← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 190

Sashe 43

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shigowarta Bedroom Din kenan Dauke da Karamin mug,Wanda Ruwan Shayin Na"aNa"a,Alhaji Mustapha ne Zaune gefen gado Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara,Ya Zabga Tagumi da Hannun Bibbiyu Har ta karisa kusa Dashi bai sani ba,Domin yayi Zurfi Cikin Tunanin Daya Tafi kan Side Drower din Jikin gado ta ijye mug Lokaci Daya ta Zauna Gefensa Tana Fadin"Abban Intee..!
Ta fada Tana Ciremai Tagumin Sai Lokacin ya Dawo Cikin Hayyacinsa ya Fahimci Ta shigo Har tana Kusa Dashi.
Ajiyar rai ya sauke kafin yace"Bansan kin Shigo ba..!
Tace Tana Kallonsa"Ina fa Zaka sani kayi Nisa Cikin Tunani..kuma kasan yawan Tunanin illah ne ga Lafiyan Dan adam..!
Sauke Dayan Hannunsa yayi Daga Tagumin yana Fadin"Umh..Tunani ya Zama Dole Sahala..Wlh na kasa Sukuni Tunanin Halin da muka baro Daada aciki ne ke Damuna..!
Umma Ta yi shuru kafin itama Tace"Wlh nima Abban Intee..Daada ta kasa fa..Yaya malami kawai take son gani..Kaji fa Baba asabe Tana Fadin ko acikin Barcinta sunansa take kira..!
Ta karishe Fada Cikin Bayyana Jimaminta.
Alhaji Mustapha ya Sauke Twagayen Numfashi kafin yace"Ko achan Baya Soyayyar Daada ke ma Ya Malami ta Dabam ce shi din D'a ne masu Soyuwa gareta Duk yafi mu sanyin Hali Shiyasa yafi Shiga Ranta Dole Daada ta Shiga Damuwa Saboda Rashinsa Kusan kwanciyarta asibiti Biyu acikin Satin nan fa..!
Umma tace"Ni Tsorana kada Hawan jinin nan ya Fadar da ita kasan fa Mugun Ciwo ne..Daman ta Amince ko ku saka baki kai da su Hajiya Bintalo ta yarda Tabi Baban Sajida Abuja In ma Baba asabe take ji Duka su tafi Tare nan Dukkun sai a Rufeshi In Allah yasa ta Samu Sauki sai su Dawo ni aganina Chan zai fiyemata ko kobamai akwai gilmawar Wani nata agabanta nan kuwa sai dai in an Taka an je..!
Har tagama Mganarta bai ce mata komai ba sai Chan yace"Ai Daada alkwarin tayi ma kanta bazata bar gidanta Dukku Da Ranta ba..Sai dai in Gawartane ta yarda a Fitar da ita..!
Umma tace"ai kaji kuma..Allah dai ya bata Lafiya Wlh jiyan nan da muka isa Naji Tsoro Hakama Basheer yace sai da nayi kwallah Lokacin Data Rike Hannuwanku kaida Baban Sajida Tana Rokon ku ku Sadata da Malami kafin ta bar Gidan Duniya..!
Yayi kasake yana jinta Cikin wani yanayi kafin ya Mikamata Hannu yana Fadin"Bani Tea din..!
Ba musu ta Dauko ta mikamai ya karba yakai baki Kurba Daya Zuwa Biyu ya Dakatana Yana Daidaita Zamansa Lokaci Daya yana Fadin"Baki san wani abu ba Salaha..Jiyan nan da Barrister ya kirani yana gayamin wai Dr.Zubaida Ta kirashi tace Daada na asibiti Wajenta Itama Tana gidan Baba asabe ta Kirata jikin Daadan ya tashi na Tsorata..Duka Duka ko fa kwana Hudu batayi da kwanciya asibitin ba ta Kwana Daya aka Dawo da ita gida..Ciwon Daada wlh yana Tadamin da Hankali akoda yaushe Ina Rokon Allah Duk inda ya Malami yake Allah ya bayyanashi Daada nada rai kada Sai ta Mutu Hakkinta ya kamamu..!
Ya karishe Fada yana kara Kurban Tea din Hannunsa Umma Tayi Kasake kafin Tace"Hakki kuma..? Ai naga kuna iya bakin kokarin ku Wajen Nemansa bai kamata kace in Kun gaza Hakan Hakkin Daada zai kama kuba sai dai in shi Yaya Malami Tunda ko Yaya ka Lalace Uwa Uwace Har Abada kuma Tana da Nauyi da Hakki akansa..
Bai katseta ba sai da ta gama kana ya mikata mata Mug din ta karba ta Maidashi inda ta Daukosa,Shi kuma ya Mikar da kafarsa Saman Cafet din Dake malale a Bedroom din yana Fadin"Me kika sani Salaha..? Ai Duka Alhakin Barin Ya Malami Gida da Iyalansa yana Wuyanmu ne..Musamman Barrister Domin kinsan da Zafi sosai Alokacin da Abun ya Faru Ya Maalami ya Samu Depression kan Abunda ya Faru da su Yusuf suma ba wani Hop kansu sai yake ganin kamar Rashin Hakuri ne da rashin Yarda da kaddara yasa komai ya Lalace Har Laluran tasa tana ta gaba Kullum Likitoci suna cewa ba Cigaba..Dalilin haka yasa yayi ta Fada gaskiya munyi kuskure Domin naga wani Shiri,Tv Kwanaki Wani likita na mgana kan masu Fama da irin Lalurar Ya malami yace Ciwon Damuwa ne Ba Hantara ko Fada suke so ba ajashi ajiki Lallashi da ban baki a Zauna dasu adaina bari suna Tuna Abunda Zai sakasu Tunani,arika yin Abunda Zai sakasu Farinciki akoda yaushe kuma Tsakani ga Allah Bamu yi wannan kokarin ba Mun kawo su Dukku Gaban daada Mun koma Garuruwan mu,bamu yi La"akari da Daada ta Fara Manyata ba, bazata iya wani Kokari ba..Sannan iyalansa suma Raunin ya Tabasu da Har baza su iya Taimakon kansu ba Ballatana Shi Yaya Malami Ahaka suka nuna suna son Komawa Gida kuma na Tabbata Saboda Wannan Dalilin ne sukayi nesa Damu bayan sun koma Lagos Sun ga ba wanda ya Damu dasu..Na Tabbata Yusuf bazai yi Tunanin Yin nesa da Kowa ba Face mai muradden Halin nan Duk Cikin Dangin mu Imran yaron yana da Zafi Daman Chan Tun Farko Bai da Shiga Dangi Sosai sai da ya Girma ne ma Ya malami ke Tarosa in zai zo Dukku..Ina da Tabbacin Shi zai ba Yayan Shawaran Haka Shi kuma Bashi da Zabi sai ya Yarda da komai Suna ganin yin Nesa Damun din Shine mafita..Tabbas muma da laifin mu..!
Ya Karishe Fada Lokaci Daya yana Saka yatsa ya Dauke kwallar Data gangaromai Umms Jikinta yagama yin Sanyi tace"Tabbas Hakane ba"a kyauta..Rashi ne sukayi Babba..Allah ya jikan Zuwaira Ya malami yayi Shuru Dole Ya Shiga Damuwa mace mai kirki Da Sanin yakamata Ga kuma Rashin ya"ya kai yaga Jarabawa Wanda bakowani bawa bane zai iya Tsallakewa Abban Intee in Wani ne sai ya kashe kansa..!
Yayin Saurin katseta da Fadin"Wlh Abun Allah ya kare..Hakama likitan yace ,Wani babban Likitan kwakwalwa ne Daga asibitin ABU Zaria yace Tabbas suna kashe kansu To zasu ga basu da wani Sauran Amfani a Duniya..Wlh jikina yayi Sanyi sosai ina so na ganar da Barrister kuskuransa ammh kuma Ban samu Dama ina ganin kamar Shi Har yau Laifin Ya Malamin yake gani..!
Umma tace"Wlh kuwa ai kaji Abunda yake Fada yau..Wai Malami ya Tafi Da gangan kuma gashi yanzu a Rashinsa zai kashe Daada..!
Umh kawai ya iya Cewa ya kasa Mgana,Umma ta Mike tana Fadin"Allah ya kyauta ka Rage Tunani Don Allah mu Cigaba da gayama Allah..Insha Allahu Allah zai bayyanasa..!
Ya amsa mata da Amen,Mug din Tea din ta Dauka Tana Shirin Ficewa yace"Bashir ya Tafi dasu Abiden ne..? Naji ban ji Motsin su bane..!?
Umma ta Dakata Tana Fadin"Ai Rigima suka sakamai nace ya Tafi Dasu Wajen Uwarsu..Tun jiya basu ganta ba..!
Ya jinjina kai kafin yace"Yaran ne akwai Rigima Irin Diyarki Intee..!.
Umma ta Tabe baki Tana Fadin"Diyar ka Dai..Ni da Tunda tatafi ta yadani..Ta kira jiya muna Dukku Tana Min tsiyan ta samu Mamarta Mai sonta ba irina mai Hanata Sangartanta ba..!
Mirmiahi yayi kafin yace"Ai gaskiya ta Fada..In wani yaki ka da wuni.Wani da kwana Dubu zai soka..ai zan bar ma Yaya Aminan ita kawai ta Aurar da ita achan mu namu gayyata ne Kadai..!
Umma tace"Wa Kai din..? Dama Zaka iya ne Abba Intee..Da Ya Amina Taji Dadi..ammh Sai dai kulafuncinta bazai barka ka barmata ita ba Jifa Tafiyar ta fa sai da kafi kwana Biyu Baka Walwala in ka Dawo Gidan nan kaga bata nan..!
Yana yar Dariya yace"Ai jiya Da Daddre na kira Inteen har tabani Ya Aminan muka gaisa Ta Tambayi Daada da Jiki..Sosai naga Inteer tana jin Dadin Zaman kano da Karatun na Gabadaya..!
Umma tace"To tana samun Damar yin sagartatan son ranta mana..!
Mirmishi ya sakarmata ita kuma ta Fice Tana Mita tana Fita ya Kwashe Kafafunsa zuwa kan gado ya gyara Kwanciyarsa Tunanin da baya so shi ya Shigayi Babban Tashin Hankalinsa Rashin sanin Inda Malami yake Domin har yau suna kan nema kuma ba wani Labari Daga kowani bangare Kuma an Tabbatar musu Tunda suka bar Lagos Har yau basu kara Takawa ba..
Ya illahi ina ya Malami ya Shiga Shida iyalansa ne..?Allahu ka bayyanashi ko Domin Damuwar Daada garesa..!

*Shakira..*
3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

           *🅿�17*

*Monday*
12:12pm
BUK
Chapter 43 · 0% Book details