Sashe 145
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
na gefe Tana kallonta Tana Sharan Hawaye Lokacin da Mami ke kuka Tana Sanar da Hajiya Turai Brr.Kabiru ya Saketa Ashar ta Lailayo ta Sakar mai Dashi da Daadan gabadaya Ta Fara fadin"Yau naga aikin Fulani Daman ance Fulani akwai bakinciki da Hassada da son kai da Wauta da Rashin Lissafi eh lalle naga aikin Fulani kuwa ni Turai..Da Tsohon Daran nan zai sakar mana ke ,gotai Gotai Dake ko kunya Kabiru bai ji ba..? Ai ko bai Darajaki ya Ragamiki don Soyayyar da kika Nunamai ba ya Duba Wadanan Zaratan ya'yan da kuka Haifa in mu bazai ga Girman mu ba..! Tafada Tana kumfar baki Mami ma sai kuka take abun ya Daketa ita kanta Hajiya Turan fa Fada ne kawai ammh Ina Zakaso D'anka da girmansa Shekaru sun ja a kore maka shi awannan Lokacin ai abun kunya ne sosai kuma ba wasu iyaye da zasu so haka ita kanta Kabirun Wlh ya bata Mamaki bata Taba Zaton zai iya Furta kalmar Saki Ga Ma"u ba Tun Daga yanayin Zamantakewarsu da yanayin Zaman auran nasu. Justice Tafida ta Fadama Halin da ake Ciki Daman yana Zaune ne yana kallon Labarai A tashar CNN,kai kawai ya gyada kafin yace"Ki Fadamata ta shirya Direba zai zo ya Dauketa..Tunda bataji mganata ba Har takai su ga haka Is ok..Kowa yayi yadda yake so..! Daga haka ya cigaba da Kallonsa Kafin Lokaci Daya yana Danna Wayarsa zai Kira Direban da zai Dauko Asma"u. Hajiya Turai ta Kallesa kafin tace"Ranka ya Dade ayi haka..?Gotai gotai da Ma"u sai ta dawo gida Zaman Miji ya saketa..? Bai mata mgana ba sai da ya gama Waya Da Direban kana ya Dago kansa bayan ya ijiye wayar yana Fadin"Sai ta zauna bayan yace tabarmai gidansa Turai..?Abunda ta Zabama kanta kenan bazan hanata ba ai ba yarinya bace She know What is Right and Wrong..Katon gidane ina dashi akwai Dakuna Kowa ya yanke ma kansa Irin Abunda ta Zamar ma kanta bazan hanasa Zama agidana ba kowa nada Righat dinsa so banga abun Damuwa ba..! Daga haka ya dauke kansa ya Cigaba da kallonsa Ai bata kara mgana ba ta Daga Waya ta Kira Mami Asma"u tace ta Shirya ga Justice nan ya Turo Direba ya Dauketa daga haka ka Katse Kiran. Mami Asma"u na kuka Umaima nayi Baffa Kabiru bai san sunayi ba yana Cikin Dakinsa Bai kuma yi Nadamar Abunda ya aikata ba.. Yana Daga Tsaye wajen Window yana kallon Haraban gidan Daga waje Mota ta Shigo Daga lambar Motar ya gane Daga Gidan Justice ne karamin Tsaki yaja yana jin karin wani Takaichi Sam dai ba Tsari ace kana Babba da iliminka da komai kace Bazaka Tsawata ma yaranka ba sai dai kace su ba yara bane suna da Rigaht din da Zasuyi abunda suka ga Dama,Daman fa In Boko yayi yawa wani Lokacin Har Kafirta Mutun yana yi. Agaban Idonsa Mami Ta Fito Umaima na Riketa Tana kuka itama kukan take Tana Dauke da Karamar akwatinta,Yana Tsaye yana jiran yaga koda Umaiman zata tafi sai yaga ta shiga Mota Direba yaja sun Fice Daga Gidan Umaima ta Durkushe nan tana kuka,Sai ta bashi Tsausayi Dalilinta yasa ya Sauko kasa ya Fita ya Rarrasota ya Riko Hannunta yakai ta Har Dakinta Fadi take "Plz Dad ka Dawo da Mami kada bari tatafi..! Kai kawai ya gyadamata ammh acikin Ransa ya Kudira in har Asma"u bata gyara ba To ya yarda su Rabu Rabuwa Ta Har Abada. Sai da yaga ta Daina kuka kana ya bar Dakin ya koma Dakinsa yana Fita ta Mike wayarta ta Kunna ta shiga Neman Layin Khamis ammh bata Samesa ba Wayarsa tana kashe. Abunda bata sani ba Khamis ya Sauke Layinsa da kowa ya san sa dashi ya Siya wani ya Dora Tun bayan da isa wajen aiki ya Kira Mami da Dad ya Fada musu ya sauka Daganan ya Sauke Layin ya bama yanmata gari da ma"abota son Holewa kara shiga Rayuwarsa ya Bude ma Club da Mashaya Bakin Aljihunsa aranar Daya koma Duk Saboda ya manta Da Inteesar Har Giya yanzu yana sha da kayan Maye wanda ke matar dashi komai Na Duniya da Duk wani bacin rai. Ganin bata Samesa ba sai ta Kira Sajida itama Dayake ba barcin Wuri take ba kuka ma take kwance Tanayi Dayake su biyu ne Adakin ita da Wata Jenefer ba musulma bace itama iyayanta Wasu ne,Ta Girgiza sanda Taji mganar Umaima wai Dad ya Saki Mami har ta tafi gida duk da abun ya Shigeta ammh tafi Tsausayama Dad akan Mami ita ai ta Chanchanci koma Menene. Jin tace mata bata samu Khamis a waya ba yasa tace ta Kira Baffa Mustapaha ta Fadamai in tana da Lambarsa Umaiman tace tana dashi bari ta Kirasa,Sajida na son tace mata ta bari sai gobe da Safe Dare yayi sai dai bata Saurareta ba Ta kashe Wayar Saboda Hankalinta ba yana Kwance bane. Sajida taji Rauninta ya Karu Tashi Tayi ta Shiga Tiolet chan ta Saki Kukanta son Ranta tanayi Tana Rufe bakinta kada tatashi Jennefer Dake Barcinta Bata da wata Damuwa,Mami Duk ita ce Silan komai yanzu kuma ta kara Bullo da wata Rigima har takai ga Dad ya Saketa ai Allah ya kara mata Ita sonkanta komai Mami zatayi sai ta Fara Duba kanta kafin ta Fara Duba wani Shiyasa taki komawa Gida bata so taga Bakinciki Sai gashi Abunda ta Guda ya Faru Abunda basu Taba gani ba ko Fada ne na Chachar Baki Tsakanin Mami da Dad har Fata take in Tayi aure Zata gina Gidan auranta yadda Mami da Dad suka gina nasu gashi yanzu komai ya kare. Sai da tayi kukan ya isheta kana ta Hakura jin kirjinta na mata suya kanta ya Fara sara mata yasa ta Wamko Fuskarta ta Fito Tana Dafa Bango Jiri take gani saboda Tsabar Tashin Hankalin Datake ciki Tazo ta Fada kan katifarta yaraf kamar kayan Wanki