Sashe 93
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
suka karisa inda su Abba ke tsaye suka gaishesu suka amsa cikin Sakin Fuska. Sannan suka juya suna gaida Mami Asma"u dake gefe tsaye tana Latsa wayarta tana kallon Mutane ta Cikin Siririn Gilashinta,Sama sama ta amsa musu ba wanda ya Damu da ita sanin Halinta. Aka Fara saka kaya acikin Mota Yusuf yayi Riverse da Motarsa,zuwa Inda Abba ke Tsaye yaci Shadda Fara Tazarce yayi shar dashi,Sadam daman Da safe yaje gida ya Dauko musu kaya nashi dana Aneesa da yara dukkansu sun Dauki Uzuri a wajen aikinsu yau sai Dukku. Awajen kowa ya hallara Imran ne kadai bai fito ba Abba ya yafito Yusuf da Hannu yana zuwa yace mai"Kira min Imran..! Yataka kenan zai koma cikin Gidan sai ga Imran ya fito Sanye cikin Riga da Wando baki da Fari na kamfanin DKNY,wandon baki ne yadan kamasa ta kasa sai wani katon bakin Booth din Takakmi sai Farar rigaraa mai kauri mai gajeren hannu Tana da Rubutu baki agaban rigan an saka GENTLY. kansa kuma yasha gyara Dadan nan ya Zauna Daram yana Sheki Fuskarsa ba Fara"a ko kadan kamar an aiko mai da sakon mutuwa Hannunsa sanye da agogon Fata,Bayansa Rataye da wata Jaka baka irin ta matafiya inda ya saka kayansa da Abunda zai bukata Tunda Umarnin Abba ne bai isa ya Taallake ba ammh ba domin shi ba ya Rantse har ga Allah bamai sakashi zuwa Dukku yau. Yusuf ya kalli Abba yana Fadin"Gama Imu din nan Abba..! Kai Abba ya gyada kafin ya juya yana kallonsa yana Tahowa Hannunsa Daya Cikin aljihun wandonsa Dayan kuma karamar wayarsace a hannu yana Dannawa ba Abba kadai dayake Dansa ba kowa awajen sai da ya tsaya yana kallon Imran koda yanayin Tafiyarsa zaka Fahimci shi din Namiji ne ballatana Cikar Zatinsa da Kwarjinsa na dabam ne. Inteesar dake tare da su Ya Basheer tana Rokonshi suna son zama amota Daya ita da Munari da Hafsah, bata san ta shagala da kallonsa ba sai da taji Basheer na fadamata to su shiga Motar Sadam shi zai tuka su Umma. Kana ta iya dawowa cikin Hayyacinta Tana Sauke Nunfashi. Imran kuwa gaban Abba ya karisa Ya gaishesu ina kwananku yace sau daya bai kara cewa komai ba ya Dauke kansa sama Daddy ne kadai ya amsa sai Abba ammh Baffa kabiru na gefe yana Waya.. Abba ya dafa kafadansa yana Fadin"me ka tsaya yi kaifa kadai muke jira..!? Imran yace"Abba Sagir nake jira..! Abba da Yusuf suka kallesa cikin mamakinsa Kafin Abba yace"Sagir kuma..? Kai ya gyada batare da yayi mgana ba suma basu ce komai ba sai Yusuf dayace"Ka kirasa zamu wuce ne..! Bai yi musu ba ya koma Gefe yana Kiran Sagir ta waya. Su kuma su yusuf suka fara tsara yadda Zaman Motan zai gudana. Abba da Daddy da Baffa Kabiru zasu shiga Motarsa Direbansa yajasu wanda ya kwana nan wajen Iro megadi. Sai Umma da Mami Asma"u zasu hau Motar Sa"id. Yusuf kuma zai Dauki Imran da Sagir,Sadam kuma zai Dauki Fareesatu da Aneesa da Safiya da yaransu sai Basheer zai dauki Su Inteesar. Kowa ya yarda da Tsarin banda Mami Asma"u data bata rai tafiso tayi tafiya Mota Daya da Mijinta sai dai bata samu Fuska ba Wajen Baffa Kabiru ko yaya naka yake ai naka ne tuni sun shige Mota shi da yan"uwansa Dole itama ta shiga Motar Sa"id gidan Baya Umma ta shiga gaba abunta. Imran bai shiga Mota ba sai da Sagir yazo kana ya yarda ya shiga gidan gaba Sagir ya shiga baya. Motan su Abba ce ta fara fita Daga gidan sai Motar su Umma sai ta Sadam sai ta Basheer sai ta Yusuf ta Karshe,Iro nata daga musu hannu da Fatan Allah ya kai lafiya. Da suka dawo sallar asuba Yusuf ke fadamai zasu yi tafiya na kwana Biyu kafin su dawo ya kula da gida yace bakomai Cikin gida kuwa daman sun kulle kulle ko"ina kafin su tafi. Sai da suka Dauki Hanya kana Baffa Kabiru ya kalli Abba yana Fadin"wanchan da naganshi Tare da Imran waye..? Abba yace"Sagir..?abokinsa ne..! Baffa Kabiru yace"Tafiyar ta Shafesa ne..!? Abba yace"Imran yace yazo yamai Rakiya..D'a na kowa ne ballatana Sagir ba bare bane na gida ne yaron wajen Yayar Salaha ne matar Mustapha Dalilinsune ma kuka san inda muke zaune..! Baffa Kabiru bai kara mgana ba Daga gani zuwan Sagir din bai mai Dadi ba Daddy dai da Abba suka cigaba da Tattauna mganarsu. Suna Hanya sun kusa shiga Gombe Inna Maimunatu ta Kira waya tace gasu fa a dukku koda ta iso ta iske Inna Bintalo da ya"yanta sun iso sun gama Gayama Daada Komai ga Daadan nan sai kuka take tana cewa Ta kosa taga Malami ko Hankalinta zai kwanta. Daddy yace ai gasu nan sun kusa isowa da yardan Allah har aka bama Daadan ya kara Lallashinta bai dai bama Abba Wayar ba yafiso suga juna Ido na ganin ido.