← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 190

Sashe 156

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Domin Sanda yaga su munari sun Fito da ita baki ya saki yana kallonnta baisan Sadda ya Furta masha Allah ba Saboda yaga tayi sanyayyan kyau mai Cike da sakama zuciya Natsuwa. Har Cikin Motan suka Rakata suka Sanyata Kusa da oga Imu wanda suna karisowa ya Dauke kai kamar baya kallonsu Munari ce da Hafsah suka gaisheshi da Dakyar ya amsa. Aransu sukace kamar Dole..? Sai da Motar su Sa"id ta Fara yin gaba da Ta Basheer da ta Sadam kana Motar Ango da Amarya ta Daga Khalil da Sagir na gefe Khalil ke tuka motar. Suna Kallon Imran ta Madubi suna Danne Dariya shi baima Lura dasu ba Tsabar Haduwar Intee da kamshinta ya gama Rudasa har bai san ya Riko Hannunta ba Sai ji yayi ta Dago Tana kallonsa Cikin Narkakun Idanuwanta. Lamgwabe mata kai yayi a Hankali yace"Meyasa baki bar wayarki a Hannunki ba Ahalin kinsan zan kiraki..? Tana Kokarin Daidaita kanta jin Yadda yake Faman shafa Hannunta Tace"Ni ban ma san inda take ba..Kamar Tana Hannun Mu..! Dakuna Fuska yayi zai yi mgana suka Hada ido da Sagir ya Ballamai Harara yana Fadin"Munafuki i donsa na kan miji da mata Watarana sai idonka ya Tsiyaye..! Sagir da Khalil Sai Dariya suke kwasa koda suka isa Wajen su Munari sun kariso suna Waje suna Jiransu ba Bata Lokaci Imran ya Fito Shida Inteesar ba wanda ya bashi Shawara shi yaga Dacewar ya Damke Hannun Amaryan Tasa gam Ransa na kuna in ya Tuna ahaka maza dadama zasu kallemai adon mata. Sune kan gaba da su Waleeda da akayi ma Kayattacen shiga suna kan gaba tawagan su Munari na baya dasu Sagir da sauran gayyar suna Shigowa wajen ya Dau Sanyayyan Kidan Aure ya Dauru ga Kyali kyali na Sauka ta Ko"ina Waje ya Cika Damkam da Jama"a Imran bai saki baki ba sai da yaga Dimibin Abokan aikinsa A Wajen Har Mr Sulaiman da Mr Tunde,mamaki ya Kamashi su kuma sai dai suka Dagamai Hannu Suna Zama Inda aka Tadanar musu MC ya Fara Jawabi,Saboda Dare yayi kuma Imran ya bada Sharadin in aka Wuce 11pm Wlh zasu Nemesa su Rasa Susan Halinsa Shiyasa suka Gayana Mc ayi komai Cikin Lokaci. Game aka Fara gabatarwa Irin dai na Mc,Tun alokacin Imran yaji ya Fara gajiya,sannan aka Umarci abokan Ango ya bada Tarihin ango Sagir da Khalil suka Fito Sagir ya Fara Bada Takaitattacen Tarihin Imran Daya Sani.Khalil ma ya karba ya bada Nashi Wanda ya sani Tun suna Lagos. Kafin Sagir ya karbi Abun mgana yana Fadin "Wato Soyayya Tsakanin Inteesar da Imran Wata soyayyace da Bantaba ganin irin ta ba..Makauniyar Soyayya ce da su kansu basu san sun Fadama juna ba in ance yana sonta yace Shi ba sonta yake ba ammh Kusan me..? Baya son kukanta..?baya son bacin Ranta bayason ganinta da wani kun Taba ganin Damben maza..?ku Fadamin soyayyahce ko yan"uwataka ke sawa Namiji yayi Fada kam mace yaji yana Kishin ya ganta da wani Ku Fadamin da karfi Soyayyah ce ko Yan"uwanta ka..? Gabadaya Hall yadau Ihun Soyayyace Wlh na Love Sai Dariya da ihu da Tafi Imran Hararan Sagir kawai yake yi yakasa mgana Sagir na Dariya yace"Uhm...Harfa Rakata yana yi.. Gadin ta ma yake Wato Mr imran ya Dade dai yana Son Inteesar Daga Karshe Dayaga za"ayimai Kafa sai ya Zabura ya mike ya bayyana kansa ammh fa shi adole bai yarda yana Sonta ba Cewa yake..! Yakasa karisawa Saboda yadda Imran ke aunamai Harara ga Ihu ya Kaure a Hall din Sagir na Dariya yana Fadin"Ammh fa soyayyar tasu ta Musamman ce..Ina wasa Dake ne..? ni Sa"anki ne..?kin Raina ni ko..? Zan Sauya miki kammani Zan yi kwallo Dake..?To Amarya Inteesar Shaawaran da zan baki a mtsayinki na kanwata Sai kin yi Hakuri kin Dage da Ninka Biyayya ga Girman Miji ga na Yaya in baki yi a Hankali ba Angon naki cikin Kwanakin nan na Amarci zai iya Sauya miki kamanni Ko kuma Gidan ku ya koma Gidan Kwallo da Mutane.! Gabadaya aka kara Saka Tafi da ihu Imran kallon Sagir kadai yake ya auna yadda zai Yi kasa kasa dashi in suka Kebe Inteesar sai Dariya take kasa kasa yana kallonta. Sagir ya cigaba da Fadin"To kai kuma abokina sai fa ka yi hakuri..Mata fa yan Lallashi ne duk da kace kai Allah ya kyauta ka Zauna kana Lallashin Mace..! Khalil ya Karbe abun mganar yana Fadin"Sagir nace Ranar Lallashin bata zo bane..Nace Jama"a ku Fadama Mr Imran Ranar Lallashin bata zo bane..Sanda zai shige Dimuwa yana Fadin Baby Plz mana kiyi Hakuri..! Ya Karishe Fada yana kwaiwayon mganar Imran ai gabadaya aka Saka Dariya wasu Harda Rike ciki Kai in aka Biyema Khalil da Sagir zasu Kullan ma da Mutane Cikinsu kuma ga ba Lokaci Imran Kamar ya Fashe Sagir da Khalil sun gama Dashi Gaban yara. Su Yusuf Dariya kamar su kwanta yana kallon Fuskar Imran yana Dariya Nasara aka Kira tazo ta bada Tarihin Amarya Daganan aka bada Lokaci akaci akasha kana aka Fito Filin Rawa Imran duk yadda yaso ya Zille sai da su Sagir suka Fito dashi suka Rika mai barin kudi shi da Inteesar da sauran Dangi aka kuma barsu su kadai su Rausaya Imran dai ko Gyada bai yi ba sai ma Inteesar data dan juya shima bai bari ba ya Rikota yana mata wani kallo Dayasa ta Dataka sai Hall ya Dau sowa da ihu Wajen yanka Cake ma abun kallo ne Imran ai Oga ne Komai nashi na Dabam ne. Awajen Dinner ma chan na kara Hango gayyar yan GMB2BANDGROUP,da nasu Hadadden ankon Dinner din masha Allah sai Washe baki suke Daga nesa suna Daukan Intee da imu Hoto saboda suna Tsoron su karisa wajen Imu ya Fahimci Hoto suke Daukansu zasu bazama duniya yace baisan Raini zai Sauya musu kammani suna Daga gefe sun kame suna Kallo kowa Daya bayan Daya suna masu Farincikin ganin wannan Ranar da su munari da Sagir kadai suka samu Damar gaisawa sosai. Anci an sha an sha Rawa an yi barin kudi su Inna Bintalo ana gefe atana Daukan ma Mami Asma"u Video Tana Turamata tana kara Tada mata da Hankali Sai 11pm aka taahi Imran suka Fara Tafiya sai da suka kai Inteeear gidan Abba kana suka wuce Gidan Sadam,Suka ijiyesa Khalil da Sagir suka juya zasu Dauko su Munari ko mgana bai musu ba ganin suna Rawan kafa kan yaran zai Fada musu gaskiya su kama kansu baya son Raini.
Chapter 156 · 0% Book details