Sashe 103
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ta Dakatar dashi da Fadin"Ba sai kace komai ba Malami..Abunda kayi daidai ne ka nuna mana Rauninka baisa ka Daina bama ya"yanka Tarbiya ba,Duk da itama Asma"u bata kyauta ba ta shiga mganar da ba nata ba sai dai Duk inda karami da babba ke Fada to Karamin ne za"a Hukunta ko da shi keda gaskiya naji Dadin Hukuncinka..! Ta karishe fada Cikin Dattako kafin ta Dora da fadin"Dalilina na Hada wannan auran don Dinken wannan Barakan dana Hanga Tuntuni ne..Za"ayi wannan auran gobe insha Aallahu kamar yadda nace..Ke Asma"u Allah yasa kiyi Hankali..Yanzu Imran suruki yake wajenki in baki Daukesa Danki ba..Kai ma Imranu Asma"u Suruka take gareka in baka Dauketa Uwa ba..Ku koyi girmama juna saboda haka..Dare yayi kowa yaje ya kwanta ya"yana kuma zamu kara Tattaunawa acikin Daki..Allah yayi muku albarka Gabadayanku..! Wasu ne suka samu amsa ma Daada da Ameen Mikewa tayi Daddy da Abba da suka mike tsaye suka Taimaka mata zuwa Dakinta,Inna Maimunatu da Inna Bintalo da Baffa Kabiru suka mara musu baya. Imran kuwa shi ya Fara Fita Waje Haraban gidan kansa sarawa yake yana jin kamar ma yayi Bindiga saboda Bacin rai wato sun Dage sai anyi ko..? Lalle zasuv samu karamar bazawara kamar yadda suka Dauramai bada son ransa ba Wlh Tallahi sai ya aikata abunda bazai ma kowa Dadi ba. Yafada Lokaci Daya yana Zaro karan Sigarinsa ya kunnata ya Haye saman Motan Yusuf ya shiga busa Hayaki ta Hanci ta baki itace kadai zata saka yaji Bacin ransa ya Ragu in ba Haka yau ba zaman lafiyaa Achan Falo kuwa kowa ya Watse Munari ta kama Inteesar suka Shige tana Waigen Inda Imran yabi ya Fita Mami kuwa ya"yanta ta Rumgume tana jin wani Radadi acikin Ranta Yayinda Khamis yazo yana bata Hakurin ganin Harda kukanta. Su Anty Safiya Daki suka shige Kowa zuciya ba Dadi Umma ma Dakin ta Shige Domin barci ne a idonta itafa bata ji wani damuwa ba mganin mai Son kansa kenan Su Yusuf kowa wajen kwanciya suka Nema kowa ba Fara"a ammh kai tsaye Sadam yace yaji Dadin abunda Imran yayi ma Mami Asma"u kila ta Daina abunda takeyi. Badai wanda yace komai Yusuf da Sagir Tunaninsu na wajen Imu basu san Halin Dayake ciki ba sai dai Dole su kyalesa sun san ko giyan Wake suka sha Karyansu suje wajensa ahalin Dayake ciki Kadaicinsa Shine mafita da wani yaje ya Damesa sai dai suna Fatan Allah ya Huci zuciyar Mazaje...!