← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 190

Sashe 54

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inteesar da Munari na wucewa Imran ya Fito daga cikin Shagon Sagir ya Tsaya a kofar Shagon ya Fito da Sigari Guda Daya ya kunnata ya Cigaba da Zuka yana Fesar da Hayaki. Sagir ne ya Fito Daga Cikin Shagon Nashi Ya isa kusa da Imran yana Kallonsa Cikin Wani yanayi kafin ya Rausayar da kansa yana Fadin"Yau Kuma a waje ake son Busa Hayakin..? Imran bai ma nuna yasan da Wanzuwar Sagir a wajen ba Ya cigaba da Busa Hayakinsa,Sagir ya kara Kallonsa yana Gyada kai kawai. Har ya Fidda rai da zai bashi amsa sai yaji yace"Kawai yau naji ina son na Busata a waje ne..! Sagir yace"Dahaka kake yi da baka Takurama yaran Shago na ba..kasan dai Tun Fara zuwanka Shagon nan Kake Takura musu ko..? Imran ya wani Mele baki Lokaci Daya yana Sauyama Sigarin nasa Hannun Zama kafin yace"I know..! Sagir ya kallesa Cikin mamaki kafin yace"Ka sani kace..? Imran sai da ya Fesar da Hayakin Daya Busa kana ya Bude baki yace"To ni zan Hana Zuciyarsu yin Abunda Tagama Da Gangaar jikinsu ne..Ban isa na sa su soni ba..Ban isa na Saka musu Ra"ayina ba sai dai na Isa na Hana su yin Abunda ni zai zama Takura gareni..! Sagir na Shirin mgana Imran ya Katseshi da Fadin"Har da kaima ai na Lura kamar na Takura maka ko..? Sagir yace"Ai ni ba tun yanzu ba ka Dade kana Takura ma Rayuwata..! Imran ya tsaki karamin Tsaki yana Fadin"Halin Dan adam kenan yanzu da ban rika zuwa ba sai kace naki Karban mganarka yanzu kuma ina Zuwa kana neman gayamin mgana..! Yafada Cikin nuna jin Haushinsa Da Sauri Sagir yace"To daka karbi mganata Ka fara koyan Sana"an ne. ? Tunda ka Fara zuwa baka komai sai dai ka Zauna kana bin kowa da kallo in ka gaji ka Busa Hayaki gayamin me ka Koya..? Imran ya saki kayattacen Mirmishin da yakan Dade bai yisa ba Kafin ya bude baki yace"Waya Fadamaka ban fara koya ba..? Tun yaushe ai ma nayi nisa da Fara koyon Dinki! Sagir ya wani kalleshi a karkace kafin yace"Bangane ba..? Ta ina ka Fara Koyon..?me kuma ka Fara Koyan..? Imran yace"Abunda Kake koyama Mutane mana Inace ba yanka Dinki bane da Hawa keke da Dinkawa bane..? Sagir yayi Dariya yana Fadin"Sannu Mallam Riga maasllaci To ai ba Haka kaga kowa na Koyon Dinkim ba balle kace..! Imran yace"Ai ni sunana Imran..Kuma Dabam nake da kowa..Kaganni nan da Kwakwalwata nake Koyon Abu bana da Bukatar Rubutawa ko Gwaji..! Sagir ya kallesa kafin yace"Uhm..wai me ma ka karanta ne a makaranta..? Imran na kallon Sagir Cikin ido kafin yace"Daman na taba Fada maka nayi Karatu ne..? Sagir yace"Ko baka Fadamin ba yanayinka da Tsarinka na Masu Ilimi ne sai dai in baka son Fadamin..Dama nine na Daukeka Abokina kuma Dan"uwana kai baka Daukeni ba Imran..! Sagir ya Fada Cikin Wani yanayi Da Imran yaji wani iri,Baki ya Mele kafin ya Saki karan Sigarin Dake hannunsa Data kare,Ya saka Rufaffan Takalminsa ya Take ta Kafin ya Laluba Aljihun wandonsa ya Dauko Wata ya saka Lether ya kunnata Sagir Duk yana kallonsa Kai ya Girgiza kafin yace"Don Allah ka Rika Dagama Shan Sigarin nan kafa..Ba Saboda Komai ba sai Saboda Lafiyarka Imu.! Imran yayi kamar bai jisa ba sai da ya Busa Hayakin yaji sa ya ji Daidai kana ya Fesar da Hayakin har zuwa Fuskar Sagir wanda ya kauda kai yana Fadin"Bana son Wulakanci fa..kan Fuskatane wajen Fesa Hayakin Sigarin naka..? Imran ya karkace kai yana Fadin"Kila..! Daga haka ya Tsuke Bakinsa Sagir ya Bata Fuska yana Fadin"Au kila ko...?Nagode ai ba sai ka ganni ba ballatana kamin Wulakanci..! Ya juya zai koma Shagonsa yaji Muryan Imran din yana Fadin"Ka Tambayeni Mena karanta a makaranta ko..? To Accounting na Karanta Nayi Degree na Farko Har zuwa Master..! Sagir Daya Dawo da Sauri lokaci Daya yana Zaro Ido Cikin Mamaki yace"Are u Serious..!? Imran bai bama Tambayarsa Muhimmanci ba yace"A University of Ibadan IU,nayi duka Karatuna..! Sagir da mamaki bai gama Sakinsa ba yace"To meyasa kake Zaune baka Nemi aiki ba..? Ko baka samu bane..? Imran ya wani kallo Sagir a Dakune kafin yace"Nayi aiki da Gt Bank Reshen Jahar Lagos a baya..! Sagir ya kara Sandarewa da mamaki Baki ya Bude Kafin yace"Kai din nan Ashe ma"aikacin banki ne Ban taba Sani ba Imran..! Imran yace"Bagashi ka sani ba yanzu..Sai me..? Sagir ya Dafasa yana Fadin"To meyasa ka bar aikin ka..?kenan in Hasashena ya Zama gaskiya ku a Lagos kuke kuka Dawo nan da Zama..! Imran ya kalli Cikin Idanuwan Sagir kafin yace"Eh..! Daganan bai kara cewa komai ba ya Cigaba da Shan Sigarinsa yana Fesar da Hayaki Sagir da ke Tsaye yana kallonsa Cike da mamakinsa Sosai akan Fuskarsa Kafin ya kara Gyara Tsayuwa yana Fadin"Ammh Tambayar Data Dade tana DAmuna ban samu amsarta ba..Shin Meya Baro ku Dachan Lagos din kuka Dawo nan..? Kuma meyasa kabar aikin kazo nan ka Zauna baka da aiki sai Shan Sigari..! Imran kamar bazai ce komai ba sai chan yace"Is a long Story..!Kila zaka san Dalilin Watarana Ammh Not Now..! Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan ya hango Inteesar Tana Tahowa Cikin Natsuwarta Kura mata ido Yayi yana Tunanin kila Daga gidansu Imran Take ganin inda Sagir ya Shagala da Kallo ne yasa Imran Shima ya Waiga yana kallon inda yake kallo,Daidai Lokacin da Inteesar din ta Iso kofar gidan Tana Dago kanta sai Cikin na Imran kamar ko yaushe alokaci Daya Zuciyoyinsu suka Buga alokaci Daya gaban Inteesar ya Fadi Ras Data ganshi,Abun kuma Daya kara Bata mamaki ganinsa Dauke da Sigari yana kallon Cikin Idanuwanta yana Zukan Hayakin yana Fitar da Hayakin ta Hanci ta baki sai ta kara Jinjina al"amarin Tana Shirin Saka Hijabintata Toshe hancinta Ta Tuna da Abunda ya Faru sai tayi Saurin Maida Hannunta da Gudu gudu ta Shige Cikin Zauren Gidansu Sagir Tana maida Numfashi. Imran ya Bita da kallo Cikin mamaki kafin ya Saki karan Sigarin Hannunsa Zuwa kasa ya saka Takalminsa ya Take ya murjeta Lokaci Daya yake Fadin"kalli yarinyar chan saboda Ta Rainani..In ta ganni tana guduna...Kamar Taga wani Dodo. ? Sagir Dayake Lura da abunda ya Faru yace"Ba Dole ta rika Gudunka ba..Taji Labarin kana Sumar da Mutun indai ya Shiga Hannunka..!. Imran yayi Tsai da idanuwansa da suka Kamkance suka Sauya Launi Saboda Busa Hayaki yace"Ina sumar wa..? Uban wa na taba Duka Har na Sumar dashi..? Sagir yace"To ni ina zan sani..?Nima ita ke Fadamim..! Imran da Ransa ya Fara Baci yace"Mganar banza..! Daga haka kawai ya juya cikin Takunsa na Sassarfa da Jarumta ya Fara Tafiya Haka kurum yaji Zuciyarsa na tafasa Sagir ya Bisa da Kallon Haka kurum yake Tunanin Hanyar da Zai Taimakama abokinsa wajen Dawo da Rayuwarsa ta Baya ta Inganta yabar wannan Rayuwar Dayake Ciki. Shikuwa Imran koda ya karisa Gida ko Gani Dakyau bayayi saboda Tsabar Bacin rai,Yana Shigowa Falon ya Fara Kwalama Munari kira Cikin Tsawa da Hargowa. Abba na Tsaye a Falon yana gyara Zaman Hulan kansa da Casbaha a Hannunsa,Fitowarsa Daga Dakinsa kenan ya Dauro alwala yana Jiran Yusuf zasu tafi masallaci Imran ya Shigo Cikin Fushi shiyasa bai ma lura da Wanzuwar Abba a falon ba. Yusuf ya Fito Daga Shashensu Safiya na Bayansa Cikin mamakin wannan Gigitattaciyar Tsawan da Imran ke amfani da ita Wajen Kiran Sunan Munari Daman shima yana Shirin Fitowa ne su tafi masallaci da Abba. Ya yusuf ne Da suka Bayyana a Falon ya Kalli Imran yana Fadin"Lafiyanka..? Me Munarin Tayi maka kake mata wannan kiran..? Ko Kallonsa bai yi ba illah Daga Murya Da yayi yana Kallon Safiya yace"Where is She..? Cikin Launin Bacin Ransa da Tuni Muryansa ta Sauya Cikin Sanyinta Tace Tana Kallon Yusuf"Tana Dakinta..! Bai Tsaya ma Mgana ba ya Fara Taku Zuwa Kofar Dakin Munarin yana Fadin"Wlh kinjin Rantsuwa Daya ko..Kika bari na Taka kafata Daga Inda Nake baki Fito ba.. sai na Tabbata da na Miki Dukan da Ba suma zaki yi ba sai kin ji Kamshin Lahira yadda Zaki ji Dadin ba wata Labarin ina Sumar da Mutane..! Yafada Cikin Fushi Lokaci Daya Jijiyoyin Kansa suna Tashi Radau Kirjinsa na wani Tashi yana komawa Yusuf ya Kallesa ya koma yana kallon Abba Da yayi Tsaye kawai yana kallon Ikon Allah. Munari Da Tun Fitowarta Daga Tiolet Taji kiran da Imran yake mata Tasan Yau Kashin taya Bushe Tsoro ne ya Hanata Fitowa,Tana Tsaye Tana Rawan Jiki dana Zuciya Jin abunda yace ne yasa ta Ta Sadakar ta Fito Domin ta Tabbata Zai aikata Abunda yace Ba wanda ya Isa ya Hanashi Mganar sa kamar Kaifi Tokobi ne in yasara sai tayi yanka.. Cikin karkarwan Jiki ta Fito Daman Kofar tana Bude ne tun Shigar ta bata Rufe ba Haka ta Hade Hannayenta Saman Cikinta Tana Fiki Fiki da ido Har sun Fara kawo Ruwa Saboda Tsoro Tana Hango Kanta Bayan ta Shiga Hannu Ya Imu yana Kwallo da ita kamar Yadda yake Fadi. Bata gama Karisowa gabansa ba ya Daka mata tsawa Cikin Kakkausan Murya yana Fadin"Kina jina ina kiranki Kina banza Dani Don Ubanki..?kin Raina ni ko..?Ko ni Sa"an Wasan ki ne.? Ya Karishe Fada yana Nuna ta da yatsa Lokaci Daya yana jin kamar yasaka Kafa ya bata wani Bugun da sai ta Suma nan take.. Munari Data Rude ai sai ta Zube gabansa ta Fashe da kuka tana yi tana Kamkame jikinta Waje Daya. Abba Dake Tsaye ya Daga Baki yace"Imran kada ka Daketa Nace..!. Ammh Imran bai ma san Abba na Mgana ba Bacin rai ya Rufemai ganinsa da Jinsa. Cikin Kufuluwa ya Kalleta yana Fadin"Wannan kukan naki bazai Hanani Sauya miki kammani yau acikin Gidan nan ba..Wane ne ya Baki Izinin kawo wannan yarinyar Gidan nan..? Kuma Waya baki Izinin da Zaki Kulla kawance da ita Da Har Zaki Rika bata Labarai akan Gidanmu..? Iskancin naki ma bazai tsaya kan Wanda kika Raina ba sai kin Tsallako kaina ko..? Saboda ban taba Yima Fuskarki Dameji ba Shiyasa Har kike da Bakin Fada ma Wata Mara Kunyar yarinyar Chan ina Duka Har sai na Sumar da Mutum ko..? Ya Karishe Fada da Tsawar data Gigita Munari Ta Fara mgana Cikin kuka."Ni..Ni...Wlh..Ban..Fada..mata ko..! Ai bata kai karshen mganarta ba ya Daga Hannu ya Wanketa da wani
Chapter 54 · 0% Book details