Sashe 70
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yana da Laifi Kadan ne na Biye maka da yayi bai fadamaka gaskiya ba. ni kuma har ga Allah bana sanin abubuwan Dake Faruwa wani Lokacin.' Ran Baffa Kabiru ya baci cikin Fushi ya kalli Daada yana Fadin"Daada Kifa Daina dora alhakin komai akaina ki Dorashi kan Malami Da ya"yansa Musamman yaron nan nashi Kanin Yusuf Mara jin mgana ga shi yana ganin yana Daidai da kowa Tun kafin hakan ta Faru daman baya son Zama Cikin Danginsa Bazan ga Laifi in sun Tattara sun tafi wata uwa Duniya ba..! Daada cikin tsawa tace"Yimin shuru anan wajen Kabiru kada ka kara cewa Tak..in ba haka ba sai na saba maka..! Kowa afalon sai da yaji wani iri Baffa Kabiru kuwa kamar ya yi Bindiga haka yake ji saboda Fushi Ita kuma Mami Asma"u Sai cika take itacda yarta Don me Daada Zata Tara Mutane tana cima Mijinta Zarafin Bazata Dauki wannan Rainin ba. Daman Tun malami nan nan Tasu bata zo Daya ba Tana ganin kamar shi ne yake so ya goga Kafada Daya da Mijinta akomai kuma alokacin Anni itama tana sakawa tana Cirewa Mai Tsada Su Asma"u ma badai ka gansu Cikin wani yanayi ba Daka gansu Zaka Fahimci suma din sun Tara kodaga Kayattacen Gidansu na Lagos Mami Asma"u tasan da Anni Zata goga acikin Dangi,saboda bata kaunar wani ya fita ita da Mijinta da ya"yanta ako"ina ne shiyasa bayan Faruwar abun Take da Zuga Barrister kan meyasa Daada take Wahalar dasu ne kan Nemo wanda basu san ina Ya shiga ba ko alokacin Dayake Ma Abba Fadan ya haukace duk itace ke Kitsamai wai yaki Daukan kaddaransa Tayaya kuma zai zo shi ya Zame musu Lalura Allah ya yita Mace mai son kanta da yawa shi kuma Baffa Kabiru yana Matukar sonta ya gama bata Dukkan Amana. Daada ce cikin Muryan kuka Tace"In bazasu yi nesa damu ba wani mataki kake so su dauka..?Suma ya"ya ne Tamkar ya"yanku Bazasu taba Jure Zama kana kiran Mahaifinsu da Mahaukaci ba Kabiru alhalin kasan Rayuwace da Rashi ta maida Malami haka da Kaddaran da bawa bai isa ya kaucemata ba..Rashin Rai yayi matarsa Zuwaira da ya"yansa Har guda Uku Kabiru ka Fadamin ko kai ne Wani Hali Zaka tsinci kanka..? Na tabbata yadda kake son matar nan naka da ya"yanka in wani abu irin wannan ya samesu na Tabbata kai kila Sai ka Rataye kanka ma Saboda Tashin Hankali..! Gabadaya falon sai ya Kaurevda Mganganu kasa kasa na Tuna abunda ya wuce a Shekaru uku da suka gabata Jikin kowa yayi sanyi Mami Asma"u kuwa Kallon Daada Take ta cikin Glass dinta aranta Tana Fadin"Bakin ki ya sari Danyan kashi mai Doyi Daada. ! Take fada Acikin ranta Domin Gani take kamar Daada na yi musu Mugun baki ne.. Daada kuka take harda Shasheka ganin haka yasa Daddy ya Matsa gareta yana Fadin"Don Allah Daada ki bar kuka kina Karyamana Zuciya..Ga Matayen mu ga ya"yanmu harda Jikoki bai kamata ba don Allah ki bar kukan nan ki Share Hawayenki..! Batayi gaddama ba ta Share Hawayenta Tana jan majina tace"Naji zan Share Hawayena ayanzu..Ammh ku sani har in dai ba Dan"uwanku kuka Dawomin dashi ba bazan Daina Zubar da Hawayaena ina kuka ba..Kuma In har baka gayama Kabiru Cewa Laifinku bane game da Barin Malami gida ba Shima baZai sai na Fasa Fadin kune Sanadin Barinsa Gida Dashi Iyalansa agaban ko waye ba..! Daddy ya dukar dakai yana Fadin"Gaskiya ne Daada..Ni ban Musa ba Muna da Laifin Tabbas Wajen Ya"yan Ya Malami su Daukesa Daga Cikin mu..! Da sauri Baffa Kabiru ya Dago yana kallonsa kafin yace"Au kaima ka yarda Laifin mu ne..? Daddy ya dago yana kallon Baffa Kabiru yace"Gaskiya ce Dole a Fadeta Baban Sajida..Na Dade ina son na Gayamaka wannan gaskiya..Alokacin da abun ya faru ba haka ya kamata mu Tafiyar da Ya Malami ba..Yana Bukatar Lallashi da jansa ajiki da kuma Nunamai Soyayyah,alokacin bai Bukatar fada ko Hayaniya domin amasu irin Laluransu Fada yana kara Karfin Tasirin Cutar acikin jikin mutum sai ya rika ganin kamar shi kadai ne,Tabbas alokacin muna da kaso mafi yawa Tunda bamu Jasa ajiki ba bamu nunamai kulawa ba sai ma Kokarin numamai ko ta Halin kakane sai ya koma yadda yake afarko kuma abun ba haka yake ba ita Cuta ce take Shiga Farat Daya Waraka sai a Hankali kuma bamu yi la"akari da Raunin Daada ba da ya"yansa kansu da suma Raunin ya Tabasu ba..bayan haka suka nemi komawa Lagos ka Amince musu bakayi Tunanin Tayaya Zasu iya wannan Rayuwar su kadai ba bayan Tafiyarsu Kaje har Gidan ka Samesu cikin Wani hali bakayi wani yunkuri domin Dawo da Rayuwarsu Daidai ba ka taho ka barsu bayan wani Lokaci aka nemesu aka Rasa tayaya bazamu dora alhakin Faruwar hakan a wuyan mu ba..? Daada uwa take garemu Hakkinta na kanmu ya Zama Dole mu yi abunda zamu yi mu Daina Sakata kuka..! Gabadaya kalamansa ya Kashema kowa Jiki shi kanshi,Baffa Kabiru ya kasa Cewa komai Domin yasan gaskiya aka fada. Daada kuwa Mirmishin ta saki irin na Manya kafin tace"Irin wannan Ranar nake jira....yau in ku bazaku iya ba Zan Raba aikin harda ya"yanku wasu ku nan kusan Baffan ku Malami shi yake Bima Kabiru bayan Hatsarin Jirgi ya Rutsa da iyalansa abubuwa sun Faru marasa Dadi har yayi Sanadiyar barin sa Gida shi da ya"yansa guda uku wadanda basu san sa ba Yanzu Asabe zata Dauko Hotonsu ku karba Daya bayan Daya ku duba wanda Allah yasa yayi katarin Ganin Daya Daga Cikin su Sai ya sanar damu..! Asabe Shiga Dakina cikin Sip ki Daukomin Hoton nan..! Ta Karishe fada ta Kallon Asabe Dake gefe da Sauri ta Mike tana Fadin"To Daada..!