Sashe 102
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gyada yana Fadin"Duk yadda kikayi daidai ne ni da Imran masu Bin Umarnin ki ne..! Mami Asma"u ta Mike Cikin Hargagi tace"To wlh in shi ya amince..Ni ban Amince ba..In dai ina Numfashi bamai Aura ma Ya"ta Dan iska Dan Shaye wanda baida Sana"ar fari ballatana na baki sai shaye shaye..! Tafada da karfi Tana Zaro idanuwanta Waje. Imran daya gama jin iya Abunda zai ji yakai wani limit din da Bazai iya Jurewa ba ya Mike da Sauri jikinsa na Rawa Cikin Dakakkiyar Muryansa mai Cike Amo da Zati yace"Kada ki kara Kirana Dan"iska..Ko Da'n Shaye..Shaye..Don"t Try it again..Don"t Ever Try it...! Ya karishe Fada Jijiyoyin kansa sun Mike Radau har ana ganinsu Naman Kirjinsa na sama da kasa Lokaci Daya yan Sakin Huci mai Zafi tare da Zafin Zuciya kamar yayi Bindiga haka yake jin kansa,Hannunsa Manuniya ya Daga yana nuna Mami Asma"u dashi Cikin Alamun gargadi. Gabadaya kowa sai ya koma kallon Imran cikin Mamaki,Umma aranta tace ai gwara yayi mganinta Haka ma Inna maimunatu taji acikin Ranta. Mami Asma"u da Ta tsaya tana kallonsa Cikin dan shakarsa Tace"In na kara fa? Me zaka iya Mara kunya Fitsararre..? Tafada Cikin Ingili tana Jifansa da Harara,Imran dayaji ya Fara rasa Duka Controling dinsa ya Fara Takawa zuwa gaban Mami Asma"u Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Sai na nuna miki Halin Dan Shaye shaye..Na kuma gwada miki Halin Yan iskan da kike Fada..! Yafada yana kallonta Ido Cikin ido babu Wani tsoro ko Shakkarta. Taji Tsoro saboda ganin yanayinsa sai dai kasawa ba nata bane Cikin Dari dari tace"An ce maka Dan shaye shaye..? Karya akayi ba Dan Shaye Shayen bane..? Tafada Cikin Nuna iya gaskiyarta ai batama gama Sauke Numfashi ba taji Hucin Imran gabda Fuskarta kamar Walkiya ya kariso gabanta Idanuwansa Sun Rufe baima gani Dakyau Zuciyarsa ta gama Rufewa da wani Duhu har yana Hango kansa yayi Ball da Mami Asma"u da sai ta Gamu da Bango kanta ya shafe ya Tabbata bazata taba manta dashi ba. Sai dai ya Daga hannunsa da Niyar Tureta Abba ya Mike da Sauri Cikin Abunda bai fi kiftawan ido ba ya Dakamai Tsawa"Imran...kada ka Fara..! Yafada cikin Tsawa da Hargagi wanda ya Firgita kowa,Mami Asma"u tayi bayan Baffa Kabiru da suka Mimmikewa Cikin mamakin Imran,Imran kuwa Cak ya Tsaya yana Sakin Huci mai Zafi idanuwansa sun Juye kamar yana cikin maye,Inteesar da Munari suka kamkame juna suka Fashe da kuka Su Sadam kuwa suma Mimmikewa sukayi cikin mamaki. Abba cikin Sauri yace"Yusuf da Sagir ku Rukemin shi..! Yafada a Taushashe Daada Dake Zaune bata Motsa ba Illah dan Mirmishi Data saki In Asma"u ta tabata Kabiru yayi shuru ta tabbata In tayi ma Imran bazai kyaleta ba yaron Zamani ne mai ji da kuruciya Shine Daidai da ita. Da sauri Yusuf da Sagir suka Karisa suka Rikesa daman suna Ta tsoron kada ya balle musu,Kokarin Fizge kansa yake yi suka mai Riko sosai Yusuf ya Kallesa yana Fadin"Imu..Imran kalleni..!natsu Nace maka..! Yafada Cikin Daga Murya,kallon Yusuf din yayi yana Budemai idanuwansa Cikin Muryansa mai cike da amo yace"Na natsu fa kace..?Kake fadamin na Natsu..? To bazan natsun ba..ka sakeni nayi mganin matar nan..Nace bana son ana batamin rai Bana so...BANA SO..! Tunda nazo na shiga Harkan wani..? Ina kebe kaina ne saboda ina Girmama yanayina..Bana so na bata ma wani rai nima bana son wani ya batamin Tayi ta mganganu akaina Cikin son ranta..Waya Dakatar da ita..?ko wayace mata ta bari bai kamata ba? Sai ni domin nagaji nayi mgana..? Wlh billahill Azim bata san Waye Imran ba yau bazan ji mganar kowa ba indai matar nan ta kara Bude baki ta Fadi wata mganar banza akaina sai na Nuna mata Kalata sai na Nuna mata ita din ba kowan kowa bace a Wajena..! Ya karishe Fada Cikin Tabbatar da mganarsa Khamis ne ya Isa gaban Inran Cikin Fushi daman Tun dazu yana Tsaye so yake yaga Karshen Rashin kunyar Imran din in zai iya Dukan Maminsu..? Lalle da yau yagane Shayi Ruwa ne..! Kikam ya Tsaya gaban Imran yana Fadin"Yanzu kai in aka barka sai ka Daketa..?kasan wacece ita agareni.?mahaifiya kasan kuwa mtsayin uwa a wajen D'anta..!?da zai iya zama ya Jure Cin Zarafinta Daga wani bangara..? Yafada Lokaci Daya yana Dukan Kirjin Imran wanda ya tsaya Kikam Shima yana kallon Khamis Cikin wani Kallo na Takaichi Karamin Tsaki yaja kafin ya kwace hannunsa a wajensu Yusuf ya Saka Hannunsa ya bambare Hannun Khamis akan kirjinsa yayi irin Wurgi da Hannunsa da Zafi sai da Yayi baya kamar zai fadi kana ya Tsaya da Kafafunsa. Cikin Nuna sa da yatsa Imran yace"Kai yaro kauce badai kai zan yi ba..Ita din wacece..?ni ba kowa bace a wajena..Ko Baffa Kabiru dake mtsayin Yayan Mahafina bai isa ya tsaya yana gayamin mganar da wanchan matan take Fadamin ba ballatama ita ba kowan kowa ba..In kai kasan Darajan Mahaifiyarka ni kuma da bani da uwa ai nasan Darajan kaina...Kauce kabani Wuri kafin ranka ya baci..! Ya Karishe fada Lokaci daya ya bangaje Khamis dake tsaye sai da yayi gefe kamar Zai Fadi Sagir ya Rikosa gaban Sajida dake makale jikin Umaimah ya Karisa Cikin kallon Kaskanci Tare da kare mata kallo Daga sama Har kasa kafin ya Nunata da Yatsa yana Fadin"Wannan abar ne kike Rigima akanta..? Ai ni ban ga mace anan wajen ba..Na Rantse ga Allah ni Imran Abubakar Malami Wannan yar taki a cikin yanmatan da zan iya maneji dasu bata aciki ko acikin Tsakiyan Shinkafa ta shiga zan saka Hannu na Tsinceta na Wurgar..Nafi Karfin yarki da Duk Abunda ta mallaka..! Yafada yana karkato da kansa Wajen Daada kana cikkn Kaushin murya yace"Daada ki janye mganarki..Ni ban amince da wannan Hadin naki ba Ko matan Duniya zasu kare Bazan iya Auran Diyar masu som kai da son zuciya ba. infact ma batamin ba..Bana sonta bazan taba sonta ba..! Yafada kai Tsaye Zaro ido Kowa yayi yana kallonsa Mami Asma"'u taji Tsoro yasa ta kasa wani Motsi tana Bayan Baffa Kabiru da shima ya kasa Cewa kala ballatana Fadan datafi karfinka sai ka maidashi wasa. Ballatana Khamis da Mamakin karfin Imran ya kamasa Sagir dake rike dashi ganin yana Kokarin kwacewa yasa ya Girgizamai kai yana Fadin"Kada ka shiga wannan Fadan..Abba ne kadai ya isa ya Dakatar da Imu ammh wlh kai bazaka iya ba..! Zallar gaskiya ya gani acikin Idanuwan Sagir yasa ya kasa Motsi. Sajida kuwa Kukanta ne ya Karu jin Abunda Imran yace ita kuma alokacin ji take Imran yayi mata Dari Bisa Dari. Inna Bintalo ce ta Saka Salati tana Fadib"La"ila Ha'illahu Ni Bintalo yau ina ganin Abun mamaki kai Imran Matar yayan Mahaifinka ka Daga hannu Zaka Daka..? Ashe baka da kunya da Tarbiya bansani ba..? Kai Tsaye Imu ya kalleta Ido Cikin ido kafin yace"Eh..Ai ba uwata bace..?ko Ita din U..!!! Bai kai Karshen mganarsa ba Yaji Abba ya Sauke mai kyakyawan mari Guda Biyu Dama da Hagu da sai da Kansa ya koma gefe yana jin Wani Radadi daga kasan Ransa Idanuwansa ya Runtse ko Dagowa bai yi ba. Abba ya Nunasa da Yatsa Cikin Takaochi da Bacin rai yace"In ka kara cewa Tak anan wajen..Ni ba Mahaifinka bane..! Da sauri ya Bude idanuwansa Jajir ya Sauke kan Abba zai yi mgana Abba ya Dagamai Hannu yana Fadin"Kace Tak zan ci maka Mutumci Imran..Kaji ma na Fadamaka..!.dole Imran yayi shuru Ya koma yana kokuwa da Bacin Ransa ji yake kamar ya Naushi kansa saboda Bakinciki da tozarci. Abba ya sauke Hannunsa Cikin bacin rai yana Fadin"Ni kaina ban isa na take mganar Daada ba ballatana kai..To bari kaji na Fadamaka ba wanda ya isa ya Tada Umarninta Za"a Daura wannan auran agobe da yardan Allah kamar yadda tace sai dai in zaka Rataye kanka ne ko kuma ka sha Fiya Fiya ka Mutu karewar rashin So kenan..! Yafada cikin Tabbatar da mganarsa kafin ya cigaba da Fadin"Kuma na Rantse in ka kara cewa wani abu kan wannan mganar sai naci maka Mutumci..Duka ka bama Asma"u da Yaya Kabiru Hakuri kafin na Saba maka..! Yafada cikin bada Umarni Imran ya Dago ido yana kallon Abba,kai lalle uba ma wani abu ne Da ace yau ba Abba bane waya isa..? Ganin ya tsaya kallonsa ne da Jajayen Idanuwansa yasa ya Dakamai Tsawa Har Jikinsa na rawa yace"Ko bazaka Duka bane ni na Duka da kaina na basu Hakurin Rashin kunyarka..? Yafada yana Nunasa da Yatsa,Yusuf ganin yadda Abba ke rawan jiki yasa ya Isa kusa dashi ya Riko sa yana Fadin"Abba koma ka zauna zai yi Abunda kace..! Yafada yana Rikosa,Yusuf ya kallah kafin yace"Kyaleni kawai Yusuf..! Yafada cikin Tabbatarwa da nuna Bacin Ransa jin haka yasa ya Kyalesa ya Karisa Wajen Imran ya Dafa Kafadansa yana Fadin"Kayi Abunda Abba yace Imu..Plz..! Bai yi gaddama ba ya saka Gwiwiyinsa a kasa Kirjinsa na kuna Cikin Dashashewar Murya yace"Ku...yi hakuri..! Lokaci Daya yana Sadda kai Cikin Takaichi yanajin kansa kamar ma yayi Bindiga saboda Zuciya. Mami Asma"u ganin an bata Hakuri yasa Ta fito daga bayan Baffa Kabiru Tana wanu tabe baki ganin haka Yasa Abba ya juya yana Fadin"Ina kara baku hakuri a madadinsa..Yaya Kabiru dake Asma"u ku yi hakuri ku yafe masa..! Yafada yana Hada Hannuwansa alamun Roko Baffa Kabiru ne ya Jinjina kai Lokaci Daya yana Sauke ajiyar Zuciya Kafin yace"Is ok..! Da haka bai kara cewa komai ba,Mami Asma"u baki ta tabe kafin tace"Uhm..Shikenan..! Abba ya gyada kai yana Fadin"Nagode..! Lokaci daya ya juya wajen Imran yana Fadin"Tashi ka koma Wajen zamanka..Kuma ba cewa nayi ka Fita ba..! Yafada kafin ya kalli Sagir yana Fadin"Sagir kamasa kuje..! Sagir na jin haka ya Rikosa yana Fadin"Tashi Imu..! Bai yi gaddama ba ya Mike ammh Idanuwansa ma basa ganin gabansa Saboda bacin rai nan idanuwansa yakai kan Inteesar dake kuka Sai Yakara Rikicewa Kujeran dake Kusa dasu ya saka Kafa ya Daketa sai da tayi baya ta Wuntsula suka tashi a Firgece su uku ita da Hafsah da Munari suna Makyarkyata da kallo Kowa ya Bisa Abba kai ya Girgiza Shi da Yusuf. Sagir yayi ya zauna yaki a Tsaye ya tsaya ya Harde duka Hannuwansa saman Kirjinsa ya Lamkwashe kafafunsa yana Girgizawa. Daddy ne yace kowa ya koma ya Zauna kana Falon ya natsu bayan kowa ya Zauna Abba zai yi mgana da Daada