← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 190

Sashe 146

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Umaima kuwa ta samu Daddy a waya Dayaga Kiran sai da gabansa ya Fadi bai da lambartaa ammh kiran Waya da Daddare haka yana Fadar ma Da Mutane gaba,Umma Tayi barci Tun Dazu Shima Wani lissafi ya Tsaidashi yasa bai yi barci da wuri ba.
Koda ya Daga Kiran Kukan Umaima ya Faramai Maraba Dakyar ta Tsagaita Tamai bayanin Abunda ke Faruwa Salati ya saka Cikin Rashin jin Dadin Abunda ya Faru ya lallahi Umaiman yace mata da Safe zai kira Abba in ta kama ma zasu zo nan Abuja Haba ai bazasu bari haka ta Faru ba,da kalaman Daddy Umaima taji Sanyi tasan Zasu ja Hankalin Dad ya Dawo da Mami gida.
Salatin Daddy ya tada Umma Daga Barci,Cikin muryan barci Take Tambayansa ko Lafiya cikin Damuwa yake Fadamata abunda ke Faruwa ita kanta Sai ta Dafe Kirji Tana Fadin"Saki..? Abun har yakai ga Saki ne Abban Inttee..?
Cikin jimami yace"Gashi kuwa..Allah dai ya kyauta bari na kira Ya malami muji yadda zamu yi yariyar tana ta kuka ko Saboda yaran..Da kuma an Riga an girma bai kamata ba..,!
Umma ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Karamar ce ta kira ko Sajidar..!
Daddy yace"Karamar ce Umaima..!
Umma tace"Allah ya kyauta..Da ka bari sai gobe da safe ka Kirasa yanzu Dare fa yayi sai ka Tayar mai da hankali..!
Kansa ya jinjina alamun Ya yarda da mganarta,Barin kiran Wayar yayi ammh Lissafin da bai karisa ba kenan abun ya Damesa da asuban Fari ya Kira Abba ya Fadaamai yana ma Hanya ne zasu dawo daga masallaci su Yusuf sukayi gaba suka barsa suna mgana shi kanshi bai ji Dadi ba suka Tsaida mganar dashi da Daddy zasu Tafi Abujan su samu Baffa Kabiru Ranar Alhamis,Saboda Abba zai Fara aiki Ranar Monday ne da haka suka Rabu Zukata duk ba Dadi.
Abba bai yi Zencen da kowa ba Shima Daddy bayan Umma bai Sanar ma Kowa ba Baffa Kabiru bai kirasu ba kuma suma basu kirasa ba suna Jira ne kawai ya gansu kwatsam
Aranar da yammah Yusuf yakai Abba Wajen Siyan Mota yace ya Zabi Wacce yake so Abba ya Zabi prado babbar ta Imran baka mai kyau miliyan 6 Sabuwarta nan take yusuf ya Biya kudin bai kai ba Sai da ya Hada Sauran kudin acct dinsa.
Tare da Motar suka isa gida atare Yusuf ya Sallami Wanda ya Rakosu da Motar.
Zuwan Motar ne yasa da Munari ata fadama Inteesar yasa ta jawota Dole tazo taga Mota tayima Abba Murna,Tana ta wani Sunne kai Abba ya jawota Jikinsa yana Fadin shi baya Suruka da ita yarsace ita Ya yusuf kuwa ta Daina Hada ido dashi gogan kuwa Tunda ga Ranar bata kara ganinsa bai nemeta ba itama bata nemesa ba.
Ranar Laraba sun fito daga Lecture din Safe ita da Munari Cafteria suka je suka siyo Lemo da Biscuit,suka Samu wani Inuwa bakin wani Department suka Zauna sun fara shan Lemon kenan suna Hira Wayar Munari tayi kara Tana Dubawa Taga Hafsah ne ta Dauka suna mgana Inteesar na kallonsu duk kan Shagalin da zasu yi da Bikin su ne Suna Fadin zasu bude Bride group za"a Saka ango da abokansa suma zasu sako kawayen Bride.
Munari na Dariya tace"Ke ango bai da Babbar Waya sai Rakani Kashi..!
Gabadaya ita da Hafsah suka saka Dariya Inteesar ta Hade rai Tana Hararanta.
Daga chan bangaran Hafsah tace"To sai mu kyalesa Daman ko yana dashi ke zan jona ki sako manashi..!
Munari ta waro ido Tana Fadin"Wa ni..?Rufamin asiri waya aikeni ballatana yaga na Dade..?
Wlh badani ba yaga ni Sakashi ki auna yadda zaizo ya sauyamin kammani..!
Dariya Hafsah ta Saka mata Munari ta Cigaba da Fadin"Abokai kuma Daya na Sani Ya Sagir..Kuma bamu da Mtsala Dashi..Kawaye kuma Imu imu ne daga ke sai Nasara sai ni sai Tasleen kanwar Anty Safiya Bana jin Intee nada wasu kawaye..!
Hafsah tace"Shikenan ma hakan yayi wai yanzu yaushe Date din Bikin..?Naji ya Sa"id na cema Anty Faree Daada tace wannan na Hannunsu Baffa kuma yace sun yi mgana da Sadam yace Baffa Mustapha yace Date din Biki Sai ya Imu ya Saka Rana da kansa Tunda shine mai gayya da aiki..!
Munari tayi Sakai sakai kafin Tace"Topha ya Imu muke jira kenan..? Dankari..!
Hafsah tace"Nima abunda nace kenan..Ita ai maatarsa in mu muna jin tsoro ita Ta tambayan mana shi mana Muna so muji Lokacin ne yadda zamu Tsara abubuwanmu..!
Da wannan Shawaran suka Rabu Tsakanin Munari da Hafsah.
Inteesar Tayi bakan tana jinsu batace komai ba..
Munari ta Zungureta Tana Fadin"Nasan kina jina da Hafsah ko..?
Mganar Tarewarki ce..Ance fa su Daddy sunce mganar Sanin Hakikanin Date na wajen Ya Imu..!
Yamutsa Fuska Inteesar Tayi kafin Tace"Sai akayi yaya..!
Munari ta Kalleta Cikin mamaki kafin Tace"Kamar ya..?Tambayo mana shi Zakiyi yaushe ne ya Tsaida Lokaci saboda Shirye shirye.!
Inteesar ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"Abunda ni ko kulani ma bayayi..Tunda aka Daura mana aure ko dan irin Text messages babu ballatana Kira..Nima kuwa na Sharesa bai nemeni ba nima ban nemesa ba Tun Ranar Monday da muka Hadu kofar gidansu Mama.!
Shakeke Munari ke kallonta kafin Tace"Au ke daman kina Jiran ya Nemeki ne...?
Kin manta Waye ya Imu..?Dankari na Rantse har ga Allah ko Tarewar kukayi ke za ki sha Wahala in har kina Tsammanin ya Sauke wannan Egon nashi ya Nemeki u are mad ma Wlh Ya Imu fa..Kai ai kina ma Cikin Masifarsa zai ce kin gama Rainasa Intee..!

*Shakira..*
3/25/22, 22:52 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�20*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Chapter 146 · 0% Book details