Sashe 170
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inteesar ta koma gida da Kudiri Tare da Niyyar gwada Shawarwarin Munari da kuma amfani dasu. Tana komawa Gida bata Zauna ba Bayan ta sha Complex tayi alwala Tayi Sallar la"asar Domin sunyi Sallar Azahar a makaranta ita da Munari. Daganan ta Fara gyaran Gidan bata gyarasa Koda yaushe sai Ranar Datake Gida shima Daga Falo sai Kitchen sai Dakinta ko Hanyar Bedroom din Imran bata Taba kallah ba. Sai da ta kal kale ko"ina Har Bedroom din nashi ta shiga ta gyaramai Duk da ba wani gyara saosai bai da kazanta Duk Abunda yayi amfani Dashi yana Kokarin Maidashi Muhallinsa Har Tiolet sai da ta wankemai Tas yana Tashin Kamshin Turaran Dakunan Data Turara Gidan dashi a Burner. Tana gamawa Ta Fada Kitchen ta Fara Sarrafa abunda Zata Dafa Saukkan Abinci Tayi Farar shinkafa da Miyar ganye Da Kifi sai ta Soya kaza Tayi mata Pepe Chicken da yaji albasa da kayan Kamshi,akwai Fruit a dayawa a acikin Fridge Saboda Imran baya bari ma ya yankemai Wani Lokacin da yawa yake siyowa Tana sha ammh ita dai barta Da Cin kayan Fulawa da Zak'i. Kayan Lambun ta yayyanka tayi Fruit Salt ta saka afrige Lokacin Data gama an Fara Kiran Sallar mangariba Bata Shiga Daki ba sai da ta Jera komai Saman Dining kana ta shiga Ciki. Wanka Ta Farayin kafin ta Dauro alwala ta Fito Sallar ta Farayi kafin ta Shafa Man shafawarta na Olive Ta Fara kokarin neman kayan da zata saka Wadanda zasu ja Hankalin ogan akanta. Cikin akwatin kayanta na Gida Wanda Nasara ta Hadamata,gabda Biki ta Bude Tasan Tana da wanduna da Riguna Lokacin Tana Gida da Zata Taho kano ne Umma ta Hanata Tafiya Dasu Taji Dadin ganinsu aciki Batasan Umma ce ta saka su ba,Domin ai Tasan Zasu yi mata amfani Tunda Gidan Miji Zataje Daman ko Gidan Maman abunda yasa Umma ta Hanata Zuwa Dashi Saboda ba kamar nan bane Da ba Kowa Daga ita sai ita sai Daddy Ya Basheer na Gidansa ba Kullum yake zuwa ba,gidan Mama kuma akwai Sagir kuma shi ba Muharraminta bane Shiyasa ta Hanata tafiya da Wandunan datake Sakawa su Lameta sosai suna Fitar da Surar Jikinta. Wani Wando ta Samu Red Colour Daga Kasa ya Tsuke sosai iyakarsa kuma daga gwiwanta Kadan ya Wuce sai Wata karamar Riga mara Hannu Itama Ja ce sai dai Tana da Zanen Baki a Jikinta an yi Rubutu kanana daga gaban Riga Data Sanya kayan Ta Tsaya gaban Madubi sai ta Fara Tunanin Anya Zata iya Fita gaban Ya Imu haka..?kayan Tun Tana gida bata cika sakasu ba sun kamata sosai Wandon ma Dakyar ta saka Gabadaya Shafaffan kugunta ya Bayyana Kirjinta ya Cika rigar ta kamata sosai da Har Shatin Cibiyarta ana gani sannan kuma Da kadan ta Wuce Cibiyarta Data Daga Hannu Lafaffan Cikinta Zai Bayyana Waje ne. Sumar kanta Da bata Kitse ba Ta Tattara ta Daure Daga kasa ta Sakamai Band kafin ta Samu Wata Hula red itama mai adon kamar Love ta gaba ta saka bayan ta Saka wani Saukakkan Dan kunnen da bazai Dameta ba kara kallonta Take ta Madubi kafin Wata zuciya tace mata"To ke Intee keda zaki burge Miji ai bakya Bukatar wannan Hular..! Tafada Tana Cire Hular kanta Sake Sauya yanayin Band din Tayi ta maidashi ta Tsakiya duk da ba wata Doguwar suma gareta ba Tana da Cika da na Zaman Falo. Karan Bude get taji Tasan ya Dawo kenan Tanaji ya Shigo da Motarsa ya koma ya Rufe get din Wanka Ta Fara ma kanta da Hunra da Turaruka masu Kamshi Da Fitar ma da Duk wanda ya Shake su Hankali yau akwai jan mgana. Kugu ta Rike Tana Sauke ajiyar rai a Fili ta Furta"Zan Burgesa..? Allah yasa ma ya Kalleni Nasan Halin Wanda na aura ba komai ke Burgesa ba..Zan so Tarkon na ya kamashi Can"t Wait naji Ya Imu ya Kalleni yana Fadin I Love u Inteesar..Bazan iya Rayuwa bki ba..! Tafada Hartana Kwakwaiyon Salon mganarsa Kafin ta Tsintire da Dariyan Farinciki Bakinta Ta Rufe jin Motsin Shigowarsa ya shiga Dakinsa kana ta Sauke ajiyar Zuciya gefen gado ta Zauna Tana Kara jiran Fitowarsa kamar yadda ta Tsara sai ta Fita Ta ja Fada daman ai basa mgana suna Fada ne. Yayi matukar mamakin ganin Dakinsa Tsab yana Tashin Kamshi Sai dai yasan Intee ce ta gyaramai Daki Mirmishi yayi yana Fadin"Allah Sarki..Yarinyar Tana da Hankali..Allah yayi miki albarka..! Yafada kafin ya ijiye Briefcase din Hannunsa ya Sabule kayan Jikinsa ya Shiga Wanka Har ga Allah yaji Dadin Ganin ko"ina na Tashin kamshi Sosai yayi wanka cikin jin Dadin Da Annushuwa aransa yana Fadin Ta Daina Fushin kenan..? Bayan ya Fito bai Tsaya Shafa mai ba Ya Saka Karamin Wandonsa baki 3Quater da vest wacce ta Dan kamasa Ya Tsaya a Hanya yayi Sallar mangariba Kishi yake ji sosai Gefe Daya yana jin yunwa kuma yau din ba Na Shan kayan Marmari bane na ya samu Abinci mai Rai da Lafiya yaci ne. Laptop dinsa ya Dauka akwai wani aikin da Manaja zai karba Ya fito Falo yana Takunsa Wayarsa Rike a Hannunsa kamar Dole yaki Sauya waya,Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya zauna Lokaci Daya yana Ijiye Laptop dinsa saman Center Table din glass din Dake Tsakar Falon Kamshin Girkin da kamshin Turaran Wutan Daya Gauraye Falon bai sa ya Zauna ba yanufi kicthen ya Dauko Ruwa a Fridge kafin ya Nufi Dining kai Tsaye ganinJerarrun kololi masu kyau da yarari a jeri Cikin Sha"awa da Burgewa Yana Daga Tsayen ya Bude Ruwan ya Kwankwada Rabi kana ya Sauke yana Sauke Numfashi kan Dining din ya ijiye Goran Hannunsa Lokaci Daya yana Bubbude Warmers din Da Pepe Chicken ya Fara cin karo Kamshi ya Dakesa Tuni Miyansa ya,tsinke sai kuma ya ci karo da Fruit Salt yana Turirin Sanyi ai Imran baima Tsaya ba yaja Kujera ya Zauna ya Zari Filet ya Diba Wannan Naman kazan Ya samu karamin Mug ya Diba Fruit Salt din Bata saka siga ba Shi ya saka ya Fara Lodama Cikinsa aransa yana Fadin"Yau Intee an sauko ba Mugunta..! Acikin Ransa yana Dariya yana Tsaka da CinNamansa ta Fito Daga Cikin Dakinta Cikin yanayin Takun Wahainiya Kowani Taku Daya Kirjinta na Shaking Tare da Kugunta Dayake karyawa duk inda tabi bai ji Fitowarta ba sai dai Kamshinta ne yamai Maraba ya Dago kansa yana kallonta Daidai Lokacin Dayakai Cinyar kaza bakinsa itama Shi Take kallo Direct suka Hada ido Gabadayansu sai da sukaji wani yam acikin Jikinsu Imran da gabadaya ya Kafeta da manyan Idanuwansa yana Kallomta Daga sama har kasa Ita kuma ganin haka yasa ta Kauda kanta Ta Kara Kaimin Takunta da dan Sauri Ta wucesa zuwa Kitchen Galala kamar Wani Sakarai haka ya Juya yana Binta da kallo Har ta bacema ganinsa. Nannauyar ajiyar rai ya Sauke sai Lokacin ya iya Tura Naman Daya Dauko Bakinsa yana jin wani Dum Dum a Tsakar kansa gabadaya Wani iri yake ji Inteesar ta Taimaki kanta Data Bacema ganinsa Domin ya kusa sume mata cikin yanayin Daya kasa gane Meyake Faruwa dashi. Bata jima ba sai gata ta kara Fitowa Dauke da Filet da Cokali nan ma ya Sake Binta da kallo yana mamakinta Yasha ganinta ba Hijabi ammh bai Taba ganinta da kayan da suka bayyana Surarta ba irin haka. Bai Taba Tsammaninhaka take ba yasha ganin mata Masu Cikar Hallita suna Mu'amala da mata a banki kuma yanayin Shigarsu mai bayyana Komai ne bai Taba ganin Macen da Cikar Hallita ta Dace da ita ba irin Inteesar ba Duk da bata da wani kiba kallon Kitse yake ma Rogo Tsab Ta mallaki mayan kayan da Kallon awajen Manya mata yake Tunanin Samu ashe Ashe Yana mata kallon yarinya ta Wuce da Duka Tunaninsa. Tasan yana kallonta shiyasa ta kariso Har Dinning cikin Tafiyarta ta yanga Bata yarda ta kallesa ba ta Duka Har Tana dan Bege Cinyarsa da Zata Diba Shinkafar da Miyar ganye ta Duka Sosai har Matsatsun na Shanunta suka Bayyana Daga sama Imran ya Hadu dasu sai kaji Mukut Sautin Wucewar Abu a makwogwaronsa Batare daya Shirya ba Inteesar na Jinsa Da ba domin ta Daure ba babu abunda zai hana bata Kwafsa ma kanta Wajen Kwashewa da Dariya ba Saboda yadda yayi Lokaci Daya yana Wani Zare ido kamar yayi karya. Fruit Salat din ta diba cikin karamin Mug ta saka Siga da yawa saboda Tana son Zaki sosai. Tana Shirin wucewa Dauke da Filet din da Mug din batare data Kallesa ba ya Daga baki yana Fadin"Inteen Daddy ba gaisuwa..! Yafada yana kallonta Cike da karim mamaki. Kai ta Dan kadai kafin ta Juyo Tana kallonsa irin sai ma yanzu na ganga ta Wani Tabe baki kafin tace"Oh..Sannu da zuwa..ai bansan ka shigo ba..! Tafada tana wucewa kan Daya Daga Cikin Falom ta Zauna yadda Zai Rika Fuskartata Galala yayi yana kallonta yadda ta Dora abincin Saman kujera batama kara kallonsa ba. Aranta ya Furta"Lalle yarinyar ta karo Wulakanci..! Kai ya Kada kafin ya sha Fruit Salat din Daya debo bai ma Cinyen Naman Dayasa ba ya goge Bakinsa da Tissue ya taso zuwa inda ya zama Wajen Zamansa Duk Dare ya Zauna suna Fuskarta,juna shi da ita Cikin Kufuluwa ganin yadda tayi wani kamar Bata gansa ba yace"Inteesar kin Rainani ko..?kina abu kamar baki ganni ba..? Dagowa tayi Tana kallonsa Lokaci Daya Tana saka Mug din bakinta ta Kurbi Abun Zuuu..kamar irin na yara Tana Tande Lebe batayi mgana Karkace kai yayi yau yaga Karshensa yarinya karama Zata Birkitasa Gabadaya ya kasa Daina Kallonta Duk abunda take yau Direct yake kare mata Kallo kamar Wani Maganadisu. Kansa ya shafa yana Fadin"Uhmm..Saboda kawai nayi miki Fada..Shine kike Fushi Dani..?shikenan ke baza"ayi miki Fada ba kenan..? Yafada yana Sakarmata Idanuwansa da suka Shanye saboda kallomta Cikin Bakkm yanayin da bai Taba Riskan kansa ba. Sai da takai abinci bakinta ta Hadiye Kana ta Dago Kanta Tana kallonsa Cikin Basarwa tace"Fushi kuma.?ni ba Fushi nake yi ba Fushi kuma ai sai manyan mata da suka san Ciwon kansu Ni karamar yarinya Dani bansan komai ba..Maganar Fada kuma ai ka Isa kamin Fada ko baka da Mtsayin Mijina kai din Yayana ne..! Tafada Lokaci Daya Tana wani Far da idonta kafim ta Dauke