Sashe 55
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Lafiyayyan marin da sai da ta Kife ya kuma saka Kafa yayi kwallo da ita ta Fadi chan gefe sai da kanta ya Bugu da kujera ji kake kum,Wanda ta saka Dole Munari ta saki marayan kuka Tana Fadin"Wayyo Allah na Ya Imu don Allah kayi Hakuri..Abba..Ya yusuf Ku Taimakamin..! Take Fadi Tana kuka Abba bai Motsa ba Shima Ransa ya Baci Yusuf ne ya Riko Imran din Cikin bacin rai ganin yana Shirin kara Bin Munari ya Taka da Takalmin kafarsa,Safiya kuma Baya taja Tsoro ya kamata gashi Tana son Isa Wajen Munari Tana Tsoron kada Itama ya Illatata. Ya Rikesa Sosai yana Fadin"Imran Wht is your Problem ne..Abba na maka Mgana ka maidashi Banza..? Me tayi maka kake Dukanta kai baka jin kunyar Dukan mace..? Macen ma Kanwarka Wacce baka da kamarta..? Imran ya Kallesa Idanuwansa Jajir kafin ya Kwace Jikinsa yana Fadin"Ina mgana tana cemin baa Haka ba..?Zan mata karya kenan ko..! Ni ina Wasa da ita ne zata Rika bama Wannan yarinyar Labarin ina Sumar da Mutane..? Yusuf Let me Tell ur wani Abu bana son na Bata ma wani Rai Shiyasa bana shiga Shirgin da ba nawa ba..Nima na Tsani ka batamin Raina Saboda BANA SON RAINA YANA BACI..! Yafada Cikin hargowa Lokaci Daya yana Wani Buga Kafarsa ya Cigaba da Fadin"Zan Cigaba da Dukanta Har sai ta Suma sai taji dadin bada Labarin ina Sumar da Mutane..ina na kara ganinki da wannan Yarinyar sai na Illataki..Nonsesses kawai..! Daga haka kawai ya Daga Kafa ya wuce Fuu zuwa Dakinsa ya Shiga ya Banko Kofa ji kake Bam! Kamar zai Ballata Abba ya Jinjina kai kawai ya kasa cewa komai Yusuf ya Kallah wanda ya Daga Munari Dake ta kuka ya kalli Safiya yana Fadin"Kamata Don Allah..! Da Sauri ta Riketa Tana mata Sannu Cikin Tsausayawa Abba ya Juya yana Fadin"Mu tafi masallaci Yusuf..! Ba Musu yabi bayan Abba suka Fice ita kuma Safiya ta kama Munari zuwa Dakinta sai da suka Shiga ta Rufo Kofar take Fadin"Kema munari me ya aike ki bama Intee wannan Labarin gashinan yaje kunnunsa yanzu..! Munari na kuka Tana Dafe da goshinta Inda Har ya Sumtuma tace"Wlh bansani Ba Anty Safiya..Bansan zai ji Labari ba da ban Fada mata ba..! Safiya tace"To ita ya akayi ma ta gansa Har ta Fadamai..? Munari na Sharan Majina tace"Bazai zama ita ta Fadamai ba..Sai dai in Tayi Zencen da Ya SAgir ne shi kuma Cikin mgana ya Fadamai kuma zai kawo nice..Daman ga Haushin Abunda Intee tamai Duka ya Hada ya Huce akaina Da kuma Haushin kawancen da muka Fara da ita Saboda yamin kashedin kada na yarda nayi kawa da kowa..Anty Safiya Taya zai ce kada nayi kawa ni ba Mutum bace da bana son Farinciki..?ko kuwa shi ba Abokin garesa ba Shi wa ya Takuramai..? Ta Karishe Fada Cikin kuka da Tsausayinta ya kama Safiya ta Rumgumeta ta bata baki DAkyar ta Lallasheta Tayi Shuru,Ta Dauko man Zafi ta Shafa mata agoshinta Bayan ta Sake alwala ta Fice ta barta Tana Kokarin Tada Sallah Itama Shashenta ta Shiga Domin ta gabatar da Sallah aranta Tana Tunanin Duk iya Hasashenta kan Imran ya Wuce Yadda Take Tunani ko take Tsammani. Su Abba basu Dawo ba sai Bayan Sallar Isha"i suna Fitowa Daga masallaci suka ga Imran ya Fito yana Saka Takalmi ya Sauya Kaya Daga Riga da Wando Zuwa Wata Bakar Jallabiya Sagir ne ke mai mgana yayi banza Dashi ya wuce kamar zai Tashi Sama Dashi akayi sallar mangariba Duk da Raka"a Daya ya samu sai ya Rama Sauran ya Tsaya Har akayi Sallar Isha"i yana Sahun baya ne Shiyasa su Abba basu Lura dashi ba. Sagir ne ya gaisa dasu Abba. Abba ya Dafa Kafadansa yana Fadin"Ka Rabu dashi Yau Zuciyar tasa ne tatashi Har gobe da wannan bakar Zuciyar sai wayi gari..! Sagir ya Kada kai yana Fadin Allah ya kyauta da haka sukayi Sallama ya Nufi Cikin gida Duk da ya Damu yana Tunanin kan mganar Daya Fadamai n in bai Kuskure ba komai zai Dawo kan Munari ne Domin zai ce ita ta gayama Inteesar Tuna Haka da yayi ne ya Dafe kansa yana Fadin ya Illahi me na aikata ne..? Nafi kowa sanin Imran in Ransa ya baci kamar Mahaukaci yake..Kada yaje ya Duke yar Mutane fa..!