← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 190

Sashe 68

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa afalon sai da ya juyo yana kallon Mami Asma"u cike da mamakin kalamanta ba ga yaran Dake Zaune ba har ga manya irin su Inna Maimunatu dasu Umma,ammh ba suyi wani mamaki ba sanin Halinta daga ita Har Mijinta da yarda suke gudanar da Tarbiyan ya"yansu. Ko ayanzu din ma yana gefe yana ji ammh kanzil bai ce ba Sai Khamis din ne da kunyar kalaman Mamin suka Rufeshi ya kasa mgana illah kada kai da yayi ya tashi ya koma Kan kujeran Dake Fuskanta Hanyar Kitchen din Dake Falon Daada so yake ya kara Kallonta Domin tagama Tafiya da Duka Tunaninsa. Mami Asma"u ta yatsina Fuska Hannunta kan Fuskar Sajida tana Shafawa tana fadin"Am sorry dota..Kada ki damu kwanta abunki bamai Takura miki indai ina Raye..? Tafada Tana kara Kwantar da Jikinta a gefen kafadanta Cikin bayyana Soyayya da kauna da Sangarta Da suka nuna mata.. Kowa kauda kai yayi bai yi mgana ba Sajida kuwa ta kara nanikewa Jikin Uwarta Bata da Niyar tashi Inna Maimuna taga Abun ya wuce Misali Ta kalli Mami Asma"u Da hankalinta ke kan wayarta tace"Hajiya Mami ai gaskiya Khamis ya fada..Da kike fadin ko agida bamai sakata aiki ba kanshi yake ji ba sai ita yau Sajida mace ce tana gabanki gobe gidan auranta Zataje in yau kin tsaya mata Zaki gidan Mijin nata ne ki ZAuna mata ki bar naki Gidan...? Tsakani ga Allah fa Mu Tuna ya"yan nan Amana ne agaremu ko ba gaskiya ba..?in na Fadi ba Daidai ba ayi hakuri..! Tafada kanta Tsaye Ran Mami Asma"u ya baci ta Dago Tana kallon Baffa Kabiru itama ita yake kallo Zatayi mgana ya Girgiza mata kai sai shine ya Kalli Inna Maimuna yana Fadin"Maimuna kina Nufin ban bama Ya"yana Tarbiya mai kyau ba kenan..? Yafada Cikin Bacin rai da Sauri tace"A"a ko Daya ni ba kai nake nufi..! "Ok bashi kike Nufi ba sai ni..Tunda nice Bare shi kuma Dan"uwanki ne ko..? Mami Asma"u ta katseta Cikin Fushin mganarta Daman ga Takaichin Zuwa ba Shiri,Inna Maimunatu ta Kalleta Cikin mamaki ta Bude baki Zatayi mgana Sa"id Dake gefe yace"Mommy plz..! Yamaata alamun hannu a saman bakinsa ganin haka yasa ta kada kai kawai tayi shuru,Inna Bintalo Dake gefe Tayi Yar dariya kafin tace"Nifa ina mamakin wasu mutanen Shikenan da Zarar ka bama yayanka Jin Dadin Rayuwa sai ace ka batasu to waya ki jin Dadi da Rayuwar Hutu..Ke Maimuna da kike Fadin Watarana Aure Zatayi in da kudi Yan aiki zasu bika Duk inda kake Sai dai ka sa ayi maka kana Bada Umarni..! Jin Haka yasa Mami Asma"u ta samu bakin mgana Cikin gatse tace"gayamata dai Binta..Naga alamar kin fita saurin gane abubuwa..Shikenan in kana Bama ya"yanka Duka Tarbiyan daya kamata Kana basu jin Dadi duk sai ido ya koma kanka..? Domin wa muke aiki Koda yaushe..? Saboda ya"yanmu ne kuma Dadin abun nima ina aiki Ballatana ace da jikin wani na Dogara ko bana aiki mu yan gidan na gada ne ba na Haya ba..kuma Alhamdulillah ko acikin Dangi ya"yana sun fita Dabam dana kowa..! Tafada lokaci Daya tana Sakin Siririn Tsaki Lokaci Daya ta maida kanta bisa Wayarta Umma Dake gefe ta kada kai kawai domin aHalin Mami Asma"u wanne ne bakonta..?. Ba wanda ya kara cewa komai sai Falon yayi Shuru,Sai ya"yan Inna Bintalo ne keta mgana kasa kasa Baffa Mustapha kuwa maamakin yayan nashi ya kamashi ganin ko Sau Daya bai Tsawarta mata sai Fadin mgana Take son ranta. Inna Maimunatu dai tunda Sa"id yayi mata mgana bata ma nuna tana Wajen ba jikanta ne a Hannunta yaron wajen Karima An yayeshi Daman Wajen sati biyu kenan Uban da uwar suka kawosa Bauchi yana Wajemta,Madara take bashi Ta Toshe kunnenta Bata ma nuna taji ba ballatana tace wani abu ba. Falon ya dau shuru na wani Lokaci Sai su Sa"id ne ke mgana da Basheer sama sama sai Inna Bintalo da ya"yanta Sai ga dawowar Baba Asabe Falon Dauke da manyan Kololi,Bayanta Hafsat ne Dauke da Filtes da Cokula,Sai Umaimah Dake Dauke da Mug din Kofuna a hannunta Daga baya kuma Inteesar ce Dauke da Kananun Vowl a hannunta Tana Tafe Cikin Sanyinta da Natsuwarta Gefen hannunta kuma Dauke da Katon Kwalin Tissue. Tunda suka fito Idanuwansa ke kanta Ita ajikinta taji ana kallonta ta Duka Zata ijiye abunda ke hannunta Ta Dago suka Hada ido sai ya Daga mata Gira,Ganin haka yasa ran Inteesar ya baci tayi saurin kauda kai Tana Mikewa Lokaci Daya Tana gyara Zaman After drees din Dake jikinta Sam bata yarda da Khamis ba kallon Dayake mata ya Sabama irin kallon da addini ya amince ya shiga Tsakanin Namiji da mace shiyasa duk ta Tsargu kanta,ita ana ta Tunamin bai dace yana kallonta kamar zai Cinyeta Danya ba. Wajen Daddy ta karisa ta Karbi Jakarta Hafsah ce ta kariso wajenta Tana Fadin"Kawo jakar muje Dakin da muka sauka..! Kamar Inteesar zatayi mata Musu sai suka Hada ido da Umma ta gyada mata kai Shiyasa ta sakarmata Jakar Umaima ma na ganin haka ta kalli Mami Tana Fadin"Mami ina kayan mu..?nima Dakin su Inteesar zan sauka..! Wani Harara ta Sakarmata kafin ta saki karamin Tsaki Tana Fadin"Kibari Ki sauka inda zan sauka keda Sajida..! Baba Asabe Dake duke tana Bude kololin Da ta kawosu take fadin"Ai bamu da mtsalan Masauki kun sani..Daada tasan tana da Zuru"a kowani Daki ta sa an gyara mata shi..Ke Umaima ki sauka inda Hajiya Zata sauka ita da Sajida ke kuma Inteesar sai ki sauka Dakin da Hafsat ta sauka Umman kaduna ta sauka Dakin Daada,Wadanan surukan namu kuma sai su sauka Daki daya,Inna Bintalo da ya"yanta Daman suna Daki Dayane Inna Maimunatu ne jiya ta kwana Dakin Daada,Mazan kuma suna Wanchan Flat din na korido Daman chan su Sa"id suka sauka Jiya da suka iso..! Ba wanda yayi gaddama da Hukuncin Baba Asabe saboda duk abunda tace kamar Daada ne ta Fadeshi. Umarni da ta basu kan su sauko suyi Breakfast,rana tayi ba musu Iyayan suka Fara Saukowa Kafin Matansu sai ya"yan Daga baya Khamis duk yadda Zai yi sai da ya Zauna Facing din Inteesar saboda ya rika Morema Kallonta ita kuwa duk sai ta Takura ta Kasa Sakewa duk Dagowan da Zatayi sai sun Hada ido yana Binta da wani Mayattacen kallonsa Dataji kallon bai Burgeta. Ganin haka yasa Tea kadai tasha sai Soyayyah Dankali tatashi bayan tace ma Hafsah wani Daki takai mata Jaka na nuna mata Dakin Dake kusa da Dakin Daada Tayi,Daddy ne ya Kalleta Tana Shirin wucewa"Intee Daddy badai har kin koshi ba..? Kai ta gyadamai Tana Fadin"Eh Daddy nasha Complex kafin mu fito Daga Gida..! Kai ya gyadamata bai ce komai ba Gabadaya da kallo aka Bita,Inna Bintalo Harda tabe baki,Umma na Lura da ita aranta tace kya yi dai ki gama Binta. Sai da ta Fara Lekawa Dakin Daada taga kan gadon ba Kowa alamun Zubar ruwa a bandaki yasa Tayi Tunanin tatashi Tana Tiolet ne sai ta Fice ta isa Dakin da Hafsah ta nuna mata komai Neat akwai gado sai Katifa babba Dake kasa Dakin bakomai sai Cafet din Daya mamaye Dakin sai Tiolet Dake gefe wajen jakarta ta Nufa Da Hafsah ta ijiye mata nan kan gado,Zama Tayi agefen gadon Tana Tunanin yadda Zata iya kwana agidan Daada yau tagama Fahimta akwai abunda badai dai ba..Dazu fa sun fara karyawa Suka Hada ido da Sajida ita har ga Allah bata ma lura da ita akazo ba sai alokacin kallon kallon sukayi ma Juna kafin kowacce Ta dauke kanta Inteesar mamakin Sajida ya kamata ganin yadda Kowa ya Zauna a Matsayinsa ammh ita Tana Nanike da Mami Asma"u kamar wata yarinya ganin Haka yasa ta saki karamin Tsaki abun ba tsari kwata kwata tasan Tana da Shagwaba ammh nata na masu aji ne ba na irin nata ba.Shiyasa duk zaman wajen ya Gundureta da kuma Kallon da Kamis yake Binta dashi ita haka Kurum taji kallon bai mata kama da kallon Mutanen kwarai ba Daga ganin idanuwansa Ya saba kallon mata koda ga yadda yake wani Kashe mata ido. Karamin tsaki taja acikin Ranta tace Dan"iska kawai. Daganan Wayarta ta Ciro a jaka tadan Kishingida Munari ta Kira sukayi mgana ta Fada mata suna Dukku in sun Dawo gobe kila Jibi ta Tadawo in kuma basu dawo ba Dole sai Saturday ko sunday ne dawowarta. Sun dade suna mgana kafin suyi sallama Daganan game ta farayi da wayarta sai barcin gajiya ya kwasheta ta Bingire ta fara barci batasan tayi barci da yawa ba sai da Taji Hayaniya akanta kana Taji Ana kiran sunanta Tana Bude ido Taga Anty Hauwa Tsaye akanta Mikewa tayi tana Mutseke ido,Tana kallom Anty Hauwa Kafin tayi mgana sai taga wasu na Sallah Ido ta Zaro tana Fadin"Anyi Sallar Azahar ne Anty Hauwa..? Anty Hauwa na saka Hijabi jikinta tace"Eh mana gajiyan Hanya ne yasa baki san kinyi barci mai yawa haka ba..! Mikewa tayi tana Mika saboda Bayanta ya Sage,Hafsah ce ta Fito Daga Tiolet tana kallon Inteesar tace"Kin tashi..? Inteesar tace"Eh wlh..ashe nayi barci da yawa haka..! Hafsah tace"Nima na shigo na ganki kina ta barcin nace gajiya..Nima jiya da muka iso haka nasha Barci na Har sai da nagaji..! Mika Inteesar tayi kafin tace"Daada tatashi Daga Barcin..? Ta daga mata kai Tana Fadin"Tun dazu..Tana Ma Falo ana ta Hira da ita ta Shige cikin ya"ya da Jikoki..! Inteesar ta kalli Hafsah kafin tace"Wai Kiran menene Daada ke ma kowa ne..? Hafsah tace"Wlh bansani ba..Ko muma da muka iso Tun jiya taki cewa komai tace sai gabadaya an gama Haduwa Zatayi mgana..! Inteesar kai kawai ta jinjina ta Tura Kofar Tiolet ta shiga Domin ta Dauro alwala,Yadda taga Tiolet din Tsab a wanke yasa ta kwabe tayi wanka Saboda Jikinta ya saki Daganan ta Dauro alwala koda ta Fito su Anty Hauwa sun idar da Sallah da Aneesa Matar sa"id da Faree matar Sadam suna Hira sama sama,Hafsah kuma na Gefe kan Darduma. Wajen jakarta ta Nufa ta Bude ta Dauko Wata Doguwar riga Ja da gyalenta,ta koma cikin Tiolet din ta saka kana ta Fito ta maida kayan Nata Data Cire cikin jaka. Hijabinta kwara Daya da tazo dashi ta Dauko ta sanya ta Tada Salla nan gefen da Hafsah ta matsa mata. Bayan ta idar
Chapter 68 · 0% Book details