Sashe 85
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba da jikinsa ke rawa idanuwansa sun cika da kwallah suna shirin zubowa Lokaci Daya ya fara takowa Tsakiyar falon duka Idanuwansa suna Kafe kan Sadam kamar wanda ya warke makanta.. Cikin wata irin Murya kewa da Farinciki da kuka Abba ya kalli Sadam yana Fadin"Sadam...! Ya kira sunansa cikin wani yanayi Sadam da Hawayensa suka gangaro saman Fuskarsa yace"Na"am kawu malami..! Yafada yana wani kada kai Abba Hannayensa ya Budemai yana Fadin"Taho nan Sadam Taho naji Dumin ka..Taho na ji dumin wani Daga Cikin Ahalina yau..! Da gudu kamar karamin yaro ya Karisa ga Abba suka Rumgume juna Lokaci Daya yana Fadin"Kawu ina ka shiga muna ta neman ka..? Kowa ya shiga damuwa saboda kai..Daada kowa yaushe kuka take yi yau lafiya gobe babu duk saboda Rashinka..! Abba yaji Hawayen dayake ta Tarewa sun zobomai yayi Saurin Sharewa Lokaci Daya ya dago Sadam yana Fadin"Ban je ko"ina ba ina nan a kasata..Nayi nesa da gida ne saboda Wasu Dalilai ko bamu hadu ba daman Lokacin da Zan koma cikin Dangina yayi ba saboda kowa ba ko Saboda Daada da nike kwana ina tashi da ita..! Kada kai Sadam yayi Lokaci Daya yana Dauke kwallarsa Dagowa yayi suka Hada ido da Yusuf dayake sharan Kwallah Wajensa ya nufa yana Fadin"Dan"uwa Yusuf..! Lokaci Daya suna Rumgume juna Inran na gefe yana Binsu da kallo Fuskarsa bata bayyana Wani Hali yakeciki ba na Farinciki ne ko na bakinciki. Inteesar da Munari gabadaya sun Shiga Rudani sai bin kowa da kallo sukeyi ita dai Munari ta Fahimci Yau boye boyensu ya kare ne Dangin sun san inda suke ita kuma Inteesar ta Shiga Rudanin kada dai ace Munari yar"uwanta ce..?Abba shine Baffa Malamin da su Daddy ke wahalan nema Daada na Rashin Lafiya Saboda shi ammh take zaune dasu tsawon Lokaci bata taba Sani ba. Aneesa na gefe farinciki ya cikata Harta su Waleed sun natsu ganin yadda Abbansu ke kuka yana Rumgume da Yusuf,sun dau tsawon Lokaci kafin su saki juna Sadam ya Bubbuga kafadarsa yana Fadin"Shekaru uku ba kwana bane..Duk ka Sauya Yusuf..! Yusuf na Dariya yace"Kaima haka duk ka Sauya..! Dariya suka saka gabadayansu Abba na Gefe yana kallonsu Lokaci Daya yana karama Allah godiya daya sa Daada bata bar gidan Duniya ba Tana da Rayuwarta zai koma mata.. Sadam ne ya juya yana kallon Imran Lokaci Daya ya Karisa gabansa yana Fadin"Imran ko .? Yusuf ne ya bashi amsa ammh Imran Sai ya wani basar Kallon ma wani barayin yayi kamar ba dashi yake ba ganin haka yasa sadam bai Rumgumesa ba illah ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Dan"uwa kai bamu san ka sosai ba..Ko a da chan Yusuf ya fika son zumunci .! Kamar yana mgana da gunki haka Imran yayi mai Abba ya Kalleshi yana Fadin"Imran sadam ne dan Wajen Goggon ku Maimunatu ta Bauchi..! Dakyar ya iya bude baki yace"Na ganshi..!. Daga haka ya dauke kansa Sama Sadam bai damu ba ya jinjina kai aransa yana ayyana abubuwa Dadama kan Imran din . Inteesar ne data gama Shiga Rudani ta Kalli ya Sadam Tana Fadin"Ya sadam...Abba..!. Tafada Tana kallonsu dukkansu da Sauri Sadam ya Karisa gabanta ya Riko Hannunta yana Fadin"Inteesar baki gane su ba ko..? Baki ga Hoton da Daada tace a nuna ma kowa lokacin da mukaje dukku ba..? Inteesar cikin kosawa tace"Bangani ba meya faru..?kamin bayani ka sani a duhu naji kana cema Abba Kawu..Kawu malami kardai kacemin Baffa Malami ne..! Ta karishe fada cikin wani yanayi gabadaya sai kallo ya koma kansu harda Imran daya natsu yana so ya Fahimci wani Abu.. Abba ya Kallesu cikin mamaki yana fadin"Sadam..! Lokaci daya yana nuna Inteesar da Hannunsa,Sadam ya kamo Inteesar zuwa gaban Abba yana fadin"Kawu baku gane juna ba..Abba Inteesar itama yarka ce..! Cikin mamaki yace"Yata kuma..? Imran ya waro ido yana so ya Fassara mganar hakama Yusuf Munari kuwa Hawaye take yi na Farinciki koda ba"a Fadi komai ba ita ta san kaunar dake Tsakaninta da Inteesar ta jini ce. Sadam ya dauki hannun Inteesar ya saka cikin na Abba yana Fadin"Kawu Inteesar ce Diyar Kawu Mustpaha na kaduna..! Abba yaji wani sanyi jiki ya kamashi Lokaci daya da Sauri ya damke hannunta yana Fadin"karamar yarinyarsa..Wacce taci sunan Daada..! Sadam ya dagamai kai yana fadin"Itace kawu..Inteesar ce kana Tare da jininka ammh baka sani ba..! Abba ya Ji hawayensa suna Kokarin kara Zubowa ya Rike Duka Hannuwan Inteesar yana fadin"bamu rike zumunci ba sosai ba...Ace yau na hadu da Diyar Mustpaha na wani Lokaci Tana Tare damu ban ganeta ba..Sai dai Wlh har ga Allah Tun ganin Farko da nayi mata naji wani abu acikin Raina ban taba mata kallon bare ba Daya na Dauketa ita da Munari Ashe Ashe itama Diyata ce..! Yafada cikin Raunin Murya da Sauri Inteesar da itama ta fara Hawaye tace"Baffa....! Tafada kafin ta fada jikin Abba tana fadin"Nima ina jin haka duk sadda na kanga sai naga kamar Daddy na..Yanayin mganarku da komai iri Dayace..In nazo gidan nan ji nake kamar ina Gidanmu in ina tare da Munari kamar ina Tare da yar"uwata uwa daya uba Daya..Ashe Gidanmu ne ku din Jinina ne Wayyo Dadi Abba..! Take Fada tana kuka Shima Abba Hawayen yake yi Shi da Sadam da Yusuf Da Aneesa da Kukan Farinciki ya Kamasu Lokaci Daya,Imran ne kadai ke Tsaye idanuwansa ba alamun Fitar kwallah sai dai yadda abubuwan suka Juye ne suka sakashi Tsintar kansa a wani Hali Tabbas Jini yafi Ruwa kauri,ko shi yasa Yafi damu da Inteesar fiye da kowa..? Ashe ita din jininsa ce..! Anty Safiya Dake gefe tana sharan kwallah Tun dazu ta fito ba wanda ya Lura da ita Hayaniya taji ta Fito tana Kwance afalo acikin Shashenta sai ta iske Abun Farincikin daya samu wannan Gidan ayau na cikon Abu Dayan da ya Rage gidan ya cika ya zama Gida irin kowani gida. Yusuf ne ya hangota da sauri ya isa gareta ya Rumgomta yana fadin"Noor Boye boye ya kare..Danginmu sun same mu..!. Tana rike dashi Tana Fadin"Alhamdulillah..Duka Burikana sun cika my dear..!. Take fada cikin Farinciki. Inteesar na kuka ta dago kanta tana Kallon Munari cikin kuka tace"Dilla ke baki zo muyi kukan tare ba. ? Tafada Lokaci Daya Hawaye da Dariya da sauri Munari ta wani taho da Sauri ta Fada Jikin Abba dukkansu ya Hada ya Rumgume sai ga Hawayen Farinciki sharr. Sadam Wayarsa ya zaro Tun dazu Sa"id ke kiransa bai dauka ba cikin Farinciki ya kirasa yana kiransa Ringing daya ya daga da Sauri yana Fadin"Sadam ya ake ciki..? An dace kuwa. !? Sadam na kallon Abba yana fadin"Sa"id an dace gani ga Kawu Malami..Alhamdulillah gani cikin gidansu Zagaye da iyalansa..! Sa"id ya mike da Sauri yana Fadin"Finally Alhamdulillah..! Bai ma jira cewar Sadam ba ya Katse kiran Murta ta sa ya rasa nayi,Komawa yayi ya zauna yana Hamdala afili kafin kuma ya Fara Tattara kayansa yau komai Dare sai ya Shiga kano Sadam ya kara Kira yana Dauka yacemai kada ya bar gidan nan yanzu zai tashi daga Office yana zuwa Gida zai taho kano ayau din nan bai iya cemai kada ya Taho ba domin ya kamata yazo din. Abba kuma yana Rike dasu Inteesar Hawayensa yaki tsayawa yana Kaicon wannan Zumuncin na wannan Zamanin da har yakai mu ga Lalacewar da jininka na tare dakai ammh baka sani ba. Waje aka samu aka zazzauna Saman kujerun falon Abba ya fara Tambayan Sadam sauran yan"uwa yana Fadamai kowa Lafiya Imran na gefe bai Zauna ba ya Harde Hannayensa saman Kirjinsa yana jin duk abunda ake fada sai dai kalma Daya Tun bayan na Dazu bai kara Furtawa ba bama wanda ya Damu dashi sanin Hali Sadam ne ke yawan kallonsa Lokaci bayan Lokaci yana mamakin shi wannan Haka yake.? Abba ne ya kalli Aneesa yana Fadin"Wannan mai Dakin ka ce..? Sadam yace"Eh Abba..ga yara na nan Waleed da waleeda. ! Abba ya mikama su hannu yana Fadin"Ku taho nan wajen kakan ku da baku sansh ba..! Basu da bakunta suka karisa Wajensa ya Daukesu asaman jikinsa. Munari da Inteesar na gefe sun rike hannun juna baki yaki Rufuwa Safiya na Cikin su da Yusuf cikin Farincikin da bazasu misalta ba,Shiyasa tunda ya Fara ganin Inteesar wlh jininsa ya bashi Intadin kamar jininsu ce,bai taba mata Wani kallo ba ashe jini jini ba na waaasa ba. Abba na kallon Waleed yace"Nasan sanda aka Haifi babban..Lokacin Maimunatu ta Kirani take fadamin Matarka ta Haihu wacce muka je cikin garin Azare muka karbo Auranta..! Sadam na dariyan Farinciki yace"Anyi haka kawu tabbas baka manta ba..! Abba na Mirmishi jin dadi yace"Ina Yayanka Sa"id da sauran kannen ku mata..? Kayya zumunci sai a hankali duk ban sansu ba..! Sadam yace"Sa"id na Garin Dutse Abba chan yake aiki yana zaune da matarsa da ya"yansu uku..Karamar kanwarmu Hafsah tana Wajensa saboda Tana karatu nan Federal Univestiy dutse. ! Abba ya jinjina kai yana Fadin"Ku kiramin yan"uwana inaso na Hada dasu yau..Gobe ina so naje ni da duka Iyalaina naga Daada na Roketa gafara..!. Imran na gefe ya kalli Abba irin Kallon nan nasan za"azo wajen bai dai ce komai ba Sadam ne yace"Kawu saboda Murna ban ma kira kowa ba Sa"id ne kadai shima yace yana Tafe yau din nan bari na fara Kiran Mommy na Fadamata..! Inteesar dake gefe tace""Ni kuma bari na Kira Daddy na fadamai..!. Dukkansu atare suka Kira wayar Sadam na Kira Mommy ta Daga Cikin Murna tana Fadin"Sadam yanzu nake shirin kiranka gama wayata kenan da Dan"uwanka yana gayamin wani Labari mai dadi kaga Yaya Malami da iyalansa..? Tafada cikin wani Shauki Saukewa wayar yayi daga kunnensa ya saka Speaker yana Fadin"Wlh Mommy gani ga kawu ga yusuf ga Imran ga Inteesar Mommy ga Matar yusuf din dan wajen kawu malamin har yayi Aure .! Inna maimunatu tana kwallah tace"Hadani da dan"uwana naji muryansa..!Sadam bai yi gaddama ba ya mikama Abba wayar ya Karba yana Fadin"Maimunatu Autan Daada..! Tana jin muryansa sai kuka tana Fadin"Ya ya Malami ashe kana da Ranka..? Ka samu lafiya Allah abun godiya..! Cikin wani yanayi yace mata"Na warke Maimunatu..Na samu Lafiya da ikon Allah..!. Inna maimunatu tace"Allah mun gode maka da kakaddara Haduwa Tsakanin daada da Ya malami..Nima bazan iya zama ba bari Alhaji ya shigo na gayamai yau din zan taho kano..! Da sauri Abba