← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 190

Sashe 124

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Daada na chan na Nazarinta ita kadai Imran ma nayin nasa shi fa a Tunaninsa zai yi Taimako ne Tunda Inteesar bata son khamis bazai bari a aura mata shi ba,Kuma bazai yarda Daada ta kawo wani ba Shiyasa yace Zai aureta ba domin ya yarda da mganarsu na cewa ko yana sonta bane baiyi Beleving kan wannan abun ba.
Daada ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Zan yi mgana kan auranka da Inteesar kuma bamai Tada mgana ta..Sai dai kaima ina so kamin wani abu Guda Daya..!
Kallonta yake yi bai yi mgana ba Daada ta gyara ZAma Tana Fadin"Da Farko Dole zaka Dawo Imran din ka Dana sani..Ka daina shan Taba ka koma aiki ka zama Mutum wanda zai iya Rike mace saboda Nauyi ne zai Hau kanka Ina so don Allah ka Dawo Rayuwarka ta baya komai yayi Tsanani Saukin sa na wajen Allah indai zakamin wannan alfarman nayi maka alkawarin Karshen Wata Zan kira kowa da kowa kuma baza"a Watse ba sai da auranka da Inteesar da yardan Allah..!
Kamar Daada tayimai gafara haka yaji Cikin Farimcikinsa Daya kasa Boyuwa yace"Insha Allahu Daada..!
Daada taji Dadi sosai ta Rika sakamai albarka Kiran La"asar ya tadasu ya tafi yayi sallah Daya dawo ya shiga ya kwanta yana Barcin gajiya bai tashi ba sai gabda mangariba Ya tashi yaje yayi salla ya Dawo barcin yammah Cikin kunci ya tashi ga kuma Fushin Inteesar bata Kirasa ba sai shima ya Shareta.
Da Daddare sun sha Hira Daada Shi kanshi yana ta mamakin kansa ko Saboda Rabi Hirar Daada ke yinsa kuma Duka Labarkn Anni ce shiyasa yake jin Dadin Hirar kuma bama Haka ba Zuwansa Dukku yazomai da Sauyi sosai yaji Dadin zuwansa Wajen Kakarsa sai alokacin yake jin Dadin da Sauran mutane ke ji in suka zo wajen kakkaninsu bai taba Samun kusanci da Daada ba sai wannan karon.
Washegari daya tashi da Safe yaga Kiran waya da bakuwar lamba ba adadi,ga Sako yayi mamakin wanda ya Kirasa,sai dai sakon Daya gani ya bashi amsa Sajida ce.
Tsaki yaja yayi Bloking dinta ya Share Sakon nata Domin baya Bukatar Wata mu'amala da ita bashi da akala da ita
Ita kuma Daman Umaima ta saka Ta Tambayan mata Munari ita kuma ta Turo ma Umaiman ta Tura mata,Shine ta Dinga Kiransa bai Dauka ba ta Turamai sako Daga baya ta Dinga Kira bai shiga ba ta Fahimci ya Kulleta ne Tayi kuka sosai kamar Ranta Zai Fita kuma ta Dora Bleeminng din komai kam Mami Tama ganin koma menene ya Faru itace Sila,Shiyasa bayan sun gama Test tayi zamanta a Hostel bata Dawo gida ba saboda Haushin Mami Asma"u take ji.

Sai ga Imran dayaje Dukku da Niyyar kwana Daya ya shantake har kwana Biyu sai dai Ranar Lahadi da Safe Bankin GTB, Reshen Jahar kano suka Turomai sakon suna son ganinsa Karfe 8:00am na safe tayimai a Office din Manaja Ranar Monday abaya bai Damu ba da aikin ba,ammh yanzu ya Damu ko Saboda mganar Daada,Khalil ya kira ya gayamai sun Dade suna mgana yana bashi Shawarwari da Kwarin gwiwa kafin suyi sallama alokacin yayi shirin Tafiya Kano da shirnsa ma ya shiga Dakin Daada yayi mata sallama Tana ta mamakin Tafiya ba Shiri yace mata wani abu ne ya taso.
Kamar kar yatafi haka Daada taji shima haka sai dai ba yarda zatayi haka sukayi sallama karfe 12, yana gombe,Daganan ya Hau Motar kano sun samu Goslow a hanya da kuma Wahalan Mai yasa basu shigo da Wuri ba sai bayan mangariba suka Shigo kano.sai dai su Abba suka gansa kamar Daga sama.

*Naji Sauki Sosai...Nagode da addu"o'inku..Allah ya bar Zumunci Ameen..*

*Shakira*
3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�13*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Chapter 124 · 0% Book details