← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 190

Sashe 155

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na gefe Kunya duk ta kamsa yadda Sagir da Khalil ke wani Rawan jiki kan kannen bayansu Hade rai yayi ya kauda kai,gabadaya suka gaida kowa da kowa har da su Ya yusuf Imran dai ta saman Lebensa ya amsa yana dan duba duben ta ina zai ga Inteeesar din..? Waje Sagir da Khalil suka ja yanmatan suna mgana ganin Tuni mutane sun Fito an Fara Lonching din ba Amarya ba ango Tunda Lonching din Harda Manya su Umma kenan da gayyar Kawayenta. Maman Nasara ta Fito da Inteeear ta Zaunar da ita inda aka Tanada Domin Amarya da ango guda na tashi da Kida mai Taken Aure ya Dauri sannan su Sagir suka shiga suka Fito da Imran Dakyar kamar Dole alhalin shima yana so ya Fito yaga Inteesar Rashin ganinta fa agaresa kamar Cuta ne. Wow..Kawai Mutane ke Fadi sai tashin Flash din masu Hotunan da aka Kira Lokacin da Imran ya daidaita Zamansa kusa da Inteesar Khalil ya Harde Hannu a Kirji yana kallon Munari lokaci Daya yana Fadin"Wow...Wow..What a Perfect March...! Haka yake fadi ita kuma Tana ta Daukansu Hoto Tana Fadin"Kai Ya Imu yayi kyau..Wow..Intee na Besty Wlh They are made for Each Other..! Khalil kallonta kawai yake yi ammh Beb din ai ta gama Tafiya dashi Kowa Masha Allahu kawai yake Fada Na ganin Tsabar kyau Zati da Haiba Wajen Imran da wani Kwarjini Duk da Fuakarsa bata saki ba ammh yayi kyau matuka Inteesar bata iya Hada ido Dashi ba kanta na kasa tana Wasa da Zobon Dake hannunta na Gwal yana kyalli. Imran dai yagama Hade Ransa Dole ya Karkace kai yana kallon Inteesar Baisan ya Kafeta da ido ba sai da ta Dagosuka Hada ido gabayansu sai sukaji kamar mayen karfe ya makalesu su Sagir dasu Munari suna ta Ihun Dariya suna Fadin kallon Love an kashe Hotuna cikin wannan yanayin ba adadi kafin Imran ya Fara Farga ya kauda kansa da Sauri yana wani Dakuna Fuska Inteesar ma kanta Ta maida kasa Tana Dariya. Anci an sha a wannan Wajen anyi Rawa an Taba Bidi"a Umma ma tazo Tajawo Amarya da ango cikin Fili Ta Rika Sakar musu Mannin yan Dubu Dubu ita da Maman Nasara da Goggo Maimunatu da ya"yanta ganin haka yasa su Sa'id ma suka shige suna Rawa suna Manni Har da Ya yusuf da su Munari gabadaya Iyalan Daada ne sun Shige suna rawa suna Liki Imran na Tsaye kikam kamar Gunki ba Domin Umma bace da kanta da sai yace Umma abarma yara mana yana nan Tsaye yana Bin Inteesar da kallo kamar ya Lasheta haka yakeji ga wani Kamshi na tashi ajikinta Inteesar taji gyara soaai Umma ma bata Tsaya kunya ba ta gyara Diyar ta Ciki da baya. Sagir ne yazo ya Hada hannunsa da nashi ya yafito su Ya yusuf suka zo suna ta Jansa da Rawa Hararansu yake yi ammh basu san yana ma yi ba Hayaniya ya ishi Imran ammh sai Mangariba aka Tashi Daga wannan Taron sai kuma Gobe in an isa Kano. Gabadayan sun gaji Saboda Zirga Zirga,Ya Basheer gidansa ya kaisu Imran suka kwana Tunda gabadaya Matan suna Gidan Umma saboda Shiryan Shiryan Tafiya da Safe. Sagir da Khalil dai sai chan dare suka Dawo suna gidan Umma Tare dasu Munari suna kara shirya Dinner Gobe Imran Harara kadai yake maka musu in suka Hada ido su kuma suyi tamai Dariya Allah kadai yaaan me suka Shiryamai gobe. Garin Allah na Wayewa Daddy yace su Fara Harama Domin su tafi da Wuri,Masu Karatu zan so ku hangomin kukan da Inteesar tasha na Rabuwa da Umma da Daddy tana Sanye Cikin Nadin Lifaya,Gaban Umma Tana ta kuka Umma ma sai Hawaye tana ta sakama Inteesar albarka. Ta Rumgumeta Tana Fadin"Umma ki yafemin..! Umma na Sharan kwallah Tace"Na yafemiki Duniya da Lahira..Allah ya Zaunar daku lafiya..! Dakyar Maman Nasara ta iya Raba Umma da Intee su Munari basasu iya gani ba Tuni suna Haraban gidan Tare dasu Sagir inda suka sanya kayansu Amota ai kuka sai Agaban Daddy ita da Imran ya Hadasu yayi musu nasiha sosai ya Hada hannayensu yace su Zama Bangon junansu Daga Karshe ya Bisu da addu"an Zaman Lafiya yadda Inteesar ta kamkame Daddy tana kuka ko shi Imran din sai da ya Taausayamata ya Rikota acikin Jikinsa yana Lallashinta Daddy kuma baya ya Juya yana Dauke kukansa. Maman Nasara tazo ta kamata zasu Fara biyawa ta badarawa gidan su Inno Kafin su wuce inda Kawunanta ke chan zasu mata Nasiha. Ya Yusuf shi zai Dauko Amarya a Motarsa Imran Motar Sadam ya shiga shida Goggo Maimunatu dasu Zainab,Suka Farayin gaba Su Sagir suna Tare da su Munari shi kuma baya son Harka da yara Shiyasa ya kama kansa akwai Motoci Tunda ga na Daddy da na Ya Basheer,sai nasu Goggo Bintalo itama da Mota tazo da Direba ita da ya"yanta Har Gidan Inno da ita aka je bata yarda ba sai taga Komai Saboda taji Dadin Kyankyasama Mami Asma"u gulma. Achan gidan Inno ma Inteesar tasha kuka su Kawu bala sun mata Nasiha sosai da Inno da Mallam Babba Muda Yana makaranta chan ya koma sun Fara Jarabawa shiyasa bai Taho ba Basu jima ba achan ba suka Dauko Hanya Maman Nasara na Rike da ita da Anty Hauwa Yusuf na Driving Anty Jamila Diyar Kawu Bala Tana gidan Gaba. Basu yi gudu Bisa Hanya ba sai 12 suka iso kano tuni su Imran sun Dade da isowa kuma Gidan Sadam din suka yada Zango,Ya Damu yana so yaji ko Inteesar ta iso yana ta Kiran wayarta Bata Dauka ba sai daga baya aka Dauka yaji Muryan Sagir na Fadamai sufa suna Hanya kuma wayar Amarya Tana Wajen su Munari Tsaki yaja ya Datse kiran wai meyasa bata Rike wayanta ne sai ta Rika bama Shashanshan yaran nan Ya ja Tsaki yafi a Kirga kafin ya Kira Ya Yusuf shi yake Fadamai sun iso har su Maman sun zo Taran Amarya zuwa Cikin Gidansu Gida ya Cika Makil suma Haraban Gidan Cike da Mutane an saka Kanofi da kujeru Hajiya Anty Safiya yayar Ango mai Masaukin baki Taci Gayunta kamar Wata Amarya. Taro Ta Hada itama gagrumi sai wanda ya gani Hajiya Mero da Danginta sun yi kara soaai Mama itace Uwar ango ita da Kaltume Matar Baba Manu,Abba dai Dole ya bar Gidan zuwa Cikin makaranta Saboda Gida ya Cika ba Mtsaka Tsinke.. A Shashen Anty Safiya aka Sauki Amarya Inteesar Wacce ke ta kuka Cikin lifaya Gefe da gefenta Maman Nasara da Antya Uwani matar kawu bala,Anty Hauwa Tuni ta shige Cikin su Aneensa an hadu ana ta Shewa da Hiran yaushe gamo bata ga su Munari ba Tadai san tun a gidan Daddy ta barsu kila suna Hanya gashi ba Waya a Hannunta Ballatana ta Kirasu. Sai 2pm na Rana suka iso wai Mai ne ya Tsaya musu a Hanya Motar Sa"id suka Shigo matan mazam kuma Motar Basheer Gidansu Imran suka ijiyesu tunda nan ma akwai yinin Biki suka wuce gidan Sadam koda sukaje Tuni su Imran har sun yi Sallah sun Wuta sun ci Abinci suma Sallar sukayi suka ci binci suka Zauna Zaman Hira da Labarin yadda Dinner anjuma Zata kaya. Imran na gefe yana jinsu to me zai ce..?bai isa yace komai ba yadda Khalil da Sagir suka Hada kai ai sun fi karfinsa sai dai ya Bisu da ido Gidan su Imran kuwa Biki fa yayi Biki Anty Safiya ta Kira dan Asharalle yazo Yayi kida Mata sun chase Har da ita ga Ciki ga komai ita dasu Anty Hauwa Ko Nauyin Jikinsu basa ji,Harda Inteesar duk sun Fito Haraban gidan suna kallon Rawan manya mata Goggo Mainunatu tayi rawa itama ta Kira Bidi"a Sosai kowa kagani yayi anko Tabbas Anty Safiya ta yi gayyah kuma an Mata kara sosai Tunda Shagali ne Wanda ba"a taba yi ba Duk Tsawon Shekarun da suka Shude Dole abiya bashi. Chan na hango yan Dandalin GMB2BANDGROUP,Suma sun cakare cikin ankonsu sun sha kyau har sun koshi sai hotuna suke da Amarya Inteesar bakinsu yaki Rufuwa Yau gasu ga inteen Imu duk da basu samu ganin Imun ba sun Rage Zafi. Sai yammah aka tashi Wannan Rawar Makota da yan"uwa wadanda baazasu kwana ba sukayi Haraman Tafiya masu Shirin Tafiya Dinner kuma suka Fara Shirya Daman already Munari sun Dauko mai Kwalliya wacce Zatayi musu na Tafiya Dinner kawayensu na Buk abokan arziki suma duk zasu je Wajen Dinner maza da mata. Pass dinka shine Code din Dressing din Dinner din shine pass din Shigarka. Amarya ko kafin 8:00pm Tayi an gama Shiryata kuma 9pm za"a Fara Dinner din,an Shiryata Cikin Less mai kyau Skya Blue itama an mata Nadin Head Deep blue,sai Daga baya an yafa mata Wani yadi mai Santsi Sya blue yana da Kwalliyan Deep blue na Duwatsu yana Daukan Ido Har kasa yanasharan kasa haka Jakarta ma Deep blue pos sai Takalmin kafarta ma Haka mai Tsini Shima Deep Blue Wata Kwalliya akayi mai mai kyau da Yarari Cikin Lokaci kamar ba ita ba kafin a Fara Shirya Sauran kawaye Tunda Sagir ya kira suma Kadan ya Rage su karisa Shiryawa zasu zo su Dauke su. Ango Imran yasha Shadda Deep Blue da Babbar Riga da Hulansa Zanna Bukar mai Zanen aikin jikin Shaddan Skya blue sai Takalmin Kafarsa Baki ne Rufaffe na Matar Damisa sai Agogon Hannunsa na Kamfanin DKNY,yayi kyau har ya gaji da kyau Kayan Dinkakku ne,,aikin Ya Yusuf ne suma sun Cakare da nasu Kalan Shigar na deep Blue din Shadda ammh su ba Babbar Riga,Har da su Ya Sa"id domin fa sun ce suma matansu Zasu je suma bamai barinsu a baya Ballatana Ya Yusuf da kafarsa kafar Matarsa Anty Safiya,Wacce Har Hajiya Mero zata Hallaci Wannan Dinner ita da kawayenta Da yan'uwanta irin su Anty Saratu. Karfe 9 da wasu Mintina su Sagir suka Kariso a Motar Abba Ango da Amarya zasu Shiga Abba ya Dawo saboda Mutane yana Gidan Sadam shima. Sai sauran Motocin kuma zasu Dauki Sauran Mutane. Sai Kiran su ake yi Hall din mai suna Mina Event Center fa ya Cika Damkam da Mutane su kadai ake jira,Imran na bayan Mota ya Hakimce yana jiran yaga ta ina Inteesar zata Bullo..? Ai kuwa yayi kyakyawan gani
Chapter 155 · 0% Book details