Sashe 141
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin shirin Tafiyarsa ya Fito Daga Dakinsa jikinsa sanye da kayansu na Sojijin Sama Ruwa Navy,Bayansa goye da wata Jaka irinta Sojojin,Kafarsa ma Cikin Wani katon Booth din Takalmi,Yan aiki ne kadai ke ta Kara kaina Atsakar Falon suna ganinsa suka Fara gaisheshi hannu kawai ya Daga musu yana Kokarin Haurawa Sama Inda jerin Dakunan Dad yake Hade da na Mami. Suka ci karo da Umaima ta FitoCikin Shirin Tafiya makaranta Sanye Cikin Uniforman dinta,Jiya Hadda ta tafi Tun safe Sai s yammah ta dawo yau kuma makarantar boko Zata tafi Rumgumesa Tayi tana gaishesa ya amsa mata cikin dan yake da Rinanun Idanuwansa da suka Rine Saboda Damuwa. Cikin Mararaice Murya tace"Ya Khamis Me ya Faru a Dukku ne..?Tunda kuka dawo na kasa gane kan Dad da Mami,Kuma ina Anty Sajida..? Ban ganta ba nazata ta wuce makaranta ne inta kiranta bata Dauki Wayata ba..! Kallonta yake yi kur yana wani Tunani Umai tayi kankantar Sanin Wani abu Shiyasa yadan yi mata yake yana Fadin"Don"t worry kin ji ko Umai..Bafa komai kinsan Halin Mami da Rigima Dad kuma da kyaluwa ko..? Zasu Daidaita kansu Sajida kuma Tana makaranta she is ok..Kila karatu ne yayi mata zafi yasa baki jita ba! Yafada yana Shafa Kumatunta kallonsa kawai tayi tafa gani a group na Daurin auran Imran da Inteesar jiya da Daddare ma ta Kira Hafsah ta kara Tabbatar mata Tana da Tabbacin komai ya Faru to yana da nasaba da hakan. Bataso ta kara cewa wani abu,Shiyasa Tayi mai mirmishi Tana Fadin"Nasan Tafiya Zakayi..So safe landed bro..! Kai ya gyada mata yana Fadin"Tanque Lil sisy..! Daga haka ta wuce saman Dining ta Nufa Domin tayi Breakfast shi kuma ya Cigaba da Haura Stairs din Dakin Baffa Kabiru ne afarko yasa nan ya Fara Shiga yana Shiga ya iskesa cikin Shirin Fita shima Sanye cikin Suit ya Matse ga Rigarsu da Hulansu ta Lauyoyinan saman gado shi kuma yana daga Tsaye yana Duba wasu Takardu Khamis yayi knooking Lokaci Daya yana Turo kofa ya shigo. Baffa Kabiru ya dago kansa Daga Duba Takardun Dayake yi yana kallon Dan nashi Cikin Dan bayyana Damuwa kadan asamar Fuskarsa. Khamis ne yadan Ramkwafa yana Fadin"Gud mrning Dad..! Ya ijiye Takardun hannunsa yana Fadin"Mrning Son How was ur Night..!? Khamis a saman lebensa yace Fine ba Domin haka din bane Kallon Tsab yayi mai Kafin yace"Na ganka da Jaka are u going..? Khamis na Duba agogon Farin Azurfan Dake hannunsa Lokaci Daya Yana fadin"Eh Dad..jirgin 8:30pm zan bi Zuwa Anambra Insha Allahu..! Kai ya gyada yana Fadin"Allah ya Kiyaye..Allah ya bada Sa"a..Be a Man kaji.! Yafada Lokaci daya yana Dafa Kafadarsa Cikin Alamun Lallashi Domin ya karanci Tarin Damuwa da Rashin wani abu Acikin kwayan Idonsa Mirmishi kawai Khamis yayi kafin yace"bakomai Dad..Kai ne ma Zan bama Hakuri akan Abubuwan da suka Faru plz ka yafema Mami ku Daidata kanku Dad..! Kallonsa yake yi ko Kiftawa bayayi wani abu nayi mai ciwo acikin Ransa Dan Mirmishi saman lebe yayi kafin yace"Ai bani nayi mata Laifi ba ita tayimin..Kuma kana dai ganin abubuwan da suka Faru son..Ya Dace na kyale Asma"u taci Zarafin Daada a banza kuma na koma ina bata Hakuri..?in nayi haka kai kanka bazakayi Tunanin wani irin Uba ne ni ba..? Ko kuma wani irin D'a ne ni..? Khamis ya Girgiza kai yana Fadin"A"a dad ba haka nake nufi ba..Ina Nufin ka Nuna mata kuskuranta abunda tayi gaskiya bata kyauta ba ka nuna mata Bata yi Daidai ba ku Daidaita kanku Taje ta bama Daada Hakuri is better in mu ya'yanku indai kuka Shiryan kanku..! Kai ya kada mai kafin yace"Shikenan..! Khamis ya Rusuna yana Fadin"Zan ga Mami kafin na wuce Dad..! Yana Daukan Takardunsa yake Fadin"In bazaka Dade ba sai mu ijiyeka Airport kafin na wuce Office..! Khamis ya juya yana Fadin"Yanzu zan Fito Dad..! Yafice Uban ya Bisa da kallon Tsausayi ya Tabbata karfin Hali kawai yake yi ammh abun ya tabasa Asma"u batasan ta Ruguje Farincikin ya"yanta alokaci Daya bane,Sakarya kawai. Takardun Hannunsa ya ke sakawa cikin Karamin Briefcase dinsa. Knooking ya farayi yaji Shuru jin Kofar tana Bude yasa ya Tura ya shiga Lokaci Daya da Sallama. Tana zaune kan kujeran Dreesing Mirror Tana waya shiyasa bata ma ji knooking din ba. "Ka shirya komai..Yau nake so na shigar da Complain din Brr.Zailani..! Iya abunda yaji kenan ya Kira Sunanta da dan karfi. "Mami..! Da sauri ta waigo cikin dan Tsoro jin kira Daga sama ganin shine yasa ta Sauke ajiyar Zuciya ta Mike Lokaci Daya Tana Fadin"Zan Sake kiran ka Brr.Zailani..! Daga haka ta Datse kiran Tana kallonsa lokaci Daya Tana Fadin"Son badai har zaka wuce ba..? Tafada tana kokarin Zama gefen gadonta. Kallonta yake yi cikin Tsaisayinta ganin yadda tayi wani Figai Figai Cikin kwana Biyu ba gayun nan sam kamar wacce ta tashi Daga Cuta Idanuwanta duk sun kode saboda kuka da Damuwa. Ajiyar zuciya ya Sauke kafin yace"Why Mami..? Meyasa bazaki bar mganar nan ba..? Daad zaki kai kara ko Daada ko su Baffa..? Karamin Tsaki taja Kafin tace"Yancina Zan kwata son..Rayuwar yata suka Lalace Wlh bazan bar wannnan abu ya Tafi a banza ba ka duba ka gani Sajida Tana gayamin mgana ni Mahaifiyarta gaban kowa da kowa..? Wlh Bazan Lamunci su Rabani da y'ata ba Dukkansu zan maka su a Kotu Dad dinka naga alamun yana so ya manta da ku ya"yansa ne zai Biyema yan"uwansa to bai isa ba ko ya amince ko bai amince ba sai na shigar da Complain..! Tafada cikin son Tabbatar da mganarta. Khamis ya Dafe kansa yana Fadin"Mami why nace.? Inace ke kikace baki son Auran Sajida da Imran kuma yanzu komai ya kare Why kike hakane.? Inace abunda kike so aka yi miki..?me yayi Saura..! Don Allah ki bar mganar nan ki Je ki samu Dad kuyi mgana ki basa Hakuri sannan kije har Dukku ki bama Daada Hakuri Saboda mganar Gaskiya baki kyauta ba Uwa uwace kuma ana Sauya mata ammh Mami Ki Sani ba"a Sauya uwa kamar yadda Muma kome kika mana kome kika Zama kina nan a Mtsayin Mahaifiyarmu bamu isa mu sauya ma Tuwo suna ba kuma sai in da karfin mu ya kare in muka ga wani zai Tozartaki..! Mami Asma"u baki ta saki da Hanci Tana kallonsa kafin ta Mike Tsaye da Sauri Tana Fadin"Au Shi Kabirun ne ya aiko ka ka gayamin haka..? Yana kokarin mgana ta Dakatar dashi da Hannu Tana Fadin"Ya isa..Basai ka kara cemin wani abu ba..Bana Bukatar jin komai Daga gareka ai ka Riga ka Fadi sakon ka Shikenan sai ka bari nima nayi mgana.! Shuru kawai yayi yana mamakin Taurin kanta Cikin bacin rai ta Cigaba da Fadin"To in aiko ka yayi kaje ka Fadamai bazan je na bama kowa Hakuri ba Domin ban Batama kowa ba Ni ya kamata ba abama Hakuri ni da aka Lalatama Yata Future dinta Bazawara zan kirata ko Sakin Wawa..?wannan ai Cutar ma tana da yawa in shi yayi shuru ni sai nayi Shuru..? Wlh basa kaunarsa sunan yana Dan"uwansu ne da basu yi mai haka ba In shi bazai iya cewa komai ba Ni zan iya kan wannan mganar sai inda Karfina ya kare..Ni ina da kudi kuma na gaji kudi da asali Zan iya shari"a Dasu har Mahadi ya bayyana Shege ka Fasa..! Kai ya gyada kawai kafin ya Juya yana Fadin"Mami kiyi Tunani..Ki kara Tunani abunda kika aikata bai Dace ba..kuma wanda ma zaki aikata bai Dace ba..Ina Tsoron abubuwa suxo su Lalace..! Tsaki taja Tana Fadin"Komai ya Dade bai Lalace ba..Bazan ja da baya kan mganata ba..! Ficewa kawai yayi ransa na kara Kunci In Mami ta aikata abunda tayi Niyya komai fa Zai Lalace wazai Dakatar da ita..? Dad bafa bazai iya Dakatar da ita ba,Ta gama Rainasa sai dai in Justice Tafida zai kira ya Fadamawa Mahaifinta Kila in ya mata mgana Taji Hajiyarsu kuwa bama zai kirata ba Domin kamar gadon Hallayanta ne Mamin ta Dauki bama zata Dakatar da ita ba sai ma kara mata Karfin gwiwan da zatayi. Koda ya Fito Dad na Jiransa ya shiga Mota suka Fice Umai ta Dade da wucewa makaranta a Airport suka ijiyesa kafin Baffa Kabiru ya wuce Wajen aiki Kafin Jirgin su ya tashi Khamis ya Kira Kakansa Tsohon Alkalin Alkalai na kasa Gabadaya Justice Tafida bayan sun gaisa ya Kwashe komai in Brief ya Fadamai sannan ya karishe da rikonsa kan ya Dakatar da Mami kan shigar da wannan Complain din..! Justice Tafida ya Fahimci jikan nashi kuma yayi mai alkawarin Zai kira Mami Tazo gida ta samesa zai mata mgana Daga haka suka Rabu Lokacin ma Jirgin su ya kusa tashi sai kiran suna akeyi kashe Wayarsa yayi ya Hau kan Layi yana Tunanin in ya tafi zai Dade bai Waiwayi gida ba sai ya manta da Bacin Ransa ba zai kara Dawowa kuma wani Bacin ran ya kara adding kan nashi ba. Koda karfe 9am na Safe yayi jirgin su ya Lula Sararin Samaniya yana Fatan Allah yasa Kakan nasa yayi wani abu In kuma bai yi ba to abubuwa fa zasu Kwabe ne,Domin yadda yaga Dad ya Shirya aikata komai kamar yadda Mami Tace baja da baya. Ashe duk wayar nan da Justice Tafida yayi Hajiya Turai Mahaifiyar Asma"u Tana Zaune ta gama jin komai suna gama mgana ta fara Bala"i tana Fada Tana Fadin"Wlh kada kace Zaka Hanata Kwatan yancinta..Wannan ai Ya saba Sharia..auran kaskasci sukayi mata da Farko ni nan na Taushi Asma"u ta yi Hakuri da mganar kuma Shikenan yanzu sai a sakar mata yar da ko Gidan auran ma bataje ba? Ai ko Kabiru bai Taki gaskiya ba Shi din banza waye shi?Takala dan talaka Asma"u ai ba Kalar sa bace Soyayya ce kawai da Allah ya Dora mata ammh ai Wlh ko Daya Kalan Zaren ai ba Kalan yadin bane in shi yana Tsoron yan"uwansa bazai iya mgana ba a kyalemin ya'ta ta kwaci Hakkinta amfanin Ilimin kenan! Justice Tafida ya Murmusa kafin yace"Hajiya Turai kubi komai a Sannu..Kada kimanta Kabiru ke auranta..Sannan wannam mganace ta Danginsa fa da Mahaifiyarsa..Anya Asma"u ta taki gaskiya?Daman ai tace bata son Auran yar taata da shi yaron Dan uwwn mijin nata ba ya Saketa ba ba shikenan an muku abunda kuke so ba kuma mganar shigar