Sashe 132
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da sai taci Uban Sajida in ta kuskura tayi mata wannan Shirmen. Abinci tace tazo taci bata cikin good Mood yasa tace bazata ci ba wucewarta Tayi Dakin da suka Sauka ita da Mami Asma"u ranta duk ba Dadi Mami Asma"u ta bita da wani kallon yarinyar nan Tana Hauka ne..? Ba a dauki Lokaci ba kowa ya gama cin Abincinsa nan mazan suka Zauna suna Hirarsu Imu ma na cikin su sai dai baya mgana Sai dai yana jinsu kawai in abun mgana ce aka Sako sa sai da ya gyada kai ko ya Rage Daure Fuskar Wayace a hannunsa Mgana suke da Intee Tana mai shagwaban gida ba kowa duk ba Dadi tana Missing dinsa,Sakar mai da kasala Take duk da ba Waya suke ba Massages ne bai biye mata yace ta wuce taje ta Dauki Littafanta Tafara Karatu baya son Shirme. Suna nan Zaune sai ga su Abba sun Fito Dukkansu sun taso Tsohuwa Daada agaba Tana Tafe sanye da Hijabi mai ruwan kasa,Bai da Tsawo sosai Carbi ne a Hannunta tana ja Inna Bintalo da Inna Maimuna suna Kafada kafada da ita sun sakata a Tsakiya. Kan kujera suka Taimaka mata ta Zauna Gabadayansu suka Zauna a kasa Umma Dake saman kujera ta Sauko ta zauna akasa,Daman Mazan duk suna Malale zaune ne saman Cafet din Daya malale Falon. Mami Asma"u dai Bata sauko ba sai ma kara gyara Zama datayi akan kujeran ta kara gyara Zaman Siririn Gilashin Dake idanuwamta Khamis na gefenta a kasa yazauna wajen Kafafunta. Tuni Falom yayi Tsit sai Sautim Muryoyin su Sa"id da suke ma Daada Barka da Fitowa amsawa take cikin kulawa,Tana Bin Kowa da kallo Daya bayan Daya sai ta sauke kallonta kan Mami Asma"u wani abu na cin Ranta Uhm Lokaci yayi da Asma"u zata gane Kuskuranta Juyawa tayi Tana kallon Baffa Kabiru kafin tace"Ina Sajida..?banganta ba ko bada ita kuka zo ba..? Kai ya girgiza mata kafin ma yace Wani abu Mami Asma"u ta yi Caraf tace"Da ita muka zo mana Daada..Yanzu ta shiga ciki..! Daada ta gyada kai kafin tace"Jeki kirata..Domin wannan Haduwar ta Shafeta sosai..! Mirmishin Saman baki Mami Tayi Damam ai tasan mganar Sajidan da wannan Tsagerin yaron nan Lalle kuwa yau Zata nuna ikonta a Mtsayinta na uwa,Sai ta ja Imran a kasan Kafarta bai isa yaja da ita ba. Tana shiga Dakin ta iske Sajida kwance Tana Hawaye jin muryanta a saman kanta ne yasa tayi Saurin Share Hawayenta ta mike Zaune tana kokarin Kauda idonta kada Mamin Ta gano Halin Datake ciki. Kallon Tsab Mami Tayi mata kafin Tace"Wai Sajida kukan Uban me kike yi ne Tun dazu..? Sajida tace"Kuka kuma..? Ni ban yi kuka ba Mami..? Tafada tana kokarin mikewa ta kaucema Kaifaffun Idanuwan Mami Asma'u Daga gano yanayinta. Mami Ta wani kalleta a karkace kafin tace"Kina Zaton ban san kukam me kike yi bane..? Uhm yaro man kaza..Dazu fitan da kikayi wajen Dan iskan yaron nan kikaje..! Sajida ta Dago kanta cikin mamaki ta Bude baki Zatayi mgana Mami Ta Dakatar da ita lokaci Daya Tana Daga mata Hannu tana Fadin"To bari kiji na Fada miki in ma Kina kokarin Saukowa ne ki yarda da auransa Cikin Sauki ni Asma"u uwarki ban yarda ba ko Zan amince da wannan auran ba yanzu ba sai na ja Yaron nan akasan Kafata ya duka yana kuka yana Bani Hakurin Rashin Da"ar da yayi min sannan kuma yana kuka yana Rokon na bashi ke sannan zan iya yarda ma ki Zauna dashi ammh in ba haka ba Duk wacce Za"ayi sai dai ayi bazan bari ki Zauna da wannan Dan iskan yaron ba.!. Tafada cikin son Tabbatar da mganarta bata damu da yanayin Sajidan ba ta Fice Tana Fadin"Ki fito Daada na kiranki..! Sajida Kuka ya kwace mata Mami bata son Imu shine Rayuwarta ba Wani irin so mai Tsanani ne ya kamata alokaci Daya tana jin kamar Zata Mutu in ta rasashi Wata Zuciyar tace to ke sai ki bari ki rasashi..Ina bazata taba bari haka ya Faru ba Imran mijinta ne kuma Dole tayikomai Saboda ta Dauwama Dashi Wannan karon zata Dakatar da Mami Zata Fadamata gaskiya She Love Imran Tana matukar sonshi kuma Zata Zauna dashi a duk yadda yake so ta kyaleta don Allah kada ta Shiga Rayuwarta ta lalata mata Tiolet ta shiga ta wanko Fuskarts tazo ta Tsane da mayafinta kana ta Fito Falom ita ake ta jira ba"a Fara Taron ba Tana Zama gefen Dan"uwanta Daada ta kalli Yusuf Tana Fadin"Yusufa Bude mana Taron da addu"a.." Ba musu ya gyara zama ya Bude Taron da addu"a aka shafa sannan Daada tayi gyaran murya ta Fara mgana..! "Da farko dai ina yi ma Duka ya"yana da jikokina da suka Taru anan wajen barka da zuwa..nasan kun baro duka Tarun ayyukan ku ka amsa kirana Naji Dadin haka Allah ya saka Muku da mafificin Alheri ya raya muku Zuru"a ya baku ya"ya wadanda zasu ji kan ku kamar yadda kuke jin kaina..! Gabadaya aka amsa mata da Ameen Ameen. Kafin ta dan yi shiru kafin ta Cigaba Cikin muryan tsufa"Dalilin Dayasa nace ina son ganinku duka da wasu Daga cikin yayenku Mgana ce Daya zuwa Biyu..na farko mgana ne kan Imranu gashi chan Dan Wajen Malami sai Sajida Yar wajen Kabiru..Kafin naje gaba a mganata kowa anan wajen ya Shaida Auran dana saka aka daura shi Wata Daya Daya gabata a garin nan tsakanin Imranu da ita Sajidan ko..? Kowa ya gyada kai alamun hakane Daada tana Jan Casbahanta tacigaba da Fadin"Alhamdulillah kuma kowa anan yasan abubuwan da suka yi ta Faruwa bayan an Daura auran da kafin a Daura Inda Asma"u gatanan matar Kabiru ta rika nuna rashin Amincewarta tare da Diban albarka kala kala ammh duk na kauda kai bam ce komai ba Saboda bai kamata nayi mgana alokacin ba Kuma ni miye nawa..?ko me zan ce tunda agaban Mijinta ne Gashi nan kabiru bai Tsawarta mata ba kenan shima ya yarda da duka abunda ta Zauna akai bai so hadin Zumunci Tsakanin jininsa da jinin Abubakar ba..! Tafada Tana dan Sauke Numfashi Kowa afalon yayi shiru yana Sauraranta Baffa Kabiru ya dago kansa ya kare kansa Daada ta wurgamai wani kallon Da Dole yayi Shuru da bakinsa Mami Asma"u kuwa na gefe Kafa Daya kan Daya tana karkadawa alamun tana jiran kowa wanda yace kule sai tacemai Chass..! Daada ta cigaba da Fadin"a lokacin da nayi Tunanin wannan Hadin har ga Allah Zuciyata Daya ina ganin cewa hakan shi Zai kara mana Dangom Zumunci da son junanmu sai Daga baya na gane nayi kuskure kuma nayo Hadi inda bai kamata ba na manta Asma"u ita ke jan Ragamar Rayuwar gidan Kabiru tamkar itace mijin shine Matar baya iya Zartar da mgana sai abunda tace,Sannan ko mganace ta Dangi bazai iya mgana ba sai da yawunta ko da amincewarta Shiyasa data nuna bata amince ba shima ya Goyi bayanta..To Alhamdulillah na Taraku ne anan saboda na gyara Kuskurena..Mustapha ina son ka bama Danka Imranu auran Diyarka Maryama mai sunana ba sai gobe ba yau din nake son adaura wannan auran indai kaima ka amince saboda ina Tsoron nuna isata akan ku Alhalin ban isa ba! Gabadaya Falon sai kallo ya koma Wajen Daada ita kuma ko ajikinta Sagir ya kalli Imran alamun How comes,shi kuma ya Dagamai gira Khamis da yayi mutuwar Zaune ya Dago yana kallon Daada lokaci Daya ya koma yana kallon Imran wanda ya Cije mai baki ya Dagamai girarsa Duka Biyu irin kaga nawa ikon..?to yaya Zata zama takan ne..? Gabadaya kowa sai mamakin Daada yake yi,Yusuf ya kalli Imran ganin ko ajikinsa ya juya yana kallon Abba da Daddy da suma suke kallon Daada aransu suna Tunanin Riikicin Tsufa ya Fara Taba Daada. Daddy ne ya bude baki zai yi mgana Abba ya girgizamai kai,Baffa Kabiru kuwa bai ce komai ba Domin ya kasa Dora komai akan Mizani.. Sajida kuwa allah ne kadai yasan Halin da Zuciyarta take ciki gani take kamar ta Kurmance bataji Da kyau ba Mami Asma"u kuma mamakin yadda Zaton ta ya sauya take yi anya Daada nada Hankali kuwa..? Abba ne ya Dago yana kallon Daada Cikin Sanyin murya yace"Daada bawai ina ja da mganarki bane..ko kin manta cewa Imran ya auri Sajida kuma Inteesar Shakikiya ce ga Sajida Daada duk da ba Haram bane ammh ana barin Halas ko dom kunya..! Karamin Mirmishi Daada ta saki kafin Tace"Na sani..Ina sane da komai..Ai ba aure Tsakanin Imranu da Sajida a yanzu..! Gabadaya mamaki ya hana kowa Mgana Inna Maimunatu ce tace a wannan karon"Daada bamu gane kan mganarki ba..! Daada ta Dago ido Tana Fadin"Ku juya amsarku Wajen Imranu..Kai Imranu gayamusu abunda kazo ka Fadamin..! Imran ba wani Tsoro ko Fargaba ya Dago kansa yana kallon yadda gabadaya Idanuwa suka koma kansa Ya gyara Zama yana kallon Idanuwan Mami Asma"u da Sajida da ya kusa Fadowa saboda Firgici da Tsoro. Cikin Kaushin sa yace"Na saki Sajida Tun Washegarin Ranar da aka Daura mana Aure da ita..! Ya fada kai tsaye Lokaci Daya yana Fito da wata Takardan a Aljihun Wandonsa ya mikama Yusuf Dake kusa Dashi Wanda yayi Jagale yana Bin Imran din da kallon mamaki. Kalamansa sun Daki kowa afalon banda Daada Data san mganar. Ammh Firgicin yafi bayyana kan Fuskar Baffa Kabiru,Mami Asma"u da Sajida wadanda Tsabar Rudani ko Motsi sun kasa. Daada ta Umarci Yusuf ya Warware Takardan ya karanta afili kowa yaji Cikin Sanyi jiki ya Bude Takarda ga Hand Writting din Imran nan ya Rattaba Rubutun kamar haka.