Sashe 30
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Safiya tana ganin Shigowar Munari Ta Sanyaya Murya Tana Fadin"Mommy zan kira ku zuwa Gobe..Ki lallashi Tasleem Plz..! Hajiya Mero Dagachan bangaran ta share Hawayenta Tana Dafa Kan Tasleem Tace"Shikenan Ki kula da kanki Don Allah..! Safiya ta gyada kai Lokaci Daya ta katse kiran bayan ta dago Fuskarta Tana kare Munari kallo ko da bata Taba ganinta a Zahiri ba a kallo Daya zata gane Ita din Jinin Yusuf ce Ballatana Ta taba ganinta a Hoto a Wayar yusuf ya nuna Mata kuma Labarin Munari da Imu har Ta gaji da ji Ta Haddaceshi Saboda Karya ne Yuauf yazo wajenta ko ya kira Wayarta su gama Hira bai ambacesu ba ko bai Fada mata ba ta Tabbata su din sune Jinshkin Mijin nata. Shiyasa ta Saki Fuskarta kamar yadda Itama Munarin ta Washe mata baki Gefen gadon ta Zauna Tana Fadin"Anty Safiya Wlcm to Our House..Ina miki Fatan Alheri..Sunana Maimunatu Abubakar malami ni lilsister din Mijinki ne ya yusuf..Ina Farimcikin Zamowarki Daya Daga Cikin Ahalin gidanmu ayau..! Tafada Lokaci daya Tana mika mata Hannu alamun Musabaha. Safiya Tayi Mirmishi kafin ta mika mata nata Hannu suka Sarke lokaci Daya tana Fadin "Nagode Sosai Munari..Nima ina Farincikin Haduwata Dake sosai..! Munari ta Washe baki kafin tace"Waya Fada miki ana kirana Munari.? Safiya tace"Wazai Fadamin banda Yayanki..? Abakinsa naji Sunanki mai Dadi munarin Abba Auta ko.? Munari taji Dadi sosai Soyayyar Dan"uwanta na Ratsata tace"Yes..Haka kirarin yake..Ina jin Dadin sunan sosai Saboda Abba ne ya Sakamin Sai kakata wacce ta Haifi Abba na Daada Dayake Sunan Autanta su Abba naci Goggo Maimuna..! Safiya tace"Allah Sarki..Duk suna ina..? Ita kakar taku da goggon taku..? Sai Munari taki Cewa sanin ba Huruminta bane safiya na Nazarinta Sai ta Waske Kafin Tace"Yanzu dai ba wannan ba..Naga Abba Sauran Imu bangansa ba ko baya nan ne..?ko shi ne Dazu muna Falo ya Shigo a Fusace ya Shige Daki ya Bugo kofa..? Munari ta kalleta Har Lokacin Suna Rike da Hannun Juna tace"Bansani ba ko ya Dawo..Nima ai yanzu na Shigo Gidan Tun safe ina makaranta Buk nake Karatu Fanni Economics..! Safiya ta jinjina kai kafin Ta gyara Zama Tana Fadin"To dawa kuke barin Abba in kika Tafi Makaranta Yusuf ya Tafi wajen aiki..? Kuma meke Damun Abba ayadda na Fahimta a labarin da Yusuf yake bani kullum yana Daki baya Fita ko"ina ko Bai da Lafiyan Kafa ne..? Da Sauri Munari tace"Lafiyar Kafarsa Kalau..Bashi da lafiya ne Shiyasa Su Yaya yusuf basa yadda ya Fito ko Falo ne..! Safiya Tayi Shuru Tana kallon Munari Kamar Zatayi mgana sai ta fasa aranta Tace kada tace Na dameta da son jin kwakwaf,sai ta Share mganar Ta kara Damke Hannun Munari Tana Fadin"Amtsayina na Bakuwa bani Labarin Ya yusuf da Ya Imu..? Wanne yafi kula dake wa kuma kika Fiso..? Saura kuma Kice My Dear baya Kula Dake sosai sai na ciki Tara..! Munari ta samu abunda take so wanda ZAta ganta Gata tana Hira da Dariya ta saba Rayuwa ita kadai adukan Shekarun da suka Dawo kano da Zama Banda Yaya yusuf bata samun Sakewa da kowa sai kuwa Abba Shi kuma Bashi da lafiya in kwana Biyu ya samu Sauki Zuwa Chan sai abun nashi ya kara Rikicewa Dama Ya Imu bamai sakashi a lissafi ko abaya ba abokin Hirarta bane Shi,Ballatana yanzu da abubuwa suka Lalacemai sosai. Ko amakaranta ya Jamata kunni Kada ta kuskura ta yi wata kawa ko Wani Mutumcin da zai ka ga Har a san Gidansu,Sharudda ya kafamata Sosai kafin ya yarda ma Ya yusuf ya biya Kudi mata kudi a wata Makarantar Kudi ta Rubuta WAEC Da NECO,Da Jamb Har ta samu Gurbin Karatu a Jami"ar Bayero Tunda Lokacin da Suka Baro Lagos Tana SS2 ne,Duk somta da Mutane ta Ware kanta Tun yan ajinsu na Shigemata tana kauce musu Har sukayi banza da ita kowa ya kama kansa bata da Lambar Kowa Itama ba wanda ke da nata sai dai ta karbi Na Class Rep dinsu saboda In wani abu ya taso ta Rika sani Har Group dinsu na Department dinsu na Wasop ya sakata Tana gani ana Hira da Dariya bata da ikon cewa wani abu,sai da ta Shiga tagani in an bada Wani Assigment ko wani Infomartion mai amfani ta Duba Duk yadda taso Rayuwarta Tatafi yadda Hallitar take bazata iya Bijirema Umarnin Yayyinta ba itama Bazata zo ta Fuskanci Wulakaci da Tozarcin da Yayyinta ke Fuskanta kan Gidansu ba. Safiya ce ta Girgiza hannunta ganin Ta Shiga Dogon Tunani Da Sauri ta Dawo Hayyacinta Tayi Saurin Zare Hannunta Tana Goge Ruwan Hawayen da suka Fara kokarin Zubomata Cikin Dariya Dariya ta Fara Fadin"Ai baza ma ki Hada ba Anty Safiya..Abaya Ni yar gatace ta gaba da Baya..yar gatan Abba da Anni yar gata kowa agidanmu..ayanzu kuma Ni yar Gatan Abba ne Duk da bai da Lafiya Dagashi sai Ya yusuf,Bai Hadani da komai ba..Zai iya yin komai Saboda Farincikina Baya iya Runtsawa sai ya Tabbatar da naci Abinci na kwanta sannan zai iya barci..Ya yusuf Mutum ne mai Zuciyar Zinare,mai kirki mai Dattako mai Sanyin Zuciya Dana Hali bashi da Hayaniya ballatana Saurin fushi Zan iya ce Miki ban Taba ganin Fushinsa ba yana da Raunin Zuciya kamar mace Irin Zuciyar Abbanmu garesa suna da Bala"in Sanyin Hali da Dadin Zama ga waanda ya Zauna dasu..Zasu iya Sadaukar da komai Saboda Ahalinsu,ZAsu iya Sadaukar da Dariyansu da Farimcikinsu Saboda Ahalinsu,Anty Safiya bawai ina Kuranta Yaya yusuf bane Domin yana Yayana ba A"a sai Domin Halin Mutum ka Fadeshi bai taba ganina Cikin Damuwa ya barni ba sai ya Tabbatar da Fuskatata cika da Farinciki Shiyasa nake matukar sonsa acikin Zuciya naji Dadi da kika Kasance Abokin Rayuwarsa Anty Safiya Ki Rikemin Yayana Amana ina mai Tabbatar Miki Baza ki Taba yin Nadama ba Domin yana Sonki kuma Shi din Tamkar Misalin mijin Maraniya ce.! Ta karishe Fada Hawaye suna wanke mata Fuska Lokaci Daya tana Riko Hannuwan Safiya wacce itama kalaman Munari suka kara Raunana Nata Zuciyar Dayake Daman a Raunane. Safiya ta Saka Hannu Tana Share ma Munari Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Shii..Ki Daina kuka..Bayan Ya Yusuf yau nima gani Zan ninka Kulawar da yayanki yake Miki Fiye da Sau Goma Nayi Miki alkwarin Zaki Sameni mai kyautatawa da kulawa da abun da Mijina yafi so da kauna.! Sai ga Munari na Dariya da kuka Tace"Da gaske..?Zaki zame mana Haske a wannan gidan Anty Safiya..? Wlh Farinciki ya Dade da Kaura a wannan Gidan Don Allah kizama Sanadiyar Dawomana da Farincikin da muka rasa..! Sai kuka Jikin Safiya ya kara yin Sanyi ta kama Munari ta Rugume tana Lallashinta Lokaci Daya Tana Fadin"Da yardan Allah.ammh sai kin Bani Dukkan Hadin kai! Munari ta Dago Tana Fadin"Insha Allahu ina Tare Dake..! Safiya Tayi Mirmishi Tana Fadin"Yauwa..To maza Share Hawayenki Kuka ya Kare..Bani Labarin Ya imu..?Shi dai Duk da ban Zauna Dashi ba Yusuf na bani Labarinsa yafi ye Fushi da Zuciya ko..? Munari na Share Hawayen tace Cikin Dariya,"Rigimamme kenan.ai Ya imu Dabam yake acikin Gidanmu..Bamai irin Halinsa..Shifa Ya Imu bakomai ke Damunsa ba Baya Shiga Abunda ba Ruwansa Ko kuma yayi shisshigi kan Rayuwar wani yafi Damuwa da kamsa Fiye da kowa abaya..Ya Imu yana da Wuyar Sha"ani ko kema sai kinyi a hankali kin bi a Sannu Zaki iya gane wasu Daga Cikin Hallayarsa,Yana da Murdaddan Halin Da bamai iyamai sai Allah Daya Hallicesa ko Abba sai dai ya Kada kai ya Bisa da Allah ya Shirya Ballatana Ya Yusuf Shi din kaifi Daya ne In yace Abu to baya barci sai ya Tabbatar Dashi Baya Saba mganarsa Mutum ne Dabaya karya,Baya kuma shayi ko Tsoron Fadin mgana koda Za"a Kashesa ne yana Da Dakakkiyar Zuciya irin na Jaruman Maza,Bashi da Fara"a ballatana yawan Dariya Miskiline sosai na Bugawa a ajarida Bashi da Sakewa da Mutane infact ma Baya son Mutane ya Imu yafi jinDadin Rayuwa Shi kadai Fiye da Cikin Mutane ko da yan"uwansa ne Bashi da Sakewa da Mata koda kannensa ne Koda Nice Bashi da Sakewa dani..Tsakanina Dashi ke ina wasa Dake ni..?ni sa"anki ne..?kin Raina mutane ko..? Tashi ki tafi Dakinki ki ba Mutane waje kafin na Sauya Miki Kammani..! Ya tsani Raini Shiyasa Tun yana amsa sunan Imran dinsa Baya Harkan Mata Nifa ko Daidai da Rana Daya bantanajin Yayi Budurwa ba,Ammy nasan a Yadda yake Kyakyawan nan wannan bazai rasa masu Sonshi ba Ni kaina Wasu Hallayar nasa suna Burgeni Barin ma Kaifinsa yana da Zuciya Bakar Zuciyar da in Ta tasomai kowa sai ya Tsorata,bazan Tsaya Misalta Miki ya Imu ba sai dai nace Miki Shi din na Dabam ne da Duk yadda kika ga kai ga Hangenki baki isa ki iya Ganosa ba Duka ba sai dai ki San wanda kika sani Shidin kamar Wahainiya ce kullum Chanza Launi yake..Baya Lallashi sai dai Shi a Lallasheshi bashi da Rauni ko kadan Dakiya garesa da Kafiya In aka Taba wani nashi nan ne Za"a ga waye Ya Imu Bashi da Sakin jiki da Ahalinsa ammh Acikin Kirjinsa yafi kowa sonsu..Na Rantsw har ga Allah ba wanda ya isa ya Dagama Gidanmu yatsa kafin ya Saukr ya Imu bai karyasa ba Salon Soyayyarsa ba irin Takowa bace tashi Salon ta Nuna kwanji ne..! Munari ta karishe Fada Tana Sakin Mirmishi Safiya Tace"Ai nima nagani DAyazo Gidanmu Duk Fadan Abbu Sai da ya Sauraramai..! Munari tace"Haka yake..Bashi da abokai Rayuwar Duniya bata Damesa ba..Baruwansa da kowa Shi kawai Rayuwarsa ya sani shi kadai sai Abokinsa Daya Sagir wanda Mamansa Abba yace ta Rakoki..Shi ne kadai abokin Ya Imu..Shima din abotarsu Wani kaddararran Lamari me Daga Allah..Allah ya Riga ya Hada Jinsu Bayan Kaunar abota akwai Kauna wacce Allah ya Hadata a tsakaninsu Duk yadda Imu yakai ga yakice Sagir bai Yakican mai ba,Dole ya Rabu Dashi zasu hadau suyi Fada kuma Duka Fadan Ya Imu ne ke jansa Shi Mutum ne da in ba kansa ba ko Allah sa ba bamai iyamai ammh Kuma ahakan suke Tare ko Daya bai Nemi Daya Daya zai nemi Daya kuma Dashi da Mahaifiyarsa kadai Muke Mu"amala kuma sune suke Shigowa Gidan nan kai Tsaye Batare da wani Shamaki ba..! Safiya ta jinjina kai kafin Tace"Tabdijam..Wannan matar da zata aureshi nake Taausayamawa..! Munari ta kwashe da Dariya kafin tace"Ai ba Matar da Zata