← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 190

Sashe 139

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Su Imran suna Cikin Tafiya sun kusa isa kano,sai mirmishi yake shi kadai in ya Tuna shi fa yanzu Mijin Inteesar ne sai Nishadi yake ji in ya Tuna hakan,Yana ayyana yadda zai Rika Zuba Mulkinsa son rai,Kamar zai Tura mata sako sai wata zuciyar ta Hanashi da Cewa kul Imran wlh Ka kiyayi kanka Yanzu taji labarin komai sai ta Zata kana sonta ne Raini ya Fara shiga Tsakaninku abunda bazai taba yarda ya Faru ba Har Abada Balle da Munari Ta fara cewa wai suna Munafunci Yarinyar taci abinci in suka Hadu sai yayi kwallo da ita Tuna haka yasa kawai ya Share duk da har suka iso Tunaninta yake yi shi bai yarda yana sonta ba Imran naso ya rika karyata Feeling dinsa.
Tun da suka Taho Yusuf ya Kira Safiya ya Fadamata ta sanar dasu Munari,Munarin ta tayata suka Dora abinci Inteesar dai bata ma da Wani Kuzari bata san da wani ido Zata iya Kallon Imu ba wani Haduwa zasu yi akaron Farkon su na mata da miji..? Ga Abba ga ya yusuf gaskiya Tana jin kunya sosai bazata iya Hada ido dasu ba.
Tuna Haka yasa ta Lallaba ta Kwashi Littafan karatunta na gobe ta Gudu Gidan Mama koda Munari ta Laluba bata Gidan ta Gudu Data Kirata a waya sai tace Tana gidan Mama chan zata kwana Munari ta Rike baki Tana mata Tsiya.
Chan din Mama ta sakata gaba da Tsokanan Abaya Lokacin Datace Allah ya Tsareta ta Zama matar Imran yanzu kuma gata mtsayin matarsa yake nan..?
Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"ai bani nace ina sonsa ba..!
Mai mama zatayi ba Dariya ba Dawowar Sagir Bayan mangariba yasa Tasan su Imu sun iso kenan Shima ai yana shigowa gidan ya Ganta yahau Tsokananta da Matar Abokina Dan iska ko mai Shaye Shaye..?
Intee Tayi kwal kwal da ido kafin Tace"Kai ya Sagir..Mama kin gansa ko..,?
Cikin Shagwabarta kamar Zatayi kuka mama tace"Kyaleta Mana kada ka sata kuka..Ta gudu ne bata son Hada ido da Abba tana Surukanta dashi ba Uba ba..!
Dariya suka saakamata yasa ta Shige Ciki Tana Kukan shagwaba wanda bai da Hawaye Sagir yace ai su Abba sun Rigasu isowa su Sa'id ya Daukosu Ya kuma wuce jigawa Sadam kuma sai da su Abba suka ijiyesa agida kana suka Wuto nan.
Dakinsa ya shiga ya ijiye jakarsa ya Fito ya Dauki Buta ya Zagaya.
Yana Fitowa yayi alwala ya shiga Daki yayi Sallah Mama ta gabatar da abinci yaci yasha Ruwa yana bama Mama labarin kadan Daga abunda ya Faru a Dukku Harda Sakin da Imran yayi ma Sajida Mama ta nuna jimami sosai ammh fa akasan Ranta tasan Inteesar tafi Dacewa da imran.
Inteesar na Daki Taji komai Duk da bataji Dadin Haka ba sai dai Taji Sakayau Nauyin Kirjinta ya Ragu da Kishin Sajida sannan taji Haushi wai Da Sagir ke bama Mama Labarin Sajida tace tana son Imran Ranta ya Baci ta Tura baki tana Fadin"Ai sai ta yi ta sonsa..mara zuciya ba ya saketa ba..!
Ita kadai tayi ta Bata rai Sai dai taji Dadin yadda Mami Asma"u Taga Karshenta sai dai Baffa Kabiru ne ya bata Tsaisayi aranta tace Allah ya kara shima.
Mama bataji Dadi ba Salallami take,ko kadan abun bai mata Dadi ba Kiran Sallar Isha"i ya Fitar dashi chan masallaci suka hadu dasu Abba da Imran sai da suka idar suka fito Waje Sagir ya yafito Imran yana Fadin"Amaryanka na gidanmu ko zaka shiga ne ka rage Dare..?
Imran yayimai wani kallo kafin yace"Kaifa Dan iska ne a ina kasan ana Rage Dare Sangiru..La"ilahaillalah..Ka lalace na bani..
Dariya Sagir ke yi shima imran Dariyan yake yi kafin yace"Abun mata da miji fa..Allah ya shirye ka zan Tashi Tsaye na nemo maka matar aure kada ka Fara Leke gidajen Jama"a cikin Dare
Yafada yana Dariyan keta Duka Sagir yakai mai a Gefen Cikinsa ya kuwa Samesa shima Imran din ya Hambaresa yana Fadin"Dan iska karya nayi maka..!
Sai Dariya suke cike da Nishadi Daga ganin Dariyan da Imran yake yi na Tsantsan Farinciiki ne bai sani ba.
Ba yadda Sagir bai yi ba Daya shiga yaki shiga Cikin Dakuna Fuska yace"Bazan shiga ba Uban me zan mata..? Ai tasan muna Hanya ta Tafi gidan Mama kuma Dataga ganka meyasa batazo tamin Sannu da zuwa ba sai nine zan Bita Allah ya Tsari Imran..!
Daga haka ya wuce Sagir yabi sa da kallon Hum ka kusa zuwa Hannu.
Shi kuwa Haushi ta bashi,Koda suka Dawo idanuwansa ita suke son gani ammh bai ganta ba kuma bazai iya Tambaya ba sai da Abba ya Tambaya Munari na Dariya tace Abba ta Fara Suriki Dakai shiyasa ta Gudu gidan Mama.
Abba Dariya kawai yayi shi da Ya yusuf Imran naji Ransa ya baci Wato ta Gudu saboda kada ta gansa ko..? Ba wani Saboda Abba karya take yi.
Da wannan Haushin ya koma Gida kunun Ayan da Anty Safiya tayi kadai ya sha ya shiga ya kwanta saboda Fita aiki da wuri gobe ammh yana ayyana yadda in suka Hadu da Inteesar zai nuna mata shi ba sa"an wasanta bane ta bar ganin suna mata da miji yanzu bashi zai hana ta kawomai Raini ya Tattaka ta ba.

*Shakira...*
3/24/22, 23:22 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�18*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Chapter 139 · 0% Book details