← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 190

Sashe 45

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

insha Allahu Daganan Mama tatashi Bayan tacema Inteesar abincinta na Kitchen Itama kuma ta Shiga Ciki yin Sallah Inteesar Tayi ma Munari Tayin Cin Abinci sai ta Mike Tana Fadin"Nagode Kawas ki bari in na Sake Dawowa zanci..Yanzu Tafiya Zanyi in ya Imu yaga ban Dawo ba Wlh Zan ci kaniyata ne..! Jin haka yasa Inteesar tamike tace suje ta Rakata,Kayan Hannunta Kadai ta ijiye suka Fice Tunda Mama ta Tada Sallah Tafiya kadan sukayi sai gasu Kofar Gidansu Munari ta Kalli Inteesar Tana Fadin"To kin ga GIDANMU..! Inteesar ta Kalli Gidan Tana Fadin"Nagani Ai nasan Gidan yanzu..Da Zama ya Isheni in bamu Shiga Sch ba sai dai ki ganni..! Munari tace"Shikenan sai na ganki..Bye sai gobe in mun Hadu..! Inteesar tace"Gobe 10am muke da Lecture ki Biyomim mu Tafi tare..ko Kina da mai kai ki ne Kada na Takura Miki..? Munari tace"Yayana ne Daman ke ijiyine in muna Karatun 8am Daganan ya Wuce Office in kuma ya Wuce Haka Dan Sahu nake hawa..Kada ki Damu Zan zo sai mu Tafi Tare..! Inteesar tace"Yauwa..Kawo wayarki na Saka miki Lambata..! Ba Musu Munari ta Daukota Daga Cikon Jaka ta Mikamata ta Saka mata Tana Fadin"Wani Suna Zan saka miki..? Munari tace"Ki saka Besty Intee..! Inteesar Tayi Dariya Tana Fadin"Au..Nima kuwa Da kin je gida ki kirani Zan saka Besty Munira..! Dariya suka saka Gabadaya Daganan sukayi Sallama ganin Maza nata Haraman Zuwa Masallacin Inteesar ta Juya Zuwa Gida Tanajin Wani Farincikin in Tana Tare da Munari Sai take ji kamar Tana Tare da yar"uwanta na jini kamar Nasara,Dayake Daga Munari har Inteesar basu Taba gaanin juna ba Shiyasa bazasu Shaida juna ba sai dai Bond din Jini Dake Tsakaninsu ne yasa Sukejin kamar wani iri a Tsakaninsu hakama ta Bangaran Munari tana jin Intesar Sosai acikin Ranta. Tana Shiga Haraban Gidan suka ci karo da Abba da Imran Harda Ya Yusuf ya Dawo Ganin ya Imu sai da gabanta ya Fadi tana gaishesu Abba ne kadai da Ya Yusuf ya amsa bandashi Daya wani Hade rai yana kallon Gefe. Abba ne ya Kalleta yana Fadin'Munarin Abba ina kika Tsaya yau kin gota Lokacin Dawowarki..? Kafin Tayi mgana Ya yusuf ya Rigata Da Fadin"Ni kaina na Damu yanzu Safiya ke Fadin Shuru bata Dawo ba Har 6:30pm ta wuce..? Yafada Lokaci Daya yana Duba agogon Fata na kamfanin Rado Dake Daure a Tsitsiyan Hannunsa. Da Sauri Munari tace"Ban samu Adaidaita ne da Wuri ba Ya yusuf Shiyasa..! Jin haka yasa Dagashi Har Abba suka Kada kai Ya yusuf yace"Kawai Daga yanzu in na taso da Wuri Zan rika kiran ki naji in kun gama Sai na Biyo na Dauko ki..Kina mace bana so kina Yin Dare a waje..! Kai ta gyada batare da tayi mgana ba ta Mike ta Wuce Sum sum ta wuce Ba Saboda kowa taki Fadan inda ta Tsaya sai Saboda Ya Imu ko kowa zai Fahimeta ban dashi ta Tabbata sai yayi kwallo Da ita bayan ya Fara Sauya mata kammin Dayake ikirarin Tun a Haraban gidan kafin su Shiga Ciki Shiyasa ta Rufama kanta asiri. Cikin Gida ta Shiga su kuma suka Fice koda ta Shiga Safiya tana Shashnta Tana Sallah Domin ta Lekats sai kawai ta Wuce Dakinta Kafin ta Shiga wanka sai da ta Kira Inteesar sai taji bata Dauka ba sai ta Tura mata sako Salam Besty nice..Munari..! Daganan ta ijiye wayar ta Tube ta Shiga Tayi wanka,Ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Ta idar kenan Tana Saka kaya Safiya ta Shigo Tana yi mata Sannu da zuwa Sai da Tagama Saka Kayan suka Fita babban Falo su Abba basu Dawo ba sai da sukayi Isha"i Lokacin Munari taci Abincinta Saboda yunwa Tea kadai ta Kara sha tayi musu Sallama ta Shige Dakinta ta Kwanta tagaji,Ta bar Abba da Ya yuauf da Safiya a Falo Abba da Ya yusuf Hira suke Safiya kuma Tana kallon Imu dai yana Dakinsa yau ko Tea din bai Sha ba Tun bayan Dawowarsu ya Shige Ciki,Sigari Ta Riga ta gama Cikamai Ciki in ji Abba Suna Dariya Shida Yusuf.
Chapter 45 · 0% Book details