← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 190

Sashe 40

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Safiya kuwa suna Cikin Hira da Abba Barci ya kwasheshi sai ta Kyaleshi ya Huta Daman barcin yana da kyau Sai ta Fada Kitchen taga Abunda Zata Dafa ta iske Nikakken kayan Miya a Cikin Fridge sai ta Dauko tace bari Tayi White rice da Miyar Kaza Tunda Taga akwai kazan Har da Ganyen Kabeji,nan da nan ta kunna Gas Din Duka Guda Biyu ta Dauko Tukunyar ta Fara aiki Cikin Natsuwa da Kwarewa aranta Tana Sakama Mommy Albarka Data Koyamata Aikim mata da yau Da aure ya kawota Wannan Ahalin da suke Bukatar Taimakonta bata san yadda Zatayi ba.
Tana Cikin Aikin ne Taji Abba na kiranta da Sauri ta Dauraye Hannayenta ta Fito Tana amsawa Abba ya Kalleta Lokacin Daya mike Zaune yana Fadin"Barci ne ashe ya Kwasheni.?
Safiya tace"Eh Abba..Nace ai gwara ka Huta Saboda mgungunka ne Akwai na Barci..!
Abba ya kalleta kafin yace"Badai wani aikin kike ba Daugther...?
Safiya ta Dukar Dakai tana Fadin"Ba wani aiki bane Abba abiincin da Za"aci nake Dafawa Munari taje makaranta In ta Dawo ta gaji kuma Ai Zaka ta zama da yunwa ne kai da kake Shan mgunguna..!
Abba ya Girgiza kai yana Fadin"A"a gaskiya Dana sani bazan bari kiyi wani aiki ba..Jiya fa aka kawoki gida nan..Sam bai kamata ba Da baki Damu Dani ba ko Tea sai ki bani nasha..Nasan yusuf bazai shigo hakanan ba..!
Mirmishi kawai tayi tace"Bakomai Abba..Miye amfanina na..? Indai ka Daukeni Tamkar Munari to ka samun Albaeka kawai..!
Cikin kada kai yace"Shikenan Daugther Allah yayi miki Albarka Allah ya jikanki Kamar yadda kike jin kaina..!
Cike da Farinciiki ta amsa da Ameen Kafin tace"Bari na koma na karisa Abba..!
Ya amsa mata da To shikenan afito Lafiya,Cikin Sauri ta koma ta Cigaba da aikinta Cikin Kwarewa.
Cikin Lokaci ta kamallah Daidai Lokacin Dataji ana ta kiran Sallar Azahar Aranta ta kudiri Niyyar Dawo da Farincikin wannan Ahalin,Ta Lura Daga Yusuf din Har Imran din ba wanda ke Zuwa Masallaci Bin Jam"i,Da sun Shigo Shikenan Ballatana su Rika Tafiya da Abba Gaskiya Hakan bai kamata ba,Suna Musulmai Ya zama Wajibi su Rika Sallar Cikin Jam"i Zata Gayama Yusuf Gasikiya su gyara Sallarsu.
Sai da ta kamallah komai ta Juye komai a Flask,ta yanka Ganyen sai dai Bata Hada ba ta bari sai Zuwa anjuma,bata bar Kitchen din ba sai da Ta Goge komai sai Ta Fito Taga Abba Baya Falo Kila ya Shiga Ciki yayi alwala ne itama sai ta Shiga Daki ta Fada Tiolet Tayi wanka Saboda Girkin Datayi Tazo ta Sauya kaya Dole zata gayama Mommy A hada mata kayanta Waje Daya in sukaje ita da Yusuf Zata Taho da Abunta wata Doguwar Riga ta Samu ta saka Kirar Armani ta Saka Mayafinta Ta Tada Sallah Tana Cikin Sallar ne taji Abba na Knooking Din Kofa Lokaci Daya yana Kiran sunan Imran Tanaji yazo ya Bude Abba na Mgana bataji me yake Fade ba sai taji Abba na Buga mata Kofa Lokacin ta Sallame sai tazo ta Bude Abba ta Gani Harda Hulansa da Casbaha yayi mata Mirmishi yana Fadin"Daugther na taso Imran nace ya Rakani Massalaci Shima mu Fara Salla Cikin Jam"i Kamar yadda kikace..!
Safiya ta Fadada Mirmishinta kafin Tace"Ka kyauta Abba..Adawo Lafiya..!
Tafada Tana Hangen Imran Din Daya Sanya Wata riga sai dai ya Sauya Wando Dogo ya Sanyo karo na Farko da Abba zai Fita da Kafarsa Tun Bayan Dawowaarsu kano gwarama Imran yana Tsayawa masallacin kusa da Gidansu Sagir yayi Sallah in dai yana Waje in ya Shigo kuma Shikenan Ammh yau da Abba ya Bukaci Haka sai yaji Shima Zakwadin Abun Acikin Ransa ya kuma Kuduri Niyyar Daga yau Dagashi Har Abba da Yusuf indai suna Gida Masallacin Kusa da Gidan su Sagir zasu Rika zuwa Sallah acikon Ransa yana Kara Taya Yusuf Murna Na Samun mace irin Safiya aransa yana Ayyana Bata Dauko halin Tsohon najadun uban ta ba.
Har suka Fice Bakin Safiya yaki rufuwa Waya ta Dauka zata Kira Yusuf Saima taga Kiransa Da yawa ya Kirata Kila Tana Kitchen ne,Nan da nan tabi bayan kiran sai dai bai Daga ba sai ta kyakeshi sai Zuwa Chan ya Kirata ta Daga Cikin Farinciki yana ma Tambayanta ina ta Shigene ita kuma Saboda Murna tana Fadamai Abba yau ya Fita masallaci Shi da Imran Yusuf Yana Office dinsa kenan Shima Dawowarsa Daga masallacin Ma"aikatansu kenan yakai goshinsa kasa yana Jeromaa Allah Godiya Farinciki Sai da yayi kwallah yama kasa Mgana Cikin Muryan Sanyi da Farinciki yake Fadin"Tanque...Tanque so Much Babe na..Allah yayi miki albarka Shigowarki Gidanmu Haske ne..Daga yau kin tashi Daga Babe na kin Koma Noor!
Cikin jin Dadi tace"Nagode My Dear..In zaka Dawo ka Taho da Jaridun da Littafan da mukayi mgana..!
Yace"Insha Allahu..Mai zan Taho Miki Dashi..?
Da Sauri tace"Bana Bukatar komai Illah Son ganin ka Dawo Cikin Koshin Lafiya..!
Cikin Annuri yace"Shikenan Sai na Dawo Take Care Of Ur Self..Zan Taho muku da Abinci..!
Da Sauri Safiya tace"Daga jiya kagama Siyan Abinci My Dear.
bai samu ce mata komai ba Farinciki ya Cika ransa Daganan sukayi Sallama.
Banganran Abba kuwa kamar Sabon Mutum haka ya koma yau ya Fita Waje yaga anguwan Dayake Rayuwa,,Iro megadi yasha mamaki ganin Imran da wani mai kama dashi da Yusuf Baki ya sake kawai Domin bai Taba Zaton akwai wani agidan ba Sai dai ko ba"a Fadamai ba zai iya Cewa Mahaifinsu Imran ne Daman suna da Uba..? Shifa ya Dauka Daga su Sai su acikin Gidan,Dayake Yusuf ne ya daukosa Gadi,Shima din Security din Ma"aikatansu ya ma mgana Shine ya Samo mai Iro,ba Saboda komai ba sai Saboda Abba suna Fita su barsa Shi kadai ga kuma Gida watarana Ake ji Tunda yanzu Mutune bana Allah.
Abba ya bama Iro Hannu suka Gaisa Cikin Fara"a Ganin kallon da yake ma Abba ne yasa Abba yamai Bayani da kansa Mamaki ya Cika Iro Cikin mamakin yace"Ammh Ranka ya Dade Alhaji ban taba ganin ka Fito ba Tunda Nake agidan nan..?
Abba ya Murmusa kafin yace"Eh ai Tun Dawormu bani Da Lafiya Likita ke Zuwa Gida yana Dubani..!
Iro yace"Kwarai kuwa anyi Haka..Likita kuwa na zuwa Lokaci Bayan Lokaci Ai bansani bane Sannu Alhaji Allah ya kara Lafiya..!
Abba ya amsa da Ameen Imran kuwa Gaba yaci yana Fadin"Abba an fa Tada Sallah..! Abba yabi bayansa yana Fadin"Mu zamu Tafi Masallaci..!
Iro yabi su da adawo Lafiya har suka Fice yana mamaki da Karin Al"ajabi A fili ya Furta"To wannan wani irin Cuta ce ashe Mutum Fin Shekarq bai Taba Fita ba..? Kuma naga Kafarsa Lafiya lau Oh..Ni iro..!
Haka yayi ta Fadi mamaki dai yaki Barinsa.
Chapter 40 · 0% Book details