← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 190

Sashe 83

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

tafe Inteesar na nuna Hanyar har Kofar gidansu Munari ya Sadam ya Zuba Hon Iro megadi ya leko cikin mamakin ganin Mota ganin bata Yusuf bane Har ya Bude musu suka Sulala cikin Haraban gidan bai Daina mamaki ba. Imran dake duke a gaban mashin dinsa d yana gyara Wani Abu ne Daga kasa yaji Shigowar mota bai Damu Daya Dago ba azatonsa Yusuf ne shiyasa ya cigaba da Abunda yakeyi. A parking space sadam ya faka Motarsa suka Firfito koda ya Fito idanuwansa na kan Imran dake Duke so yake ya Dago da kansa yaga ko waye..!? Ita kuma Munari duk ta Tsure yau mai kwatanta Hannun Ya Imran sai Allah tunda ta gayyato wasu gidansu abunda ya tsana. Imran mganar Waleed yaji yana kiran Daaddy,yasa ya Dago da kansa Lokaci Daya yana Mikewa gabadaya Daidai Lokacin Sadam nata saitinsa suka Hada ido Hudu atare gabansu ya Fadi,lokaci Daya suka Zura ma juna ido Aneesa ma ta Juya tana kallonsa duk da ahoton ya kauda kansa hakan bai hanata ganesa ba. Imran ya taba Haduwa da Sadam Lokacin gaisuwan rasuwan su Anni a Dukku sau daya domin da suka zo gaisuwa basu kwana ba Shida Sa"id..!Yusuf ne ya sansu sosai Tunda suna waya lokacin sannan suna Haduwa in yaje Dukku duba Daada. Imran mamaki ne ya kamasa yana so ya Tuna Fuskar Sadam ya kasa..?sai dai yaji wani yanayi ajikinsa. Sadam kuma sunan Imran ne ya bace masa ya kasa kamawa sai kuma gwiwansa dayayi sanyi ganin yadda Imran din ya Hade rai bamai ma Nuna ya Taba ganinsa ba. Inteesar da Munari basu Fahimci komai ba yaran sukaja zuwa cikin Gidan Aneesa ta bara musu baya ta Kosa ta shiga gidan ta kara Tabbatarwa ko gaskiya ne duk da Shaidu Biyu sun nuna kansu. Wayar Sadam ce ta yi kara yana Dubawa Sa"id ne shima ya kasa Natsuwa Kashe kiran yayi ya Turamai sako..!
Chapter 83 · 0% Book details