← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 190

Sashe 144

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 8:30pm na Dare ya shigo Gidansa,Mami Asma"u ma bata Dade da shigowa ba gidansu ta wuce Mahaifinta ya kirata awaya yace Tazo yana son ganinta Justice Tafida. Duk da Justice Tafida yace mata ta Janye Ra"ayinta ammh bata ji ba shi kuma Dan Boko ne mai akidar Dabaya mtsama ya"yansa kan Ra"ayinsu zai gayamaka gaskiya Ruwan ka ne kayi aiki Dashi ko kar kayi aiki dashi Shi dai bazai Tursasaka Dole ba kayi Karatu kasan Daidai da akasinsa. Hajiya Turai ce ta rika Zuga yarta ta batayi Tunanin abunda kan je ya dawo ba Mami Asma"u saboda Tana ganin kamar abun kunya ne aji wannan abun ya Faru da yarta yasa ta Roki mahaifiyarta karta Fadama kowa cikin yan'uwanta Asma"u basu da yan Uba Hajiya Turai ce kadai Matar Juctice Tafida tun auran Saurayi da Budurwa. Da wannan Famfon Asma"u ta Dawo Gida Allah Sarki Umai ce kadai agida Daga ita sai yan aiki,shiyasa saboda Kada kadaici yayi mata yawa data yi wanka Ta sauya kaya ta Sauko kasa ta Zauna Wajen Umaima Wacce take assigmemt din da aka basu a makaranta ta Hanyar Browsing a wayarta. Bata ce ma Mamin komai ba bayan gaisuwa saboda ba Huruminta bane Ammh Tabbas akwai Mtsala Tsakanin Mami da Dad din,Suna nan Zaune ya shigo Kallo Kallon sukayi ma juna Shida Mami Asma"u shi ya Fara Dauke kansa Umaima ce tataso Ta Rumgumesa tana yimai Welcome lokaci Daya tana karban yar karamar briefcase din Dake hannunsa ya Haura Sama tabi bayansa Mami Asma"u ta bisa da Hararan kasan ido gobe goben nan Zata je ta shigar da kara taga mai hanata Har Dakinsa Umaima takai masa Jakar ta Fito ta barsa zai yi wanka bayan ta Fadamai tana Jiransa ya Sauko su yi Dinner. Saboda Umaima yasa bayan yayi wanka ya saka Jallabiya ya Sauko kasa Direct Saman Dining ya Nufa Umaima na ganin haka tace ma Mami itama Ta taso,suci abinci Saboda Umai yasa ta Mike Tana wani Takun isa ta karisa Saman Dining din ta Zauna gabadayansu haka sukaci Abincin kowa na saka abunda zai Fishasheshi acikin Ransa Umaima ce kadai ke karadinta ita Kadai duka iyayen Daga Uhm sai Uhm ne Har suka gama cin Abincin kowa ya Watse Umaima Dai Dakinta ta Shige Ta karisa assigment dinta ta kwanta daman ka"idan Gidan da Wuri kowa ke shigewa ya kwanta taji ta samu natsuwa Dazu da sukayi mgana da Sajida bayan ta Dawo makranta Ita Sajidan ta Kirata sai dai yanayinta a Sanyaye yasa tasan Zarginta ya Tabbata wani abu ya Faru ko yana kan Faruwa Sun rabu da Sajida kan Umaima din zata zo ta ganta Ranar Sati a makaranta Tunda ita Sajidan tace ba zata samu Dawowa Gida Weekend ba wannan Satin. Akallah ta samu natsuwa bada yawa ba. Misalin Sha Daya na Dare Baffa Kabiru ya gama Duba wasu Tarkadu kan Shari"ar da suke kai ne Kana ya Mike ya Fice Daga Dakin nashi Sai da ya Fara Leka Umaima yaga tayi barci kana ya Rufomata kofa Direct Dakin Mami Asma"u ya Nufa Daman Saboda Kada Umaima taji Sa"insan da ita ne yasa ya bari sai ta kwanta barci. Bai Tsaya ma mata Knooking ba kawai ya Tura kansa Lokaci Daya da Sallama Fitowarta Daga wanka kenan ta Saka wata doguwar Riga mai Taushi Ta barci shirin kwanciya Take yi ya shigo. Dakata tayi da kokarin Zama kan gadon ta gyara tsayuwarta Tana kallinsa shima kallonta yake yi Cikin Wani yanayi sai dai bai Hango Nadama a Tare da ita ba yasanta Tana da Kafiya da Taurin kai,Ko a Sharia in ta samata naci bata sukuni sai Tayi Nasara. Gyara Tsayuwa yayi Lokaci Daya yana Harde Hannunsa ya goya a bayansa Cikin Kallonta ido na ganin ido ya Fara takowa zuwa gabanta suna Tsaya suna Nazarin juna na wani Lokaci ita ta Fara kauda idonta a Kansa saboda ai Namiji ne bazata iya Juran kallon Cikin Idanuwansa ba. Cikin dan Sanyin Murya yace"Asma"u Meyasa kika cike complain Form..? Kai Tsaye yayi mata Tambayar yana kallonta Tana kallonsa Dan mele baki tayi Tace"Kafini Sani..! Yana kokarin Boye bacin Ransa yace"Wa zaki kai kara..? Mahaifiyata ko yan"uwana..? Mami Asma"u bataji wani ko Dar ba Tace"Dukkansu..Zan yi kara Domin da saka Hannunsu Rayuwar y'ata ta ragu,je in kai kayi shiru ni bazan yi Shuru ba sai na kwaci yancina..! Bata gama Rufe baki ba ya Tare ta da Fadin"Yanci ko..?ina yancin..? Ke kisan wani abu wai shi yanci ne..?In yancin kike nema shi aka baki kin nuna bakisan auran Sajida da Alokacin na mara Miki baya saboda son da nike miki yanzu kuma an yi miki Abunda kike so kuma ya Zama abun Tozarci a wajenki..?ke wata irin macece mai son kanta Asma"u..? Baki Tunanin kowa sai kanki.?tunda mukayi aure na Sakar miki Duka wani Dama hatta da Damar dangina Duka na baki ina bin Duka Dokokin ki kamar kice Mijin nice matar..Ina jin mganarki ina Danne Ra"ayi na Saboda na Fitata naki Ra"ayin Duka wannan abun bai isa yasa ki gane ke mai son kanki bane..?ki duba irin abunda kika aikata a Dukku Saboda na baki Dama kika cima Daada Zarafi kika Hada da yan"uwana ke baki ji kunya ba..?in nayi ma iyayanki Haka zakiji Dadi..?nace ki Duka ki bata Hakuri gaban Duka Kowa da kowa kika Nuna ban Isa Dake ba Nima ba kowan kowa bane a Wajenki,Sanadinki Daada tayi Fushi Dani kinsan Dafin Fushin Uwa kuwa Asma"u..? Kuma Duk da Hakan bai isheki ba Sai kuma kika Bullo da wata mganar banza na zaki kai uwata da yan"uwana kotu ke gaki Ubanki Tsohon Alkali kuma ga ki Lauyar gwannati ko..? To Shege ka Fasa Asma"u ni kuma zan nuna miki Jini yafi Ruwa kauri Uwa da yan"uwa suna gaba da kowa a wannan Duniyanan nagodema Allah Dayasa na gane kuskure tunda wuri kuma da yardan Allah Duk Zan gyara inda na kuskure ba kyalekin da nake yi bane yasa kike Wasu iskancin ba To kiyi yanzu nagani nace kiyi yanzu na gani din in ban yi mganinki ba..! Har ya gama mgana Mami Asma"u bakinta a Bude Tana Binsa da kallon Mamaki Kafin tace"Ni yau kake Zagin Ubana Kabiru kan gaskiyata..? Kai Tsaye yace mata"Eh an Zaga din Ashe Uba yafi Uwa ko..! Naki iyayan yan Daraja ne kuma yan gold ne ashe kina Sane nawa uwar kika Raina..! Cikin Bacin Rai tace"Iyayena sunsan Abunda sukeyi bazasu taba aikata abunda Taka Uwar ta aikata ba...Mai son kanta kawai..! Cikin Shima Bacin rai da Hargowa ya nunata da yatsa yana Fadin"In kika kara Fadin kalma Daya na batanci kan Daada sai na Bata Miki rai..! Azatonta Burga yake mata sai ta gyara Tsayuwa Cikin Gatsali da Hargowa tace"In nace fa..? Me zaka iya Kabiru..?Na Fada na kara Fada Daada Tsohuwa ce mai son kanta Mara adalc..!bata gama kai karshen mganarta ba wasu Tagwayen Maruka Dama da Hauni suka Ziyarci kuncinta Saboda Zafin marin Da Sai ta Kife saman gado Cikin Zafin zuciya jikinsa na Rawa yake Nuna ta da yatsa yana Fadin"Kadan kika gani in har bakin ki bazai yi linzami ba..Na Rantse har ga Kika Kara fadin Tak kan Daada sai nayi miki Abunda baki Taba Tsammani ba..! Yafada Jijiyon kansa suna tashi Saboda Bacin rai Mami Asma"u da mamaki ya Sandarvda ita Gefe Daya ga Zafin marin Daya gigita Daga zaunen Hannanunta saman kuncinta Cikin Zubar Hawaye tace"Ni ka Da ga Hannu ka mara yau Kabiru..!? Kai ya gyada Mata yana Fadin"Wannan ma kadan nayi miki In baki iya bakin ki ba Sakarya kawai wacce bata san inda ke mata ciwo ba..! Mami da kukan Bakinciki ya Ciyota ta Mike Cikin Hargowa da kuka taci Kwalan Baffa Kabiru Tana Fadin"Wlh baka isa ba Tunda ka mareni baka mari banza ba..Kan gaskiyata..? Ance Daada ta cika sonka Tsohuwar banZa ce i...! Bazai iya jin Duka kalamanta ba Saboda in ya gama ji Bacin rai zai sa yayi mata Dukan Mutuwa Watsar da ita yayi a kasa cikin Fushi da Tsananin kamar ya bita ya Tattakata yake ji bai Taba Nadamar auran Wayewa da Boko ba sai yau Cikin Fitar kwallar Cin Zarafin Dayajama Daada Uwa garesa yace"Kije na SAKE KI Saki Daya Asma"u..Kibar min gida yanzu nan..kuma mganar Complain kada ki Fasa shigar da kara ni kuma Ina nan ina Jiranki Yar iskar mata kawai mara lissafi..! Bai Tsaya Jiran Kwakwzonta ba ya Fice Daga Dakin Saboda bacin rai har Bangaje Umaima yayi bai sani ba wacce Rigiman iyayan nata ya Tada ita kuma taci kalmae Sakin da Dad ya Fadama Mami ai sai ta kasa Gaba ballatana baya,Balle taga yadda ya Fito ta Fusace sai Hawaye da kuka kafin ta Kwashu gudu zuwa Dakin Mamin nan ta ganta inda ya yasar da ita kamar irin ta shiga Shock haka Domin tayi kuri ne Hawaye suna Zubomata Shar kamar an Bude Famfo. Gani take kamar waasa wai ita Kabiru ya ce ya saketa?Duk Abunda take yi Tana Takama da Son da yake mata baata Taba Tunanin Akwai Watarana da Kabiru zai Furta mata Kalmar Saki ba ba Burga kawai take yi Tana Tunanin bazai iya ba,Tana ganin Soyayyar Dayake mata bazai barsa ya iya Sakinta ba yanzu Daya Furtamata Sai Duniya ta Fara juyawa da ita. Umaima ta Rungumeta Tana kuka Tana Fadin"Mami What all dis..?Dad fa naji yana Fadin ya Sake ki plz ki Fadamin wasa ne ba gaskiya bane.! Mami Asma"u ta Zura mata ido Tana Fadin"Kema kin ji ko Umai..?Daddy ku yace wai ya Sakeni..Da gaske ya Sakeni ne..? Umaima na Kuka tace"Mami Haka yace kema kin ji nima naji da kunnena yace ya Sakeki ki bar mai gidansa Why Mami..?meyasa kika azagi Daada.?kamar uwata take fa kema a wajenki Kada ki manta Ita ta Haifi Dad bazai Taba Jure cin Zarafinta Daga Bakin kowa ba Koda Kece kuwa! Sai alokacin Mami Asma"u ta tabbatar da kanta komai fa daya Faru gaskiya ne Kabiru ya saketa kuma yace ta barmai Gidansa ai sai ta Rukumkume Umaima ta fashe da kuka Innalillahi me ta aikata..? Saki Gotai gotai da ita da manya Ya"ya ta koma gida Zawarci bata Taba Dauka Haka abun yake ba Lokaci Daya Nadama ta Isketa,Mikewa Tayi Da Karfi kamar Wata Zararriya ta Rarumi Wayarta ta Doka ma Hajiyarsu Waya Umaima
Chapter 144 · 0% Book details