← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 190

Sashe 41

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka achan masallaci ma Bayan an Idar da Sallah Sagir yaga Abba da Imran Daga Baya Dayake da suka Zo an Tada salla har anyi Raka"a Daya sai suka Tsaya Baya Tunda gaban ya Cika Bayan an idar suka Rama Sallar Farkon Abba na Zaume Bakinsa yaki Rufuwa sai da ya Share kwallah Mutane kuwa basu Damu ba Duk da basu Taba ganinsa ba suna Tunanin baki ne a anguwan Tunda ai Gari da Yawa Sagir ne har Zai Fice yaga Imran sai Chan yaga Abba Cikin mamaki yazo ya gaida Abba ya amsa mai Cikin Sakin Fuska Yana Fadin"Sagir ko..?
Sagir ya gyada kai Abba yace"Mu je Wajen masallaci..!
Mikewa sukayi suka Fice Abba kuma ya Tsaya gaisawa da wasu Daga Cikim Masallacin Sukuma suka Fita Waje Sagir ya kallesa yana Fadin"Abba ya samu Lafiya har ya Fara Zuwa masallaci..Na tayaku Murna Abokina..!
Imran ya jinjina kai batare Da yayi mgana ba sai ga Abba ya Fito suka kara gaisawa da Sagir,yana Tambayan Mama yace ya gaisheta,Tare suka Jero har Zuwa Bakin gidansu Sagir din ganin ya Tsayane yasa Abba ya Tambayeshi nan ne gidansu yace Sagir din ya nuna mai Shagosa Abba ya saka albarka Daganan sukayi Sallama ya koma Shagonsa Cikin Mamaki acikin Ransa yaji Dadi Sosai.
Safiya na Jera Flaks,kan Dinnig Su Abba suka Shigo da Fara"anta Tayi musu Maraba Imran dai Bai ko kalleta ba ya nufi Hanyar Dakinsa sai yaji Tace"Arm nace ba..!
Ya juyo yana kallonta Tacigaba da Fadin"Nace ga abincin fa..!
Imran ya kalleta kafin yace"ke kikayi Girki da kanki..?
Mirmishi Tayi batace komai ba Abba Dake Zaune yace"Ni kaina sai da na Hanata ta Dage sai tayi..!
Imran bai ce komai ba bayaso yayi mata gaddama Saboda karamcinta sai ya Kada kai yace"Later Zan ci..!
Kai ta kada mai Shikuma ya Shige Dakinsa Shirya komai tayi kan Dinning din Harsu Filet sai da ta Jera Ta je gaban Abba ta Durkusa Tace mai ga Abinci chan Abba ya rasa bakin mgana sai saka mata albarka yake karon Farko Daya Taba Zaman Dinning,ba kan gadonsa yaci Abinci ba Ita Safiya ita ta Yi Serving Dinsa ta Hadamai Cowslow daidai wanda Zai ci,Ta Daukomai Ruwa da Lemo Zata Tafi yace ta Zauna itama ta Zuba taci Duk da tanajin kunya ta kasa ma Abba Gardama Dole ta Zauna itama taci Sosai Abba yaci Abincin Sosai acikin Ransa yana sakama Safiya albarka.
Ranar Wuni yayi afalo Salla kadai ke Tadashi Safiya na Tare dashi suna Hira Kamar sun saba.
Yana bata Labarin Kazar kazar dinta kamar Asma"u Safiya Taji Rauni ya kamata ganin Abba na kuka ita Tayi ta Lallashinsa Tana kara Numamai Mutuwa ta Allah ce addu"a kadai suke Bukata,Abba ya Share Hawaye yace"Hakane Daugther Allah yayi miki albarka..!
Daga yau Addu"a ne Tsakanina da Matata da ya"yana Allah ya jikansu..!
Safiya ta amsa da Ameen.
Sai yamma Munari ta Dawo itama ganin Abba haka yasata Farinciki taRumgumesa Tana Murna ya gayamata yau Har Fita yayi Yaje masallaci,Kuma Duk Sanadin Safiya Munari ta Rumgume Safiya Tana Fadin"Thank u Bhabi..!
Munari bakinta yaki rufuwa ganin Dinnig Da kololi Shake da Girki ta Buga Tsalle Saboda Murna Abba nata Dariya sai kuma tarufe baki Sanin Halin ya Imu kada ya jita kuma ya jitan bai dai Fito ba Tsaki yaja acikin Ransa yace"nonsesss..!
Sai da taci ta Koshi Tana Santi
Daganan Munari ta jata Dakinta,Suka Zauna suna ta Fira tana ta Bata Labarin Makaranta Sai da aka kira mangariba ta barta ta koma Dakinta ta Sake wanka,Ta fito Tana Sallah Yusuf ya Shigo Gidan
Ya Tarar da Abba da Imran suna Masallaci.
Bai gama mamaki ba sai da yaga Aikin da Safiya Tasha Da Labarin da Abba ya bashi na Safiya yadda suka Wuni Hira yau ya ma kasa mgana Saboda Farinciki.
Yau agidan Rana ta Farko da suka Hadu Saman Dinning suka ci Abinci Munari da Safiya sun kara Shiga Kitchen sun yi Ferfesun kayan Ciki Imran Shima ya Fito Ferfesun Yaci kadan Yasha Ruwa ya koma Daki Abba Dai yaci Sosai,Da Yusuf da Munari bayan sun gama Suka koma Falo suka Dasa Hira Yusuf ya Dauko Jaridun Daya Siyoma Abba masu yawa Tundaga na Watan Daya gabata sai Littafan addini su azkar,Muwada Malik,Buhari da Musulim
Da Qur"ani izifi Siitin Karami na Karatu Abba ya Karba yana ta Godiya Safiya tace Saura Medicated glass Wanda Abba zai Rika sakawa in zai yi karatu Saboda karamai karfin gani.
Yusuf yayi na"am da Mganar Hatta Abban ma Saboda Zama Waje Daya Raunin Idanuwansa sun Ragu.
Da Sallar Isha"i Abba da Yusuf da Imran Tare suka Fita Masllaci Sagir Sai da ya bama Mama Labari Bakinsa yaki Rufuwa ita kanta Mama tayi Farinciki,Inteesar na gefe Tana Latsa Wayarta bata Saka musu baki ba Tunda ba da ita suke mgana ba.
Yusuf kuwa sun kwana Farantama juna Rai shida Safiya sun Riga sun zama Daya ya gama Gudartama Ransa Cikin Satin nan da anyi musu Albashi Zai Kwashe ya Dauketa suje ta Zabi Furture,da Zasu zuba ashashen da Zasu Zauna,Sai kayan sawanta Bayaso Wani nata yazo ya ganta tana Zaune a Dakinsa Hakan bazai mai Dadi ba Wlh Iyayenta sun gama mai komai da suka Kawo mai Haske acikin Gidansu.

*Kalma Daya akan Safiya..?kalma Daya akan Oga Ranka ya Dade Imu🤣Kalma Daya ga Inteesar Inteen Daddy da Ya Basheer Maryama Takwaran Daadan Alkali Dukku..!*

*Shakira....*
3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

        *🅿�16*

*Bayan Sati Daya*

Bayan kwana Bakwai da Auran Yusuf Da Safiya Abubuwa sun Fara Daidaita Gidansu Yusuf yanzu ya Fara Dawowa Daidai Tare da Mutanen Cikinta,kuma Duk a Dalilin Safiya Tuni ta Saka Yusuf ya kira mai gyara ya Saita Tv,Sai dai kaga Abba Zaune afalo yana Karatun Jarida Sanye da Gilashin sa mai karamai karfin gani ko kuma yana Karatun Littafin addini Safiya Dake kai kai da kawo Tsakanin Falon da Kitchen suna Taba Hira Sama Sama.
Ya kasance Duk Safiya Tare suke Breakfast,kuma Duk Dare suna Dinner Tare sai dai Imran ne bai Cika Zama Cikinsu ba,Ba wanda kuma ya Damu Sanin Halinsa Tun suna Lagos Shi yafi jin Dadin gudanar da komai na Rayuwarshi shi kadai batare da kowa ba.Mutane suna da matukar Muhimmanci a Wajensa,Bai yason Ka takuramai Shima yana Girmama Rashin Takura ga wasu koda su din Ahalinsa ne sai dai Kowa ya gansa yasan yana Cikin Farinciki Gidansu ya Dawo Gida irin na Kowa Bayan sunyi bankwana da Farinciki Da Dadewa.
Asatin Har Masallacin jumma"a Abba yaje Tare da Yusuf da Imran Cikin Farinciki kuma da Likita yazo Dubasa Yaji matukar Dadin ganinsa yace in Har Abba zai Cigaba da Tafiya haka Hakika Mgani bazai kara mai amfani ba Zai iya Dawowa Daidai  insha Allahu,Farincikin Haka yasa Yusuf yayi Shawara da Abba da Imran kan yana so ya gyara Shashen Dake Koridon Dakin Munari Safiya ta Tare acikinsa tunda wanda suke Zaune yanzu Ciki Dayane,sai kuma yana son Siyamata kayan sawa,Abba yaji Dadin Haka Saboda Safiya ta Chanchanci komai na Rayuwa Shi ya bashi Umarnin Ya taba Kudin Dake bankin Nura marigayi,Tunda akwai kudi Har yanzu yayi amfani Dashi Imran ma ya yarda da Shawaran.
Ranar Sati da auransu da Daddare suka Tafi Gidansu Safiya Shi da ita sai Tace Tare da Munari Zasu je Wanda Cikin Satin Daya sunyi matukar Shakuwa kamar yaya da kanwa In Munari bata je makaranta ba Suna Tare da Safiya aiki Tare suke yi Girki ma Haka wajenta tana ta kara koyin Abubuwa sosai Tunda ita Munari Da Karfi Da yaji ne ta iya girki,Lokacin Tana Karama Ba komai ta iya ba Sai dai ya Zaman mata Dole ne Tunda itace Macen Cikin yayyin nata da Taimakon Waya Online Clasess,Sai kuma Goggle yasa take kwaba Wasu abubuwan ammh Zuwan Safiya ya Kore mata komai,yasa ta gane ashe abaya Duk Shirme take yi.
Koda suka je Alhaji Alhassan Baya nan Ya Tafi Fagge,Mommy Tayi Farincikin Ganin yarta Cikin Kwanciyar Hankali Tayi Fresh na Amarci,Tasleem Ta Rumgumeta Tana ta Murna ganinta,Mommy bata Taba ganin Yusuf ba sai Ranar ta yaba Sosai da Zabin Diyar tata Domin a Fuska yana da Kamala da Cikar Zati Tayi musu Nasiha Sosai,Tasleem Taja Munari Dakinta suna Hira Mommy Taja Yarta Ciki Suka bar Yusuf da Labarai da ake Nunawa a Nta,gabansa Cike da kayan makulashe da yar aikin Mommy ta Cika Gabansa Dashi Ruwa Kadai ya iya sha.
Mommy take Fadama Safiya abunda yakai Abbun su Fagge kararsa ta kai Wajen Goggo,Bayan taje Gidansu ta Fadama Iyayenta Halin da ake Ciki Mahaifanta basu saka baki ba Sai dai sun Tausheta Datayi Hakuri Tunda aikin Gama ya Riya gamu,Yayartace ma Da ta ke binta Anty Saratu Dataji Ta Dinga Fada Dayake Tana da Fada sai Iyayensu suka Taka mata Burki Itace ta bata Shawaran su je Chan Fagge sun Fadama Goggo ko Yaya ne ai Mahaifiyarsace Zataji Rashin Jin Dadin Rashin Darajata da Yan'uwansa da Alhassan bai yi ba Shine sukaje ita da Anty Saratu suka Fadama Goggon komai sai da Tayi kuka Dataji Abunda ya aikata Shine ta Kirasa yaje yau Tun Dazu Kila Chan zai kwana Tunda Har Dare yayi bai Dawo ba,Daman Tun Bayan Faruwar abun Mommy ta Daukemai basu Dawo Daidai ba.
Safiya bataji Dadin Rashin Jituwan Dake Tsakanin iyayenta ba Har yanzu yasa ta Sanyaya rai ta Dafa Kafadan Hajiya Mero Tana Fadin"Mommy Sam bana jin Dadin Rashin Jituwan Dake Tsakaninki da Abbu..Don Allah ki manta Komai indai Saboda ni ne Wlh Tallahi bana Cikin ko Wata Mtsala Mijina yana sona Abba kamar Diyarsa Munari ya Daukeni Bana Cikin Wata Damuwa baki ga alama ba..!
Hajiya Mero ta kalleta ta Kada kai Tana Fadin"Ammh ai Da Farko shi da Kansa yace yayi Bincike basu da Kowa anan..Basa da wasu Dangi Anya Safiya Kina ganin hakan ba wata Mtsala bace...?kuma fa yacemin Mahaifin su Mahaukaci ne akacemai..,?
Chapter 41 · 0% Book details