Sashe 73
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Sakarci kamar wata yarinya Duk Inteesar na jinsu ita dai bata Tofa ba sai dai kawai ta Murmusa aranta Tana fadin ita Taga Rashin kunyar Sajida tun lokacin ta Gama Sanin Halinta kaf ta kuma san inda ta ijiyeta.. Sai gabda mangariba suka gama aikin white rice ne sukayi da Miyar Naman Rago sai Ferfesun kaji da Daddy ya bada kudi su Basheer suka Fita suka Siyo sai Salat da Lemon Aya da na Kankana suka Hada,Daganan kowa ya tafi yayi sallah Su Umma da su Inna Maimuna daman suna Falo suna kallo suna Taba Hira Mami kuwa da ya"yanta suna Daki basu Fito ba koda Umaima tace zata je Kitchen hanata Tayi. Inteesar dai bata iya Sallah ba Sai da ta Watsa Ruwa kana ta gabatar da Sallah Tana Kan darduman har aka Kira Insha"i tatasshi ta gabatar ta Idar ba Dadewa taji Hayaniya afalo kenan Mazan sun Dawo daga masallaci sun Shigo kenan,Tana nan zaune bata tashi ba Hafsah tazo tayi Sallar Isha"i tace tazo su je su Taya Baba Asabe kawo su abinci Karima na Wajen tace Su Anty Aneesa gasu chan suna kwasowa jin haka yasa bata yi yunkurin Fita ba sai da Hafsah tace ta Fito suci abinci kana ta Fito duk da bama ci Zatayi ba ita abu mai Ruwa Ruwa Zata sha Shiyasa tana Fitowa Kitchen ta Nufa ta Tsiyayo Ruwan Zafi a Flaks ta Hada tea a wani karamin Mug ta Fito dashi da Cokali Tana Juyawa Daki tayi niyyar komawa Domin yau cin abincin basu Daddy suna Dakin Daada suna mgana Matan ne sai Ya"ya sai jikoki sai Tattaban kunnen Daada Dake Tsalle Tsallemsu afalon. Har takai Kofar Dakin taji an ce"Ina Zaki..?badai bazaki ci abinci ba Inteesarr..! Yadda ya fadi mganar ne Cikin Wata Murya yasa ta waigo Khamis ne ko ya Kureta da Mayen kallonsa kauda kai Tayi Tana Fadin"Eh am ok..! Sai da ya wani kalletaa kasa kasa kafin yace"U are ok dame..? Me kikaci..? Takaichi da Haushi suka kama Inteesar ba ita kadai ba Hadda da Mami Asma"u da Sajida da basu ga Dalilinsa nayi ma Inteesar mgana ba. Rausayar dakai tayi Cikin Kosawa Tana Fadin"zan sha Tea..! Tafada tana Dagamai Mug din Dake hannunta Zai sake mgana Mami Ta Kallesa Kafin tace"Khamis plz kaci abincinka Tace She is ok ko Dole ne..? Tafada Cikin Halin ko in kula Umma naji batace komai ba sai chan Tace"Intee bamai cin abinci bane..Tafi daman shan Ruwan zafi in Zata kwanta.! Mami Ta tabe baki Kafin tace"Plz Help me.. tell Him..! Daga haka ta Tsuke bakinsa Shima bai kara mgana ba sai Binta yake yi da kallo Itama Juyawarta Tayi ta zata Shigo Dakin Sa"id ya Kirata ta waigo Cikin Girmansa yace"Ya Zaki tafi..? Da fa mun gama cin abinci zam karbi lambar kowa..Kowa kuma zai yi Sharing Cantact dinsa da Dan"uwansa..! Yake Inteesar Tayi kafin tace"Ya Basheer plz ka bashi Cantact dina..! Harara ya Dago ya Sakarmata yana Fadin"Ni dan aikin ki ne..? Shagwabe mai Tayi tana Fadin"Plz Bro..plz Mana..! Kallonta yayi kafin yace"Ok..Naji kafin ki samin kuka..! Dariya tayi har sai da Fararan Hakoranta suka Bayyana tace"Tanque Bhaya..! Sa"id ne yace"To in an bamu taki na Sauran fa yaushe zaki karba..? Da sauri tace"In d mrming kafin mu tafi Insha Allahu..! Kai ya jinjina kafin yace"Is ok..Buh ki karba kisan Is very Important..! Kai ta gyadamai kafin ta Juya ta Shiga Cikin Dakin tana Sakin Sirrin Tsaki Aranta Tana Zagin Khamis kallo kamar Wani maye yayi ta Kallonta Haba ita fa ta kosa Gobe Tayi subar Gidan nan ta koma Tayi Shirin komawa makaranta Munari tace itama bazata Shiga School ba sai in ta Dawo su Shiga gabadaya. Tana gama Shan Tea dinta ta Haye gado Ta gaji Barcine a Idonta Lokaci Kadan baeci ya kwasheta Sama Sama Tana jin Tashin mgangansu Daga Falon Daada. Su kuwa sai wajen 11pm Taron ya tashi Adaran Sa"id ya Bude group din ya Karbi Lambar Kowa ya sakashi,Daga kan iyaye har kan Kanne da yayyi irinsu,Ya kuma Umarci Kowa ya Karbi Lambar kowa,haka akayi sukayi ta Sharing din Cantact din juna da alkawarin Kiran juna Lokaci bayan Lokaci,Umma daman Tana da Mami sai dai su yi Wata Biyar ba wacce ta kira Kowa acikinsu Sai ta karbi ta Inna Maimuna da Inna Bintalo yaran yaran kuma suka Karbi da junansu,Umaima ce ke bata Lambarta Cikin Dadin rai banda Sajida har gwarama Mami ta bata nuna wani abu ba Ba wanda na yabi ta kanta Ballatama ya Damu da ita banda Hafsah ba wanda ya karbi Lambarta,Sai ya"yan Inna Bintalo Daman Hadeje ce da kano,Lambar Inteesar kuwa Umma ce tayi ta badawa Mazan kuma Basheer ya basu Wannan abun yafi yima Khamis Dadi Domin Hanya mafi Sauki kenan Wajen Cimma Burinsa kan Inteesar da Tunda ya Fara ganinta Tunaninta da Soyayyarta suka yi mai mugun kamu basu barshi yayi barcin Kirki ba.,Love at first sight kenan Su Daddy kuwa sai Wajen 12pm suka Fito Daga Wajen Daada suka ci Abinci suka Nemi makwanci Nasihohi ne Tayi musu sosai mai Shiga jiki wanda Har sai da shi kanshi Baffa Kabiru ya yarda da Kuskuransa kuma yayi ma Daada alkawarin Inshu Allahu zai gyara Daganan suka Shiga Hira da Tsara yadda Zasu Hada hannu dasu da ya"yansu su zama Zuru"a Daya ba Wariyar Launanin Fata shi ya bata musu Lokaci basu Fito da wuri ba. Ranar Daada Tayi barcin Farincikin Data Dade batayi ba. Washegari Tun 4am na asuba Kowa ya Tashi saboda Sammakon Tafiya,ko kafin karfe bakwai na Safe Masu Shirin Tafiya duk sun Shirya Baffa Kabiru suka Fara Tafiya Sadam wanda Zai je kano Inteesar ta karbi Lambar Matarsa Aneesa tayi mata alkwarin in ta koma kano ZAta zo Gidansu tunda tace suna Sharada Phase3 ne da Zama. Daga sune sai Sa"id da zasu je Dutse Tare suka Tafi da Hafsah tunda Tana Wajensa ne itama sun karbi Lambar juna ita da Inteesar,karfe tara na Safe su Inteesar suka Mika Hanya sun bar Inna Maimuna na Shirin Tafiya ita da ya"yanta sai sun Biya ta Bauchi Inna Bintalo kuwa sai gobe Zata koma,gida duk yayi Shuru tunda Baki sun Watse Daada ta Bisu da addu"an Allah ya kaisu Gidajensu Lafiya kamar yadda suka zo hankalinta bai kwanta ba sai da Kowa ya Kira yace ya sauka Lafiya Har Inna Maimunatu da suka Tafi Daga baya suma sun sauka Bauchi lafiya sai dai kuma wani Haduwar In Allah ya nufa.