← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 190

Sashe 69

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da Sallar Tana Zaune shuru Hafsah ce ke mata mgana Sama Sama take bata amsa saboda Ita bata da Sakin jiki Tana Tambayanta kan Karatunta ne,tace mata Buk kano take ita kuma Hafsah tace Dutse take Karatu Federal Univesity Dutse Tana ZAune agidan ya Sadam. Umma ce ta shigo Dauke da Abida sai kuka take ta mikama Anty Hauwa tana Fadin"Uwarta take son gani..! Dariya tayi ta sunne kai kafin ta Karbeta sai ko yarinya tayi shuru ta Lafe jikin Uwarta Umma ta Rike baki Tana Fadin"Ikon Allah..Yaran Zamani ita anan ta san uwarta..! Inteesar tace"Umma kema ai kene kiyi ta Wahala dasu bafa ya"yanki bane..Ni ce nan ya kamata ki rika Wahala dani ni da nake Autanki..! Ta Karishe fada Tana Tura baki Umma ta Aikamata da Dakuwa tana Fadin"Damam nasan zaki yi mgana ai Kishiyoyinki ne dasu kike Kishi..Inteesar Allah ya Shiryaki..! Dariya su Anty Hauwa suka saka Daidai Lokacin da Baba Asabe ta Shigo Tana Fadin"Nam kuma Wata Hira ake yi ana Dariya shine ba"a Kirani ba..? Umma ta Waiga tana Fadin"Ni da jikar nan takice Baba Asabe..Kishi take da ya"yan Wajen Basheer! Baba Asabe ta Kada baki tace"Aiko nice nayi Kishi..Tunda fa kikazo kike Dauke dasu ita kuwa ko kadan baki kulataba..Jika dai bai fi D"a ba atoh..! Jin haka Yasa da Sauri Intee tace"Yauwa Baba Asabe kema kin gani ko..? Tace"Kwarai na gani kuwa mai sunan Uwar Dakina..! Umma tace"Kidai na kama mganar yarinyar nan..Shigen son jiki ne da ita Tana Gamsamemiyar Budurwa da ita Zan kama Dauka ina Sakama jikina..?indai jika bai fi ba D"a ba to ai D"a bazai fi jika ba..! Dariya aka saka gabadaya ganin Inteesar ta Tura baki Baba Asabe tajuya tana Fadin"Gaskiya dai mune bamu yarda ba..Kufito Falo Daada Tayi kira fa..! Jin haka yasa Dukkansu suka mike Suka Fice Inteesar ne Karshen Fita da kamar zata Cire Hijabin datayi sallah sai ta Tuna kallon kurillan da Khamis ke Binta dashi sai ta fasa ta Dauki Wayarta ta Zura Hannayenta Cikin Hannun Hijabin ta Fice zuwa Falon. Daada na zaune saman kujera Tana Sanye da Hijabinta Fari,wanda yakai mata Har gwiwa Casbaha ne a Hannunta tana ja,Daada duk ta Rame ta kara Fari Tsufanta ya kara Bayyana Daga gani bata da Cikakkiyar Lafiya. Daga kasanta kuma Baffa Kabir ne da Daddy sai Chan gefe kuma Inna Bintalo da gayar ya"yanta Inna Maimuna na kusa da Umma,sai su Any Hauwa da matan su Sa"id,Su Ya Basheer na Daga gefe suma a kasan Cafet din suke zAune su hudu harda Khamis Sai Hamshakiya Mami Asma"u Tana Zaune ya"yanta Guda Biyu Umaima da Sajida sun sakata a Tsakiya ganin haka yasa Inteesar taNufi Kusa da Inna maimuna inda su Karima ke zaune gefe Hafsha ne nan ta Zauna Abiden na ganinta ya baro Wajen Umma ya Rarrafo wajenta Ganin haka yasa ta Dagosa Tana Fadin"Nifa ba Daukan kaba Shegen Karfi ne Dakai..! Daada Dake zaune tana Nazarin kowa sai da Murmusa tace"Ba"a dai san mai sunan Maryama da Rangwanta ba..! Dago kanta Inteesar tayi tana kallon Daada Cikkn Tura baki tace"Daada kada mu fara fadan nan dake..kinga dai baki da Lafiya ki samu dai mu Rabu Lafiya muzo muci gunban Mutuwarki..! Daddy ne ya juyo yana Fadin"Intee..! Ya kirata alamun tayi Shuru sai ta Dukar dakai Daada Tayi Mirmishi Tana Fadin"Kyaleta Mustapha..Daman ai wasan jika da kakan nake so nayi da Jikokina bana samun Daman..Dukkanku kuna wata uwa Duniya..Bana ganin ya"yanku sai dai ku..Kusan yadda nake jin Farincikin in na ganku kunzo Tare da ya"yanku..? Baku sani ba Shiyasa baku Damu da ku kawosu wajena ba sai dai wanda ya Girma ya kawo kansa kamar su Basheer sai Megidana Akali sai su Sa"idu sauran yaran kuwa bana ganin kowa..! Ta karishe Fada Muryanta ta Fara kamar ta saka kuka Baffa Kabir ya Dago kansa yana Fadin"Daada don Allah ki daina saka wannan aranki..Mune fa Ahalinki Duk Duniya baki da kamarmu..Mganar yara kuma Daada kin sani ba domin karatu ba Da zaki rika ganinsu akoda yaushe..! Daada tamai wani kallo kafin tace"Kayya Kabiru kullum mganar kenan Karatu..Naji karatu..Ba sa samun Hutu ne..?suna samu meyasa alokacin baza ku kawosu ba yanzu anan Wajen ba Domin kiran da nayi muku ba na Tabbata ku kadai zaku zo..Matayen ku ma ba Sosai suke zuwa ba sai wani abu ya taso..Na tabbata Wasu anan Rabonsu da Dukku sun manta wasu kuma kila yau suka fara ganin junansu a Mtsayinsu na yan"uwa ina amfaninshi...?kunga hakan ya Dace kai ne Babba Kabiru kafi kowa sanin yadda Mahaifinku marigayi Alkali yake da Riko kan Zumunci sai gashi yau bashi da rai Daga Gidansa ma Cikin ya"yansa Zumunci ya Lalace kuma yayi Rauni..! Kowa afalon yayi Shuru yana Sauraran Daada mgangunta sun kashe ma kowa Jiki Inna Maimuna ta Kada kai tana Fadin"mganarki gaskiya ne Daada..Ni kaina Rashin Zumuncin nan namu na cimin Tuwo a kwarya Daada..Ace muna da yawa fa gamu da ya"ya ga jikoki zmunci duk mun Sakeshi kuma Laifin yana Wuyanmu ne muke da alhakin Nuna ma ya"yanmu gidajen yan"uwanmu Domin susan kowa..Koda muka yi Nisa muna da Rufin asiri daidai Gwargwardo Muna da abun hawa zamu iya Tashi muje duk inda muka ga Dama..Allah na Tuba cikin mu ba wanda yabar kasar nan Baban Sajida yana Abuja in anso arika Ziyartar juna Abuja ai kamar zuwa Dukku ne sai Ya Mustapha yana Kaduna ina Kaduna ina Abuja,Sai ya binta Dake gombe nan da Gombe ma Allah na Tuba Menene aciki Tsakani ga Allah..? Ammh bamu yi wwnnan kokarin ba..Daada ce kadai muke zuwa Dubata mu da ta zame ma Dole bamu yi Tunanin suma ya"yanmu Dolensu ce ko banza nan din Tushensu ne Sai kiga ammh suna Ziyatar sauran Dangin nasu na uba ko na uwa mu bamu damu da susan kowa ba gaskiya akwai gyara ban Cire kaina ba Har ni ina Da Laifi kuma ko Daada batayi wannan mganar ba ni zan yita ko Saboda Mganar Barin Ya Malami Dashi Da iyalansa Daga cikin mu wani Abun Takaichi ne da Abun mu Zauna musanta ina zamu bulloma Al"amarin..? Nasani kun sani Wlh ko Kaffara bazan yi ba Rashin Lafiyan Daada Tana da alaqa da rashin Sanin Takaimaiman Wani Hali ya malami ke Ciki da Iyalansa ne ko nayi Karya Daada..? Takarishe Fada tana kallon Daada wacce Har hawayr ya fara wanke ma Fuska Cikin Muryan kuka Daada tace"Kin yi gaskiya Maimunatu..Wani Lokacin in kikayi mgana kamar yayanki Malami haka yake da Sanyin Hali da Hangen nesa..Hakika abunda ke Cikin zuciyata kenan kuma Dalilin kiran danayi muku shine kan gaba sai yadda Zamu taru mu gyara Kuskuran da muka Bullo dashi acikin Ahalin mu Tukafin mu Kara yawa abubuwa suzo suki gyaruwarmana yadda muke so..Ko kuma na Fadi na bar Duniya ku Watsar da Zumuncinku Gabadaya..! Ta karishe Fada tana Sharan Hawaye da Gefen Hijabinta Daddy Cikin Sanyin Jiki ya Dafa Kafafuwan Daada Yana Fadin"Don girma Allah Daada ki Daina kuka..Mun gane kuskuranmu kuma mun miki alkwarin zamu gyara..Mganar Ya Malami kuma Na Rantse miki har ga Allah Dagani har Barrister bamu zauna ba muna ta Cigiya kuma da yardan Allah za"a dace ina ji ajikina Ya Malami ya kusa Dawowa garemu..! Daada ta Kwace jikinta Cikin Bacin rai tace"karya kakeyi Mustapha..! Gabadaya falon sai da aka juyo ana Kallon Daada yadda Tayi mgana Cikin Fushi Daddy ya Dukar dakai Yana Fadin"Allah ya huci zuciyar Daada..! Daada bata tsaya Sauraransa ba ta Cigaba da Fadin"Koda yaushe kalaman ku kenan kaida Dan"uwanka In nayi mgana sai kuce kuna iya bakin Kokarin ku..?yau ne ya bar gida..? Yanzu fa Kimamin Shekaru uku har da wani abu da Bacewarsa shi da Iyalansa Ammh ba wani Labari sai Faman Fadamim kike yi kuna iya bakin kokarinku..Ina Kokarin yake..?ba wani Kokarin da kukeyi kowannenku yana chan yana Harkan gabansa Kawai Shi ya Dameshi baku Damu da Dan"uwnku Daya bar gida Cikin Lalura da Raunin Rashin Daya Fuskata ba..To bari kuji na Fada muki ba iya Kokari nake so kuyi ba Sama da Kokarinku zaku yi ku dawo min da Dan"uwanku gida in ba Haka ba Nima Zaku wayi gari kunyi Sanadiyar Rasani Kamar yadda kukayi Sanadiyar Barin Dan"uwanki Cikin Ahalinsa yabar komai nashi yayi Nesa Damu saboda yadda kukayi ta Tafiyar dashi..! Ta karishe fada Tana kara Goge kwallarta da Haban Hijabinta Kowa afalon ya kasa Motsi saboda Shesshekan kukan Daada,Baffa Kabiru da tunda aka fara mgana bai ce komai ba sai alokacin ya gyara Zama yana kallon Daddy Lokaci Daya ya maida Hankalinsa wajen Daada yana Fadin"Haba Daada wannan wani irin mgana ce ya zaki dora mana Alhakin baarin Malami gida..? Wannan ai ba mgama bace ya bar gida ba saboda komai bane sai baya son a Fadamai gaskiya sannan ya Biyema Mganar ya"yansa Har ya iya Tafiya har yau bai nemi kowa ba..Daada ki Dora duka Laifin akan karansa shi da ya"yansa ba akanmu ba..! Mami Asma"u dake gefe tace"Nima abunda Zan ce kenan Baban Sajida What all d Bleming akan ku kuma..? Wanda ya tafi batare dayayi Shawara da kowa ba..Shi ya kamata a Dora ma Duka Laifin ai Daada..! Inna mainunatu ta Kalleta Tana Fadin"Sam bai kamata ba abunda kuma kikayi ba Daidai bane..Bai dace Manya na mgana ba kina saka baki ba..Koda kike Matar ya kabir wannan ba Hurumin ki bane mganace ta Tsakaninsu bai kamata ki saka baki ba gaskiya...ko kuwa nayi Laifi Jama"a..? Tafada tana kallon Daddy kai ya gyada mata kafin yace"baki Laifin komai ba Maimunatu..! Daada ta Dago daga Sharan kwallar Tana Fadin"Kabiru ka tsawartama Matarka..Kada ta kara sakamin baki in ina mgana da Ya"yana..! Bai da yadda zai yi Dole ya juya wajen Mami Asma"u data gama cika Da mganganun Inna Maimuna sai Harare Harare take bai mata mgana ba da ido kadai ya Kalleta alamun kada ta kara Mgana sai ta koma tayi Laushi Lokaci Daya Tana kara Rumgume Sajida Dake jikinta Inteesar Dake rumgume da Abiden tayi Tsaki acikin Ranta kafin ta Juyar da kanta Karaf suka Hada ido da Khamis ya Kureta da ido Saurin Kauda kanta tayi acikin Ranta tana Ayyana wannan kodai Maye ne wlh kurwanta kur indai itane. Daada ta kara Gyara Zama cikin Shakewar murya tacigaba da Fadin"Zakace min kada na Dora alhakin barin Malami gida akanku Kabiru..? Musamman ma kai Domin Mustapha In
Chapter 69 · 0% Book details