Sashe 136
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
baya Tana ta kuka yana Lallashinta Fadi take Shikenan Nagama Tozarta ni Asma"u na gama Yawo..! Baffa na jinta yayi kamar baya Motar Umarni ya bama Direeba kafin ya kwana yayi hon megadi ya wangale get suka Fice Daga Haraban gidan cikin su ba wanda iya Bude baki yace Ina Sajida domin ai idonsu ya Tabbatar musu da abunda ta aikata bata Bukatar bin su. Suna Fita Dada jikinta ya Rikice Dole Daddy yayi ma Dr.Zubaida waya tace Gatanan zuwa Gabadaya Taron ya tashi Zucicyi ba Dadi banda Imran da Ransa Fes ko ajikinsa. Sajida Inna Maimunatu ta kamata zuwa Daki Tana ta lallashinta da bata Nasiha ammh bata Daina kuka ba Su Abba basu samu natsuwa ba sai da Dr Tazo ta Duba Daada Jininta ne ya Hau ta bata mgunguna Tace data samu Barci Shikenan kuma adaina Tuna mata da abunda zai sakata Damuwa,jininta ya hau sosai su Abba suka amsa da ba komai zasu kiyaye dukkansu suna Dakin Daada sai da ta Samu barci suka Fito sukayi Sallar La"asar data Subuce musu, kowa ka gani ba Fara"a Saboda Halin da Taron ya tashi da abubuwan da suka Faru ba masu Dadi bane. Banda Imran Dake cikin Daki yana aiki Bisa Laptop dinsa Ransa Fes ko ajikinsa Sagir na kallonsa yana ayyana Imu karshe ne Shi ko ajikinsa Daga gani ma Dadi yake ji to me zai Damesa...? Abunda suka aikata ne suke Girba.