Iya zane zai iya Zama ya zana sai dai Haka nan yake son kara Kallon Fuskarta Kamar za"ayi mai gafara Dalilin haka ya koma Zuwa Shagon Sagir,wanda yaransa Har sun Fara Sakewa suna Murnan Takurarre ya Daina zuwa sai gashi Ranar kwatsam ya Dawo,Ai Ranar ba wani wanda yayi Wani Motsi mai Karfin Sanin Halinsa Mganarsa kamar yankan Takobi ne in yace Dole sai takai Sara ne.
Ba domin kowa ya dawo ba sai Domin Inteesar ya gama yanke ma kansa mganar Cewa Inteesar ba haka ta barsa ba indai ita ba Aljannah bace to Akwai wani abu akasa.
Taya ya haka kurum rana Tsaka Zai Dawo ba Wacce yake son gani sai ita a Baya yadda da ana cewa Ana ma Mutum asiri sai yanzu ya Fara Tunanin asiri tamai ya Zama Dole ya ganta ko yatambayeta Me yasa tamai asiri sai dai bai samu ganinta ba,Ko makaranta suka Dawo bata yarda ta Sauka ta Kofar Shagon Sagir sai takara Chan gaba in kuma a kafa suka Tako da Sauri take wuce wajen bata ma ko kallon Barayin Duk da tana ganin Imran din ammh shi baya ganinta,sai sau Daya kuma kafin ya yi wani yunkuri ta Shige shi kuma bazai iya Binta ba.
Ana cikin haka suka Fara Test basa Samun Lokaci domin suna gabda Fara Exams din Farkon Zangon Karatunsu.
Daddy yazo ya ganta Sau Daya shima amakaranta ya Bita bai gayamata zai zo ba,Kawai ya Kirata yace ta ina..?murna kamar Inteesar zata Shida aka kuma yi Rashin Sa"a Munari ta Shiga Masallacin yin Sallah ita kuma Inteesar sai bataje ba ta Zauna anan Department dinsu tana Duba littafanta Daddy ya kirata.
Ashe ma ya shigo Cikin makarantar yana Office din abokinsa Wani Daurin auran Yar abokin su da sukayi karatu Tare ya kawosa,chan taje ta samesa suka ga juna,bai wani Dade ba yace zai tafi Har Department dinsu suka Dawo Neman Munari bata ganta ba Ta Kira wayarta sai ta Tuna ai jakar na Munarin gata a Hannunta,Kuma har Masallacin taje akace mata ta Fito,Karshenta Dai Daddy tafiya yayi basu hadu da Munari ba sai bayan tafiyarsa ne ta ganta ashe itama Nemanta Takeyi kuma ba waya ballatana ta Kirata Cikin Rashin jin Dadin Inteesar ta Fadamata Zuwan Daddy da Tafiyarsa ta bata 5k din Dayace ta bata Ita kuma 15k ya bata 10k yace takai ma Mama Munari ta karba Tana ta Godiya Tare da Cizon Yatsan Rashin Ganin Daddy a Karo na Biyu.
Sati biyu da gama Test dinsu suka Fara Jarawabawarsu Cikin Kwarewa Dama Tuni sun shiryamata basu sha Wahalanta ba,Inteesar nata Murnan Zuwa Gida Kaduna yayinda Munari ke alhinin kewar Inteesar din.
Sai uku sukayi suna Jarabawa kafin su gama sun samu Hutun Sati uku kafin su Dawo su Dora a Karatun Zango na Biyun aji Daya
Aranar da suka gama Inteesar Kamar Zata Suma saboda Murna ta gama Hada kayanta Ya Basheer da Safe zai zo ya Tafi da ita.
Munari duk ta shiga Damuwa Saboda Tafiyan Inteesar din itama Tana jin Zatayi matukar kewar Munarin.
Bayan sun Rabu aranar Inteesar Tayi Tunamin ta bama Munari wani abun Da Zata Rika Tunawa da ita sai ta Dauki wani Dankunnen gold dinta mai Sarka da Zobe da awarwaro ta saka ajaka zata kaima Munari ba Domin bata dashi ba sai Domin Wani abun da Zata Rika Tunawa da ita in ta koma Kaduna itama Zataje Munarin ta bata wani abun da In ta koma Kaduna ta Kallah Zata rika ganinsa kamar Munarin.
Karfe 5pm tayi ma mama sallama ta Fito tana Sanye Cikin bakin Wando plazo da wata Riga Mai Dogon Hannu ammh Tana da dan Tsawo,sai ta Sanya Farin hijabinta mai Hannu wanda yakai mata Har Gwiwa.
Karamar Jakar data saka Dan kunnen aciki sai Kafarta Sanye cikin Takalmi Sahu Ciki Fari kalan na mata.
Tun fitowarta Gidan ya ganta Lokacin ya Fito Daga Shagon Sagir Karan Sigari rike a Hannunsa yana sha Gida Zai tafi Domin yagaji da Zaman sai ya ganta Tanufi Hanyar gidansu Gabansa sai da yya fadi,Tun bayan mganar Data Fadamai na ya Daina shan Taba Kowa yasan ya Rage shanta sai dai Yanayin Dayake ciki na bukatuwan son ganinta ya kara maidashi Ruwa..
Jikinsa har wani mazari yake Zuciyarsa na Ingizasa yabi bayanta Cikin Takunsa na Sasasarfa ya Taka mata Baya Kowani Dakika na Takunta Sai Zuciyarsa ta Buga,kawai ya gama Sakama Ransa yarinyar nan asiri tayimai kuma yau sai ya Shaketa ta gayamai inda ta Binne koma Menene taje ta Hakosa Imran yafi karfinta bama Itaba yafi karfin matan da suka Fita komai da komai da duk Abunda suke Takama.

*Janafty*
3/22/22, 23:06 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*🅿�23*
Chapter 61 · 0% Book details