← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 190

Sashe 18

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ban samu zuwa ba..Taje har gidansu Nasara,! Mama tace"Allah sarki..Suma munyi mgana dasu Ranar Har Yaya Salisun Yake fadamin Nasaran zata Fara karatu itama anam kadunan..! Umma tace"Eh kasu zatayi ita..! Mama tace"Allah ya taimaka..! Umma ta amsa da Ameen Ameen suka Cigaba da Hiransu na Zumunci. Inteesar kuma taji Dadin wankan Datayi da ruwa mai Zafi Bayan ta Fito ta Fiddo kayan Shafanta ta Shafa ta Bude akwatinta ta Dauko wata Riga da Sikat mai gajeren hannu ta saka Saboda sune na zaman gidanta,atamfa ko wani leshi bai cika Damunta ba sai Umma ta matsa mata ko kuma taje gaida Inno ta isheta da Mita haka Daada Shiyasa bata marmarin zuwa Dukku har yau har gobe Shiyasa ba kowa ya santa ba sai dai sunanta da aka sani ba. Bata wani cin yunwa tunda sun ci abinci kan gadon ta kwanta Tana Sauke Numfashi Lokaci Daya Tana bin Dakin da kallo Tana Hura hanci tana Shakan kamshin Turaran Wutan da Mama ta Turara dakin dashi Masha Allah komai tsab Dashi Dakin ya Burge inteesar Duk da bai kama Kafar Dakinta na Gida ba sai dai ita Ba haka iyayenta suka bata Tarbiya ba,Bata da Dagawa ballatana Girman kai Kowa Daya ta Daukeshi Umma ta Koyamata iya zama Duk inda Rayuwa ta Fada mata ballatana ita kanta umman ba masu arziki bane Har yau har gobe Mallam Babba Hatsi yake saidawa akasuwa Itace sana'arsa Mahaifinta ne mai arzikin ammh bata da Halin kyama ko nuna tafi kowa barta da Sangarta da Tabara irin na yaran da iyayansu suka Shagwaba Shima bawai na Dolanci ba Domin tasan me take yi. Tana Daga kwwncen Taji Umma na gayama Mama ta rika Zaneta in Taga zata mata Sangarta ta tsawatar mata kamar yadda Zatayi ma Sagir Mama tace bakomai Insha Allahu Baza"a samu matsala ba,Tana da kwancen Take Tura baki,Sanin Halin Umma taso ta Fito Wajen Daddy suyi Hiran bakwana Gajiya ta Hanata Tun tana Jin Hiransu Umma har barcin yammah ya kwasheta sai dai Taji Umma ta Daga mata Duka Tana Kiran Sunanta. Bude Idanuwanta Tayi Cike da Barci Ta saukesu kan Umma Data Dauro alwala ga Ruwa nan na Diga,kan Fuskarta Hararanta Umma Tayi Tana Fadin"Kinga irin Halin naki ko..? Sai ki tashi kiyi Sallah..! Tafada lokaci Daya Tana kokarin Sanya Hijabi ta tada Salla kan Darduman da Mama ta Shinfida mata. Dakyar Inteesar ta iya mike Jikinta duk ya Mutu ga kasalan Data kamata ta Shiga Tiolet tayo alwala Tazo gefen Umma Ta Tada Sallah bayan ta Bude karamar akwatinta Data Jera Sabbin Hijabanta da mayafanta ta Dauki Daya cikin wanda Anty Hauwa ta bata ta saka ta tada Sallah. Nan itama Mama ta Shigo Tayi alwalan Tayi sallah Bayan ta idaar ne ta juya tana kallon Inteesar tace"Maryam bazaki ci abincin bane..? Inteesar taji abun wani bambarakwai Domin bamai kiranta da asalin sunanta sai Inteesar,Kai ta gyada kafin tace"Kila sai anjuma Inna Cikina ya cika..! Umma ta karbe da Fadin"gatanan sai kin mata da gaske..Bata son Cin Abinci shiyasa kullum Zaki ganta jiya iyau Sillen kara kamar a Hureta ta Fadi..! Umma ta karishe Fade Tana yar Dariya ganin yadda Inteesar din Ta Zumbura baki tana Dakuna Fuska ganin haka yasa Mama Jawota Jikinta ta Rumgume Tana Fadin"Kyale Sahala..In kika Tashi Zuwa Hutu na Tabbata bazasu ganeki ba..In ita bata son yar Dake ni ina so..Daman Daga Sagir sai ni agidanan naji matukar Dadin zuwan yata..! Tafada Cikin nuna Murnanta Sai Ta bama Inteesar Tsausayi Sai ta kara Lafewa ajikinta Tana Fadin"Yauwa Mamata..Daman Umma bata sona..Nima na samu Mamata yanzu..! Umma ta kyabe baki Tana Fadin"Kuje kuyi ta kaya..Indai wannan ne zaki dawo min ne..! Mama tace"Insha Allahu bazamu Taba Dawowa ba sai adawowar alkhairi..! Inteesar sai Mirmishi take Na jin Dadi Bazatace batasan Inna Amina ba,sai bata taba Zama da ita sosai haka ba wani lokacin in tazo tana makaranta sanda zata Dawo kuma Sai tatafi Gidan Inno ranar data kwana gidansu kuma Tana Dakin Umma ba wani Shakuwa Tsakaninsu sosai... Hira suka Cigaba da yi sama Sama Inteesar an samu Abunda ake so sai ta kara lafewa Jikin Mama Kamar wata mage har tana lumshe ido,Abunda bata samu wajen Umma ita bata yarda da wannan Sakarcin ba. Suna cikin Hiran ne sai ga Sagir ya Shigo bayan yayi sallama Suka amsa mai ya Shigo Ciki ya Duka yana gaishesu da yammah suka amsa mai sai yake fadamusu Daddy ne zai wuce masauki sai Gobe zai Dawo. Mama ta Mike Ita da Inteeaar Dataji Zencen Tafiyan Daddy. Umma ma ta mike,Mama ce tace"Bazai kwana anan ba Salaha..? Tunda ga Dakin Sagir zai Ishesu sai shi ya barmai katifar Shi kuma sai ya kwanta kasa..! Umma tace"Haka kawai Yaya Amina shi da Dakinsa yayi kwanan kasa..? Barshi yaje masauki Koma kinyi mgana bazai Zauna ba..! Mama bataji dadi ba tace Shikenan Dukkansu suka Fita Tsakar Gida Inda Daddy ke Tsaye da Gudu Inteesar ta isa gareshi ta Rungume Tana Fadin"Daddy na..! Shima riketa yayi yana Fadin"Intee ta..Uwata ta kaina..! Yafada Lokaci Daya yana Shafa kanta,Kara lafewa tayi ajikinsa kamar wata mage Sagir Dake gefe aransa yace"Yarinyar nan akwai Shagwaba..! Mama ce tace"Alhaji bazaka kwana anan ba..? Naga ai duk gida ne..? Daddy yace"A"a Yaya Amina bari naje masauku da safe zan dawo mu wuce in Allah ya yarda..! Bata da tacewa illah ta Bishi da Allah ya kiyayewa ya Fice Yana Rike da Inteesar Umma da Sagir suka Bi bayansu Har zaure Inteesar ta Raka Daddy tana ta mai Shagwaban gobe bazata iya Shiga makaranta ita kadai ba Wahala Umma tayi karamin Tsaki Tana Fadin"Kada Allah yasa Ki iya..gobe da wuri Insha Allahu muna kaduna in zaki warware wannan Son Jikin naki da Rangwantanki kiyi karatu..Daman Daada ta kira waya tace abaki kina bacci tace na Fadamiki ki Dage da karatu banda Sangarta da Sakarci..! Kafin Umma ta gama mgana Inteesar ta kusa saka kuka Ta kalli Daddy tana Fadin"Daddy kaji Umma ko..? Daman Daada nan itama bata sona.Koda yaushe tayi ta min Fada..Taci ka Fadan Tsiya..! Umma tayi mata Dakuwa Tana Fadin"Kinga naki nan..? Wato Tacika Fada ko..? Ai Mai Biye mikin ma ta isa dashi kuma Fada take yi mai a zauna Lafiya ballatana ke..! Ai sai Inteesar tayi kokarin saka kuka Tana Dira Kafa Daddy ya Dafa kanta yana Fadin"Kada ki bata Hawayenki Inteen Daddy..Gobe da safe ki Shirya da Wuri in xamu Wuce sai mu Biya ta makaranta inkingama Komai kin Fara Shiga lacture sai mu wuce..Ga Dan"uwaki nan sai muje Dashi sai ki samo abokin Dawowa Tare..! Sai alokacin Ta saki Ranta Daddy ya kalli Umma yana Fadin"Sahala bana jin Dadin yadda kike Hantaran yarinyar nan fa..? Duka nawa Intee take da zaki bi ki Rika mata Fada kamar wata Babba..? Ba Umma bace take mamaki ba Domin ita saba gani Sagir ne yake kallon Inteesar yana auna mganar Daddy wai duka Duka nawa take..? Wannan gansamemiyar Budurwance yarinya..?lalle yau yana ganin Abu xai so Imran yana wajen nan ya Tabbata da ya kusa Mutuwa saboda Takaichi. Umma bata tsaya bata bakinta ba ta Juya tana Fadin sai Allah ya kaimu ta shige Cikin gidan Ta bar Daddy na Fadama Sagir gobe tare zasu shiga makaranta Dashi Sagir yace ba mtsala Dayake Shima yana da Lacran safe. Shidai yana gefe yana kallon Sangarta irin ta Inteesar Dakyar ta Saki Daddy ya Fita Sagir ya Rakashi Wajen Mota sukayi ssllama kana ya wuce Shagonsa yana kara mamakin Inteesar afili ya Furta.."Mama zata sha Fama..!
Chapter 18 · 0% Book details