Sashe 147
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inteesar ta kalli Munari cikin wani yanayi tace"Na shiga uku Munari ya Zan yi yanzu..? Tafada tana kwalkwal da Idanuwa kamar Zatayi kuka Munari ta gyara Zama Tana Fadin"Ya kuwa..?kin fa san Halin ya Imu mijinki ba irin na kowa bane Inteesar..Kuna son junanku ammh Soyayyar tana Wahalar daku baku Sani ba..! Inteesar ta Harareta Kafin tace"Ya akayi kikasan muna son juna..?in ni na yarda Yes ina son ya imu shifa kinga alamun Sona a tare dashi..? Tafada Cikin bayyana Damuwarta. Munari ta Dan yi mirmishi kafin tace"Wlh Ya Imu yana sonki..So mai Zafin da bai isa ya iya Guje miki ba..soyayyar Data shigesa batare Daya sani ba,Kema kuma kina sonsa soyayya mai Zurfin da baki san yaushe ta Fara ba Intee..! Inteesar ta kalleta kafin tace"Duk ya akayi kika san haka..?ke da ba Soyayyah kike yi ba..? Munari tace"Ni ina son soyayya ina son naga Masoya suna Kwasan Soyayya Raba Raba na Dade da Fahintar ku keda Ya Imu kyaleki kawai nayi Naga gudun Ruwanki,Sai kuma gashi komai ya zo karshe kun zama Miji da mata to ai zama bai ganki ba yarinya ba yanzu bane zaki kwanta kice zaki ja ajin nan ba Sai mun kamasa a Hannu in Tafiya tayi tafiya sai muja Zaran mu son ranmu yadda Zai zo ya fara ban baki da Lallashinmu batare da ya sani ba..! Inteesar ta Sauke ajiyar zuciya kafin tace"Munari Wlh ni kaina sai Daga baya na Fahimci na kamu da Son Yaya Imu ban Fahimci haka ba sai da aka Daura mai aure da Sajida kamar na Mutu haka naji alokacin..Ammh ni yanzu Damuwata Daya ne Shin ya karbi Aurena saboda yana sona ko Saboda ba yadda zai yi ne kamar na Sajida..? Munari tace"Saboda soyayyar dayake miki yasa ya aureki ba komai ba..Wlh Ya Imu yana sonki zaki ce na Fada miki Inteesar..! Inteesar tace"In hakane meyasa bai Taba Fadamin ba..?bai taba nunamin alama ba..? Munari tayi karamin Tsaki Tana Fadin"Shi Ya Imun ne zai Fada miki Yana sonki a wannan gabar ko..?U are not Serious Ai shi kanshi yana karyata kansa ne bai gama yarda yana sonki ba kece zaki sakasa ya Furta alokacin da bai sani ba..! Inteesar Tayi shiru kafin tace"Ta yaya..?ta wacce Hanya zan bi hakan ta Faru..? Munari ta Rike mata Hannu Tana Fadin"Ai kin Riga kin kama Zuciyarsa..Ya Imu bai taba bama Wata Mace dama a Rayuwarsa kamar yadda ya baki ba..Kin ga kenan kina da Babban Mtsayin da ba kowa ke dashi ba..yanzu gyarawa zaki yi ki Sani Ya Imu ya TSani Raini shiyasa bazai Taba Nemanki ba yana ganin in yayi Haka Zaki Rainasa,Ammh ke in kika Rika Nemansa ya zaki saka ya Fahinci kina basa Girmansa a mtsayinshi na Mijinki ko bai kiraki ba ki kirashi dan Text din ba Fasawa Zaki yi ba ki cigaba da yayi a wannan gabar Lokacin sa ne Ki bari namu Lokacin na gaba..Lokacin da zaki ja ajinki son Ranki kuma Dole ya Biyoki ya Lallasheki Saboda ya riga ya Fada Komarki Alokacin bazai iya Karyata Kansa ba bazai iya karyata Soyayyar Da yake Miki ba..! Inteesar ta gyada kafin tace"Yanzu me zan yi..? Munari ta gyara Zama kafin tace"Kiransa Zaki yi kice kin Kirashi ne ki gaishesa da aiki..In mun Tashi Daga School mu wuce gidanmu ki Dagaci dawowarsa Daya shiga Daki ki Dauki Ruwa ki bisa dashi In kika kai mai ke Macece kinsan yadda Zaki yi ki Tambayesa Yaushe yake ganin Za"ayi Bikin Tarewarku muji mai Zai ce..! Inteeesar ta jinjina kafin Tace"Allah yasa kada ya gwasale ni..! Munari tace"Dillah ke ce fa..?wlh baya gwasaleki..! Inteesar batayi mgana ba ta Fiddo da Wayarta acikin jaka ta lalubo Lambar Imran ta Kirasa wajen Kira Biyu tayimai bai Dauka ba ana uku sai ya Latsa mata Busy ta Dago kamar Tayi kuka Tana kallon Munari tace"Ya fa kashemin Kira..! Munari tace"Kara kira me nema ai yana tare da Hakuri..! Batayi musu ba ta kara Kira wannan karom bata Dade Tana Ringing ba ya Daga cikin Kaushin Muryansa na Koyaushe ya katseta Daga Sallaman Datake yi mai yana Fadin"Tunda kika ga kina ta Kira ban daga ba meyasa bazaki Fahimci ina aiki bane Inteesar....!!!! Yadda yaja sunansa sai da Jikinta ya amsa wani yarr Lumshe ido tayi kafin ta Bude,Munari na gefenta tanajin komai Duk da ba a amsa kuwwa aka Saka wayar ba Tanajin abunda yake Fadi Tunda suna Zaune ne kafada da kafada Zungurin Inteesar tayi ganin tayi Shuru Ta kasa mgana Sai ta Kalleta sai ta Fara mata alamun tayi mgana da idonta ganin tayi Shuru yasa yace"Kin Tsaidani ina aiki kuma kin yi shuru..?meyasa kika kirani..?any problem..? Da Sauri Inteesar Tace"Am..Ba..Bakomai..Daman na Kiraka na gaisheka ne ya aiki..? Yana Daga zaune saman kujeran sa Hannunsa Daya saman Laptop din Dake gabansa Dayan ne ya Sagala Wayar a kunnensa kafin yace"Kin kirani ne ki gaisheni..?yaushe kika Fara Kirana ki gaisheni..,? Bai bata Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Bakisan inda nake kwana bane..?Yarinyar nan Tsabar kin Rainani ma ni kike gani kina Guduwa kamar kin ga wani Sakarai ko..?na Kyaleki ne naga iya inda Zaki Tsaya ni ba Shashasha bane da zan saki aikin gabana na koma ina Lalacewa wajen Lallashin ki me akayi miki..?ko auran ne baki so..? Inteesar da idonta ya Fara cika da kwallah Tace"Yi hakuri.! Da sauri yace"No ba zencen yi Hakuri bane ko baki son auran ne kin fi so a warware kije ki auri wanchan Yaron..? Inteesar da Sauri Tace"Ban ce ba..! Tafada Tana Tura baki Sanyi yaji acikin Ransa kafin yace"To meyasa da kika gani kika gudu kina kuka..?na Dake ki ne..?kada fa ki manta ko ba Mtsayin Girman Miji ba ni yayanki ne so kinga ina da Girma Biyu a wajenki ammh na Lura baki kiyaye ko Daya ina Mijinki ammh Sai ki tashi ki Kwana ki Wunu baki neme ni ba irin U don"t care din ko..? Uhm ai yayi miki kyau zan kula Dakai na bana Bukatar komai Daga Wajenki sai dai bazan yarda ki Taremin agida da nayi mgana ki Faramin kuka ba..! Yafada kai Tsaye cikin kokarin Fadin Abunda ya Dade yana Damunsa acikin Rai. Kasa mgana Tayi jin tayi Shuru yasa yace"Is ok..ina aiki ne we tok later..Ko kuma in na dawo..! Da Sauri Tace"Am sorry..! Kansa ya shafa yana jin bacin Ransa na Sakinsa yace"Ya zan yi Dake..?ai dole na Hakura kada nace ban hakura ba ki Fara kuka Har sai Daddy daga Kaduna yaji Labari Tunda an Hadani da Shagwabbiyar kamarki ai an Hadani da aiki ni kuma gashi ban iya Lallashi ba ban da Taushi ko kadan Kananun kuka suna batamin rai Wani Lokacin ya za"ayi kenan..,? Dariya tayi batayi mgana Munari na gefe tana jinsu tana kallon Inteesar Wato Love kenan mai saka ko Sarki ne ya Rusuna. Jin Tana Dariya yasa yace"Au dariya ma na baki..?zaki yi bayani ne in muka Hadu..Later..! Yana Shirin katsewar wayarsa Munari na mata Rada tana Fadin"Banza kice i Miss u Allah ya dawo min dakai Lafiya Mijina..! Inteesar ta kalleta tana Kyafta ido Munari ta kara Fada tana wani kare Bakinta kada yaji batasan shi Tuni yaji ba har zai kashe Wayar yaji ana mgana Kasa kasa kunnensa kamar na Maciji yake yana da karfin ji sosai shiyasa ya Dakata mamaki ya kamasa Wato ma mara kunyar yarinyar nan Tana kusa kenan..? Ai shi fa ya gama Shiga Ciki Tunda ya auri Irin su Munari ammh Dole ya Tsare Giransa ya Tauna Tsakuwa Domin aya taji Tsoro. Bai yi mgana ba sai da Inteesar tace"Hello Ya Imu kana jina..? Idonsa ya Lumshe kamar Tana ganinsa yace"Uhmm..! Sai da ta Runtse ido kafin tace"Allah ya dawo min dakai gida Lafiya..And...! Ta kasa fada ta Fara Raba ido Munari na Zungurinta cikin Danne yanayinsa yace"And What..?Umh..!? Da sauri tace"I miss u...! Da sauri ta Datse kiran Tana Fadin"Ina jin kunya Munari..Ya Imu ne fa..! Munari tace"dillah sai me shi ba Namji bane..?ana koya miki yadda Zaki kamsa a Hannu kina wani Shirme ke kika sani Wlh ya ta baki Wahala..! Inteesar na shirin mgana wayarta ta Dauki kara Tana Dubawa ta Zaro ido Tana Fadin"Munari na Higesu Ya Imu ne ya Sake kira..! Munari tace"Shine me..?ki Dake ki Dauka kefa yanzu Matarsa ce kina da Damamarki da yawa ba kamar irin mu bace..! Jin haka yasa Hannunta na rawa Tana Dauka kafin tayi mgana yace"Saka wayar a amsa kuwa..! Cikin Zaro ido tace"Eh me kace..? Dakuna Fuska yayi kafin yace"Abunda kikaji a Farko..! Dagowa tayi tana kallon Munari itama Tana kallonsta kafin ta Sauke Wayar a Kunnenta ta sakata a amsa kuwwa. Cikin Nauyin baki tace"Na saka..! Gyara zama yayi yana Fadin"Sannu da aiki Jullet Uwar soyayya..?har ke ce kika tsara ace min i miss u ko..?Mara kunya yaushe kike..?da har kikasan ana kiran I miss u..?daman ba Karatu kike Tsayawa yi ba abunda kike koya kenan ko..? Munari ta kwaso Rantsuwa ya Dakatar da ita yana Fadin"Stop..Stupit ni sa"anki da zaki rika karanta mata abunda Zata ce min don Kaniyarki..?Jikin ki na kaikayi ko..? tsaya Tsaya ma waya baki Izinin miji da mata suna mgana ki shiga Tsakiya..?ke Matar aure ce ko uwar mata...? Munari da bata rai kafin tace"A"a..! Cigaba yayi da Fadin"Oh ko ni kuka maida abokin Wasanku..? wlh as from to Day in muna Mgana ki rika Tsshi Daga wajen ko Tarinki na kara ji sai na Tattaki kina so ki koyi Rashin kunya ko..?sai ki bari in kin kawo wanda kike so muka aurar Dake sai ki koyi gayamai U miss u..Bush gril kawai kuma ki bari mu Hadu Dake ki gani sai nayi kwallo Dake..! Bai jira cewarsu ba ya Datse kiran yana Jin Aransa na baci Inteesar din ce ta Rainasa ba wata ba itama zai koma Gidan sai ta Raina kanta. Munari kamar tay kuka Take Fadin"Daga Taimako..?ai shikenan..! Inteesar mai Zatayi banda Dariya Munari na Kallonta batace komai ba Ta sha kunu ta Dauki Lemonta ta Suri Jakarta ta wuce Inteesar ta Rakata da Dariya Lalle ne ma Ya Imu Wato munarin ce nawa take..? Bata san I miss u ba..Ita kadai in Ta Tuna Sai tayi Dariya sai da tagama shan Lemunta kana ta tashi tatafi Neman Munari Cikin Ajin Da suke Lecture ta ganta Tana karatu