← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 190

Sashe 15

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan Fitan Baba Asabe Alhaji Kabir Cikin Jimami da Damuwa ya Jinjina Hannun Daada Dake cikin nashi yace"Daada menene mtsalan ne wai..? Kinga ni bama mu kadai ba Hatta Baba Asabe bata son rasaki ballatana mu ya"yanki da bayan Rasuwar Baffa kece komai namu mu da iyalanmu yau in kika Fadi kika Mutu ina kike so mu saka kanmu..? Kafin kiran Baba Asabe Dr.Madina ta kirani Tun satin chan Daya wuce ta fadamin yadda Jininki baya kasa Daada kullum sai kara Hauhawa yake yi Ta rasa Dalili Daman ina ta Shirin Tahowa aikine sukamin Yawa Cases gareni har uku Shiyasa baki ganni ba Sai jiya da Daddare da kiran Baba Asabe ya sani Dole na Biyo Jirgi Daganan na Hawo taxi zuwa nan..!
Ya karishe Fada yana kallon Daada wacce ta ke sharan Hawaye kamar wata karamar yarinya kafin ta Dago Tana kallonsa tace"Bani da wata Damuwa sai ta Dan"uwanka Kabiru..Ace yau wajen Shekaru uku bashu ba Labarinsa Shi da iyalansa..? Anya an taba irin wannan Kuwa batan mutum ba Daya ba ba Biyu ba..Kabiru..?
Ta karishe Fada Cikin Taruwar kwallar acikin Idanuwanta.
Fesar da Numfashi yayi yana kara Nazarin yanayin Daada Daman yasan Tatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki..Damuwar Daada Gabadayanta ta Malami ce Shiyasani kowama ya sani.
Cikin Lallami yace"Daaad kiyi Hakuri don Allah..ki kwantar da Hankali wannan Abunda kike yi bashi bane mafita..Ina so ki Sani Malami fa ba bacewa yayi ba..Ko kuma wani Mumman Abu bane ya same shi ba fa..? Daada da kansa ya Zabi yayi nisa Damu yaje inda Bazamu taba ganinsa ba koda Mun Nemesa..Kada ki manta Dani da Mustapha mun Taka Har Chan inda suka zauna Nemansa bamu san iyaka ba mun samo Miki labarin Da kansu suka bar komai nasu Daada..Gidanshi bai saida ba sai dai sun Rufeshi Jami"ar Dayake koyarwa munje Shima ba wani bayani haka Ma"aikatun da yaransa ke aiki munje sun Tabbatar mana da Cewa Sun ijiye aiki da kansu Daada..Kuma Har yau bamu Daina nemansu ba Saboda ke Daada..Na saka a saka ido saosai duk Randa akaga wani Cikinsu na Bada Lambar a wayata a kirani ammh Har yau babu Wani labari Daada..!
Ya karishe Fada Cikin Bayyana Takaichinsa indai ya Tuna da Abunda Dan"uwan nasu ya aikata..
Cikin Sanyin Murya Daada tace"To ina zasu tafi..? Ina jin Tsoron kodai wani mumman abu ya same su..?
Alhaji Kabir yace"Ina ji ajikina babu abunda ya Samesu..Ko Satin Daya gabata naje banki..Na saka an Bincikamin account din Malami an ga ana Cire kudi Lokaci Bayan Lokacin kinga kenan Duk inda suke suna chan suna Rayuwarsu Daada Sun manta Damu da komai nasu Batare da wani Tunani ba..!
Daaada ta Girgiza kai Tana Fadin"Ban yarda Malami zai manta dani da ku yan"uwansa da asalin gabadaya ba..Kada ka manta Faruwar abunda ya Faru ya Taba kwakwalwar malami baya Cikin Hayyacinsa..Laifin na ya"yansa ne Musamman Babban..!
Alhaji Kabir cikin jin Haushi yace"Bai fa Haukace ba Daada...Ciwon Damuwa ce kawai ai Bai fita Hayyacinsa ba yasan Daidai da Rashin Daidai..Na yarda ba da son Ransa suka tafi ba Sai dai ina da Tabbacin da saka Hannun wannan Yaron nashi mai Taurin kai da Zuciya wanda kaf cikin Dangin bansan ina ya kwaso wannan Hallayar ba shine zakka a acikin wannan zuru"ar namu Daada.!
Duk Halin da Daada ke Ciki sai da ta Murmusa Cikin girgiza kai Tace'"Ba Zuciya bace Kabiru..Haka Hallitarsa yake mutum mai saurin Fushi da Fusata Akoda yaushe ina yi musu Uzuri da addu"an duk inda suke Allah ya karesu..Ni Karamar nake Tsausayi tunda itace Mace basu san kowa ba Duka Dangi suna nan Dukku,Dangin Uwarsu ai Nice nan Kabiru Tunda ni na yaye Zuwaira na Riketa har ta girma Mahaifinka ya aura ma Malami ita ina ji ajikina Duk inda suke suna chan su kadai Cikin kewa da kawa Zucci.!
Ta karishe Fada tana Sharan kwallh yana kallonta bai ce komai ba sai da ya Numfasa kana yace"Kada ki damu Daada..Insha Allahu muna iya bakin kokarin mu da yardan Allah zamu dawo da Malami Cikin Ahalinsa..!
Daada taji Dadi ta kara Damke Hannayen Kabir tana Fadin"Haka nake so naji Kabiru..Allah yayi muku albarka kaida Sauran yan"uwanka..Nasan ka kirasu duk ka shaida musu Tun Safe Bintalo da Maimunatu da Mustpaha ke kirana ban Daga ba Saboda nasan aikin Asabe ne..!
Ta fada TanaFadada Mirmishinta,shima Mirmishin yayi ganin ta saki Ruwa ya Dauka ya Tsiyaya yasha ya ijiye Kofin kafin yace"Nida Mustapha kadai mukayi mgana Da Safe Daada..Nayi mai mganar tahowa mu hadu dashi muyi miki mgana kila zaki fi jin mu.Sai kuma yace min kano yake Shirin Tafiya shida mai Dakinsa zasu kai yar wajensa Zata fara karatu anan Buk kano,To yacemin yayi ta kiranki baki Daga in na iso na kirashi in bashi kuyi mgana..!
Baki Daada ta saki kafin tace"Badai wannan Sangartattaciyar yarinyar nan Mustapha zai kai wata uwa Duniya da Niyar Karatu ba..?
Alhaji Kabir na Dariya yace"Kai Daada..Takwarki ce fa...Kike Fada da ita..!
Karamin Tsaki Daada taja kafin tace"ammh kuma bata Biyo Halina ba...ayi yarinyar sai Sangarta da Sokanci ta girma ita ba yarinya ba Duk Mustapha ya bata yarinyar nan Shiyasa sam bana Shiri da ita ko nan garin bata zuwa ko Uban ya matsa sunzo Tare bata ko yarda ta kwana tasan Halina Kaniyarta nake Ci ni ba"a zuwa gidana ace za"amin Sangarta da Sakarci..!
Shidai yana ta Dariya kafin yace"Shiyasa Sajida tace Daada Rigima kamar me..!
Daada tace"Ita ma kaji wata yar Tselan uwa nan..Ita bata da Sangarta sai dai Shigen kiyuwa da Son jiki..Duk Asma'u ta gama batasu dakai..Gwara ma Umaima tafi ta kazarkazar,ammh Duka nafison mai sunan megidana Hamisu!
Alhaji Kabiru yace yana yar Dariya"Shima zaku fara fada in har yaji kina cemai Hamisun nan..!
Daada tace"Ni rabani da Fi"ilinku na yan zamani..Hamisu shine sunan kwarai ba wani Feleke ba..Yana ma ina kwana Biyu ban jisa ba..?
Yace"Yana chan Anambara inda yake aiki kila ya shiga Ruwa ne..Muma kwana Biyu bamu yi mgana dashi ba..Sajida kuma ta Fara karatu anan Base Universty ba Zama Umaima kuma kinsan Bana kinta da kulafuncin Uwa sannan itama ga makaranta ba Lokaci..!
Daada ta gyada kai Tana Fadin"Allah ya rayasu...ya kuma bada sa"a da Rayuwa mai kyau ya kuma yi muku albarka ya kara arziki..!
Ya rika amsawa da Ameen kafin ya Dora da Fadin"Nazo da kayan abinci da Dankalin Naga kamar naku yayi kasa ne..!
Daada tace"Akwai sauranshi..Kai da yan"uwanka bakwa gajiya ko Sati Biyufa ba"ayi ba Bashir dan wajen Mustapha ya kawomin kayan Abinci da kudi hakama Itama Bintalo ta aiko Direbanta dashi..Babu abunda zence muku sai Allah yayi muku albarka ya Raya muku Zuru"arku suyi ta muku hidima kamar yadda kuke yi mini..!
Alhaji kabir yace"Ameen Daada..In bamu yi miki ba wazamu yi mawa..? Ai bamu da kamarki Allah dai ya kara Tsawon rai..! Lokaci Daya yana Lalubo wayarsa daga cikin Aljihun wandonsa
Daada ta amsa da Ameen daidai Lokacin da Alhaji kabir ya Kara wayar akunni yana Fadin"bari na kira Mustapha Daada..!
Kai ta gyadamai kaunar ya"yan nata nakara Ratsata,tana fatan Allah ya cika mata Burinta na Hada ya"yanta waje Daya

*****
Chapter 15 · 0% Book details