← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 190

Sashe 38

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Acikin Wannan Halin Imran ya Fito Daga Dakinsa Sanye da Jallabiya baka,daga alamu kuma Tashinsa keman Sigarin sa ne ya kare,Sannan kuma Dole yaga Sagir Domin yagayamai Yar gidan Wacece Wannan Mara Mutumcin yarinyar,Sai kuma Fitowarsa yaci karo da Abun mamaki Abba ne Zaune afalo yana Karatu.?
Gani yayi kamqr bai gani Daidai ba Sau ya kara Matsowa yana Mutsike Idanuwansa Still Dai Abu Daya yake gani Safiya ce ta Ganshi Da Sauri Tace"Ina kwana..!
Sai alokacin ya ganta Kallo Daya yayi nata ya kauda kai Shi ai bacin Ran Daya Kwana Daahi Jiya yasa yama manta da Yusuf da wata Amaryansa ma,asaman Lebensa ya amsa mata da Lafiya lau,Kusa da Abba ya Karisa ya Zauna yana kallonsa ganin haka yasa Abba ya Dakata da Karatun ya Dago yana Kallonsa Imran Cikin Mamaki yace"Abba ...Abba Kai ne..!?
Abba ya Murmusa kafin yace"Na"am..Nine Imran..!
Yafada Lokaci Daya yana Dafa Kafadansa Saboda Murna Imran baisa Sadda ya Rumgumesa ba yana Fadin"Plz Abba..Come Back..We Need Dr.Abubukar Malami Back..Wanda Ke Tsaye Ga kafafunsa Saboda Ahalinsa  ba Abubakar Malami ba Wanda Ya koma Yusud da Imran ne masu Kula Dashi ba..!
Abba ya Murmusa kafin ya Buga Bayan Imran alamun Lallashi Lokaci Daya ya Dagosa yana Fadin"Insha Allahu..komai Zai Zama Tarihi Tunda My Son yayi Dacen Samun Mace Tagari..ita tace na Fito Falo na Huta ta kuma Bani Qur"ani tace nayi Karatu..!
Abba ya Fada yana Nuna Safiya da kanta ke kasa..!
Imran ya murmusa kafin ya Mike yana Fadin"She do alot to us..Tanque so Much..!
Batace komai ba sai ta murmusa aranta Tana Tuna Hirarsu da Munari.
Abba ya kallah Kafin yace"Abba ka Cigaba da Karatunka..Bari na Je nan kasa Wajen Sagir..!
Abba ya gyada kai kafin yace"Sannan kuma Zaka Siyo Sigari ko..!?
Imran ya Waigo yana kallon Abba Kamar bazai ce komai ba sai kuma yace"Eh Abba..Ammh Zan yi kokarin na Rage shanta Saboda kai..!
Abba ya girgiza kai yace"Imran...Imran To Nagode..!
Bai kara mgana ba ya sakai ya Fice Daga Safiya Har Abba suka Bisa da kallo Abba yana kallota yana Fadin"Ni na Haifeshi ammh Wani Lokacin yana Matukar min kwarjini..Rashin Tsoronsa da Gaskiyansa Wani Lokacin Suna kara Sakani naji yana Burgeni da shiga raina..!
Safiya Batayi mamaki ba Tunda Munari ta gayamata Yusuf ma ya mata Bayani Abba bai nemi Jin ta bakinta ba yace"Allah ka kara Shiryamin ya"yana..!
Safiya ta amsa da Ameen acikin Ranta Shi kuma Abba ya Cigaba da Karatunsa Yana jin Wata Natsuwa na Shigarsa Natsuwarsa da Tun Bayan Rasuwar su Anni bai kara Samun irinta ba sai yau.

*Ina godiya Masoyana da Tarin kaunarku ga wannan Labarin Allah ya saka da alheri WhatApps fans dina Duka ina ganin Sharhinku ina kuma Godiya sai yan Wattpadian Kuma ina ganin Voting dinku da Comments dinku ina Matukar godiya Allah ya saka da alheri Allah kuma ya bar Zumunci Ameen..*

*Shakira...*
3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

           *🅿�15*
Chapter 38 · 0% Book details