← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 190

Sashe 111

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khamis da baisan da wanzuwar Imran Daga bayansa ba ya shagala da kallon kyakyawan Surar Inteesar da gashin daya kwanto ta saman Goshinta ya tafi dashi har baisan Sadda ya Furta"Wow..Beatifully.! Yafada Cikin wata Murya mai cike da Muradi mai girma. Imran Dake bayansa wani Takaici ne ya kara kamasa Tuni naman Goshinsa ya Tattare ya koma Waje Daya Inteesar yake kallo wace ke kallonsa Cikin Wani yanayi Dayake kara Wutar bacin Ransa. Kokarin Daidaita kansa yake shi yasa bai yi mgana ba Hannu kawai ya Saka Cak ya Dauke hannun Khamis dake Rike da Inteesar Cikin ZAfinsa har sai Da wajen yarfar da hannun Khamis yayi baya Ya fadi kasa Dabas Saboda Imran din da karfi ya Wanchakalar da Hannun nashi,Shi kuma ya saki Jikinsa ne saboda baisan Haka Zata Faru ba Shiyasa ya kasa Rike kansa Har Sai da yakai kasa. Da mamaki ya Dago suka Hada ido da Imran Dakemai wani kallo na rainin Wayau da kaskasci. Saurin Mikewa yayi shima Ransa ya baci Cikin Bacin rai yace"Mallam Lafiya kazo ka Tureni na Fadi kasa..? Imran ya Kara Hade rai bai yi mgana ba Ganin haka sai Ran khamis ya Fara Tafasa yana ganin Karshen Rainin Hankali Imran ya gama Rainasa shiyasa yakarisa gabansa ya saka Hannu ya Daki Kirjinsa yana Fadin"Mallam ina mgana ka kyaleni..? Wa ya baka izinin Tabamin hannu Har kana Tureni..? Yafada Shima Fararan Idanuwansa sun Fara Juyewa zuwa Jajaye Alluran Sojojin shima sun Fara aiki ajikinsa. Imran Dayake Cije baki Yana kokarin Daidaita Bacin ransa yaki cewa komai illah Inteesar ya kalla wacce Ta Fara Fiki Fiki da ido tana neman yin kuka ganin Abunda ke faruwa. Cikin Dakiyarsa yace"Ki koma Cikin Gida..! Tsayawa tayi tana kallonsa bata tafi ba Khamis ya kalleta yana Fadin"Tatafi ina..?Ina Ruwanka da ita ai bakai ka Kirata ba..Inteesar ba inda Zaki ok..? Yafada shima yana bata Umarni Sai kawai ta Tsaya ta kasa gaba Ballatana Baya,Ran Imran sai ya kara Baci Zuciyarsa ta Fara Tafarfasa Cikin Daka mata Tsawa yace"Nace ki bar nan..! Yafada Cikin Dakakkiyar Muryansa Cikin Fushi Daya Tsorata Inteesar ta Juya Zata Koma Cikin Gida tana Kokarin Boye kukanta da Hannunta Bayan ta saka Mayafin jikinta Ta Rufe bakinta dashi saboda kada kukanta ya Fito Khamis na ganin haka yayi Saurin Riko Hannunta again yana Fadin"Ba inda Zataje..Zan gani in kai ka Kirata in kuma Zaman ka takeyi Acikin gidanan..Haba rainin wayau ka ya Isa haka..Kana ganin cewa tsoron ka Kowa yake ji shiyasa kake yin Abu ba"a Tanka maka..? Wlh ina Daidai da Duk Abunda kake takama dashi Inteesar ba inda Zataje sai kayi abunda Zakayi in ka Isa..! Ya Karishe Fada Cikin Bacin Rai yana kuma Rike da Hannun Inteesar wacce take kokarin kwacewa ganin yadda Imran yake kallon Hannun nata kamar Zuciyarsa Zata Buga ya mutu gabadaya Cikin Kokarin Daidaita kansa yake fadin"Sakar mata Hannu..! Khamis ya kallesa yana Fadin"In naki fa..?Ko kana Tsammamin zaka Dakeni ne..? Imran ya Taune Lebensa na kasa Kafin Cikin Tsawa yace"Nace ka Sake mata Hannu Kafin Raina ya baci..Nayi maka Biji Biji anan wajen..! Khamis ya taresa Shima Cikin Tsawa yana Fadin"Naki na saketa din kayi Abuda zakayi..Ina Ruwanka in narike mata Hannun..?Au sonta kake yi..? Lalle baka da Tunani Shaye shayenka sun gayamaka karya in ka manta bari na Tuna maka Yau aka Daura maka aure da Sajida kanwata Ko agarin gaba gaba muke ana barin Halas ko don kunya..Ko kana so baka so Inteesar mallakina ne ina sonta kuma Zan aureta ita din Tawace..! Ya karishe Fada yana kara Riketa wannan karon harda Kafadunta duka Biyu. Ai Imran sai yaji wani Tukikin Takaichi acikin Raina Duhu ya mamaye idanuwansa na ganin yadda Khamis ya Rike Inteesar baisan Sadda ya isa gabansa ba ya saka Hannu ya Daki Kirjinsa da Hannunsa ya Kara Bangajesa da Karfin da sai da Ya kara Faduwa duk yadda ya kara saka Karfinsa Sai da Imran yadin ya kaisa Kasa Inteesar ta ja gefe ta fashe da kuka Jikinta ya fara Imran Cikin Dakakkiyar Muryansa Ya na nuna Khamis daya yatsa yake fadin"In ka kara Saka kazamin hannun nan naka ka Tabata wlh sai ka Raina kanka..?ubanta ne kai da zaka rika Tabata duk sanda kaga Dama..?Kuma daka ke fadin Shaye shaye bai fadamin gaskiya ba da kudin tsoho ko da na Tsohuwa nake shaye shayen..? Auran kanwarka kuma ninace ina sonta..? Nace ni nace ina sonta balle kazo kana gayamin mganar banza..Har Abada wannan yarinyar bata isa Imran ya sota ba Domin bata kai wannan mtsayin ba..Kuma na Rantse da Allah daya Halliceni in ka kara Cewa Inteesar taka ce sai nayi maka Dukan Mutuwa acikin gidan nan..Bazata taba zama taka ba Har Abada..! Ya karishe Fada yana Kumfar baki,Khamis da shima idonsa ya Rufe ya Mike jikinsa na mazari ya Fara Ture Imran yana Fadin"Kaima sonta kake yi kenan..?mallan sai ka Fadamin kishi kake yi domin na Tabata? To baka isa ba Inteesar da kamilalle ta dace ba Dan iska Sauran Shaye. shaye ba..Gashi na Riketa in baka Min Duka ba wlh baka Haifu Cikin uwa da u.! Bai gama Rufe baki ba Yaji Saukar Naushi a bakinsa yana kokarin rike hannun inteesar yaji wannan Dukan Daya sa sai da ya Duke yana Dagowa Bakinsa ya fashe sai jini Ya duba ya gani Hankalinsa ya tashi ya mike shima yakai ma Imran duka shima abaki shima nan da nan bakinsa ya fashe ganin yadda suka Fitar ma da kansu Jini yasa Zuciyar zaratan maza ta Fara Zalzal akan kishi Batare da bata Lokaci ba suka Sarke da Mumman Dambe Kowanne yana Dukan Dan"uwansa duk inda ya Samu da Karfin da Allah ya basu.. Inteeasar ta Dora hannu asaman kanta ta kwarara ihu dayaja Hankalin Megadi Dake bakin get ya Zuro da gudu ganin abunda ke Faruwa,yana kokarin Rabasu ammh ya kasa Inteesar ganin haka yasa ta Nufi Cikin Falon gidan tana Ihun Kiran sunan Daddy da Abba. Wanda daman duk suna zaune afalon suka fara jin Hayaniya sai ga Inteesar ta shigo tana kuka tana Haki Lokaci Daya tana Kiran sunan Abba da Daddy gabadayansu suka Mike Har wadanda ke Daki sai da suka Fito,Cikin Tashin Hankali Abba da Daddy suka Isa ga Inteesar suna Tambayanta meke faruwa Cikin Tashin Hankali.. Tana kuka Tana nuna musu waje Cikin Rawan baki take fadin"Abba...Abb..Imran..! Hankalin Abba ya tashi ya Riketa yana Fadin"Ki natsu Inteesar Ki Fadamana me ya faru da Imran din..? Inteesar ta girgiza kai Cikin Muryan kuka tana fadin"Abba Imran suna Fada da Khamis a waje..! Ido kowa ya zaro Cikin kidima kafin kowa yayi waje da sauri Abba kamar zai Fadi harta su Munari ba"a barsu abaya ba Baffa Kabiru da Mami Asma"u dake cikin Daki tanamai Rigiman gobe su koma Abuja sukaji kukan Inteesar suka Fito agabansu ta Fadi suna Dambe da Khamis ai Mami Asma"u kamar ta Kife Glass din Idonta na neman ya Fadi ta Fita Haraban Gida kamar ta Kifa Saboda Razama Harta Daada sai da ta Fito Falo jin wannan al"amarin Jikokinta Guda Biyu suna Fada da junansu. Yadda suka Fita suka iske wannan Fadan ya tashi Hankalinsu Cikin Lokaci sun jigata junansu,Khamis yana da karfnsu na Sojoji Shi ma Imran yana da karfi ga Zuciya Duka Idanuwansu sun Rufe basaaji basa gani. Abba da kansa ya Rike Imran da karfi Shida Yusuf da Sagir da Basheer Daddy kuma da Su Sa"id suka Rirrike Khamis suna sun hada ma kansu jini da majina,Matan masu Rauni sai kuka Irinsu Munari dasu Hafsah Mami Asma"u hannu ta Dora akanta tana Ihu Tana kururuwan Fadin Imran zai kashe mata yaronta Harta Sajida sai ta Fito sai kuka Baffa Kabiru Shima yana Cikin masu rike Khamis ganin yadda yake Zillo yana neman kwace kansa. Imram ma haka yake cida yana zillo kamar wani kadan Ruwa ammh su Abba suka Dannesa. Daddy ne ya Daka musu tsawa yana Fadin"Kai meye haka.?Meke Damun ku ne..? Kuzo kuna Dambe kamar Wasu yara abunda kannenku zasu yi ku yi musu fada ammh ku da kanku Zaku Zauna kuna Fada da junanku..ku Sake su naga wanda ya kara Taba Dan"uwansa in ya isa..! Ya fada Cikin Bacin Rai Sakinsu akayi suka koma suna maida Numfashi Imran ya Lakato jinin Dake gefen Bakinsa yana kallon Khamis yace Cikin Muryansa"Ba shikenan ba..Tabbas in ka kara maimaita kuskuran da kayi Wlh..Sai na Maka abunda yafi wannan..! Yafada yana Haki Khamis din Shima Yana Hakin yana Lakatan jikin Dake gefen bakinsa yana Fadin"In kafasa..Ai basai na kara ba..Mu Cigaba mana Uban wa kike tsoronka..! Yafada Cikin bacin rai kokarin kara Hadewa suke Mami Asma"u ta shiga Tsakaninsu Tana Fadin"Khamis zan ci Ubanka in baka bari ba..In shi bai da Tarbiya kai baka dashi ne..? Tafada Cikin kuka Sai ya koma ya tsaya yana Maida Numfashi,Imran kuma kallon Mami Asma"u yake kamar yayi ta Dukanta sai dai ya Taushi kansa,shima Numfashin yake Saukewa. Inteesar da Munari sun kamkame juna suna ta kuka Kowa abun baimai Dadi ba Mami Asma"u taja Hannun Khamis suka Nufi Falo Yusuf da Sagir suka kama Imran zuwa Cikin Falon Su Abba suka mara musu baya sauran ma Haka Daada na Falon tana Jiransu Ranta Duk ya baci Umarni ta bata Kowa ya nemi waje ya Zauna ya"yanta suka matsa gabanta. Ta shiga Fada ta Inda take shiga bata nan take Fita ba Ta nemi jin ba"asin me yafaru Khamis ne ya iya maida mganar Imran kuwa kala bai ce ba yana Gefen Sagir yana Sauke Numfashin Alamun Fushin bai gama Sauka ba. Khamis ko kunya yana Fadin Saboda ya Rike ma Inteesar hannu yasa Imran yace zai mai Duka Mami Asma"u Cikin bacin rai tace"Ya zata kaima Kanwar lasa ne da zai Latsa ka yaga Jini..D"ana Soja ne yasan Me yake yi..Kuma Daya rike mata hannu ina Ruwansa Wht is dey a taba hannu ai yar"uwansa ne bai kamata ya shiga ba Kowa anan Wajen yasan Imran bai da Gaskiya adauki mataki ko ni na Dauka bazam yarda adakeni kuma ahanani kuka ba..! Take Fada Cikin Bacin rai ba Zato ba Tsammani Imran ya Dago Jajayen Idanuwansa yana kallonta kafin yace"Waht is dey a taba Hannunta..?Shi Ubanta ne ko Muharraminta da zai Rika taba ta duk sanda yaga Dama.?ba Soja yake ba ko Shugaban Sojojin Duniya ne in ya
Chapter 111 · 0% Book details