← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 190

Sashe 42

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Safiya ta Murmusa Tana Fadin"Mommy wa kika Taba ganin ya Fado Daga sama bashi Da Dangi? Suna da Ahali da Dangi irin na Kowa Mommy kawai yanayi ne yasa kika gansu kuma Mganar Abba..,karya ne Mahaukaci bane Wlh Sharri ne..!Nan da nan ta Fara bama Mommy Labarin da Yusuf ya bata ba Domin komai ba sai Domin Hankalin Mommy ya kwanta,Agurguje ta gayamata komai ta Karishe da Fadin"Mommy Kinsan Rashin Uwa a gida Babban Gibi ne..Su kuma Rashin Uwa sukayi da yan"uwa Har Uku yaya zasu Fuskanci Wannan Rashin..? Abba kuma Yayi Rashin Mata ce Uwar yayansa..Kuma yayi Rashin Ya"yansa Har guda uku alokaci Daya..Yaya kike ganin Haka Amtsayin in ya Faru Dake Mommy..? Sannan kuma yan"uwansa suka ki Fahimtarsa Ballataa su Taimakesa kan Halin Dayake Ciki..!
Mommy ta Share kwallah Saboda Tsausayi tace"Allah Sarki ashe Hadarin Jirgin Daya kashe Mutane dayawa din na harda Mahaifiyarsu da yan"uwansu aciki..?Abun Tsausayi Allah ya jikanasu da Rahma..Wlh naga Kokarin yaran..Allah yayi miki albarka Safiya Yanzu Hankalina ya kwanta na Tabbata Mahaifinki bai kai Hannun banza kina Hannu nagari..!
Ina alfahari Dake Ki Cigaba da Abubuwan Dakike,Insha Allah ke ce Haske acikin Gidansu da yardan Allah..!
Rumgume Mommy tayi Tana Share mata Hawaye,Sun Dade aciki suna Tattaunawa sai da Yusuf ya kirata yace su Fito su tafi sun bar Abba Shi Kadai,nan ne ma Mommy ke mata Mganar Kayan Daki Take gayamta Yusuf yace shi Zai siya komai kawai abunda take Bukata Turaran TuraraGida sai na kaya,Sai abubuwan da ba"a rasa Mommy tace Insha Allahu zata kira Anty Saratu Zasu Shiga Kasuwa Zasu siyomata komai Sai Tajita,kafin suyi sallama sai ta bata leda guda Cike da kayan gyaran Jiki,Tace abunda bata gane ba ta Kirata Taji Takaichi yarda takai yarta Baatare da wani gyara ba Ammh ko Yanzu Lokaci bai kure mata ba Saratu Zata Hada mata komai Tunda itama Tana Taba Sana"ar kayan gyaran Mata..
Koda suka Fito Tasleem da Munari sun Gama Hadamata Duka kayanta Kadan suka bari akwati Uku suka Cikata Harda su Takalma da Takardunta na makaranta sai Littafan addu"o'inta,da Sauran littafanta na Karatu Novels na Turanci dana Hausa,Sakawa su kawai akayi a Mota Mommy da zasu Tafi Tayi ma Yusuf Gaisuwan Rashin da sukayi bai yi mamaki ba Sanin Safiya kila ta gayamata yaji Dadi sosai ya amsa yana Godiya Munari da Tasleen suka yi Sharing din Cantact din juna,Tace Sai tazo,Safiya tace ta na nan tana Jiranta suka Tafi suna Daga musu Hannu,Bayan Safiya ta bar Sallahun Agaidata mata Alhaji Alhassan in ya Dawo Mommy aranta taji bazata Fadamai ba Kuma Zata kwabi Tasleem So take sai ya Girbi Abunda ya aikata da kansa Tukunnah.

Washegari Ta kama Lahadi ne Tun Safe Yusuf yace Safiya ta Shirya Zasu je ta zabi Funutures,da Kayan sawa,Bata iya cewa komai ba Domin Ta Lura Yusuf baya son gaddama,yau Munari ce tayi aikin Gidan,Tace Safiya Ta Huta Tun Safe tana Daki Gaida Abba kadai ta Fita,ta Dawo Daki ta Kwanta,Dole tatashi ta Shirya Bayan ta Shirya ne tace Tana so suje da Munari Ta tayata Zabe ya bata Rai yace Shima ai ya iya Zabe Dariya Kawai Tayi ta bar mganar,Doguwar Rigar Wata atamfarta ta Saka Mai kalan Green sai tayi amfani da Bakin Mayafi da bakar Jaka da Takalmi,Shima Yusuf din Shaddarsa Mai Duhu ce,Sun Fito Cikin Shirin Fita Suka iske Abba Falo suna Kallon Arewa24 shida Munari ganinsu sun Fito a Shirye yasa Munari take Tambayan ina Zasu je..? Abba ya kwabeta yace ina Ruwanta Tsakanin Miji da mata sai ta bata rai Tana Tura baki Abba da Yusuf suna Dariya Sanin shi yasan Inda zasu je.
Sallama sukayi ma Abba ya Rakasu da adawo Lafiya,
Wani Kamfanin saida Kayan Funuture suka Fara zuwa Tare da Safiya suka Zabi Kalan Bedroom da Falo,Dayan Bedroom din Dazai zama nasu Brwon and White sukace a Hada musu komai ,Dayan kuma da Zai Zama ko na Baki suka Hada Black and White,Sai Falo suka Hada Blue and Ash..Komai sai da aka Hada musu Harda su Cafet,kayan kallo,Sun siya Fridge Da wasu kanunun kayan Kitchen Tunda akwai karamin Kitchen a Ashashen,Ta Bank ya Tura Musu Kudinsu ya bada addreess Suka kuma Jadadda musu kayansu zai isa Kafin Su isa Gida Tare da Ma"aikatansu da zasu Hada komai sukayi musu godiya Daganan suka Shiga Kasuwa Safiya ta Zabi Kaya kama Daga less da atamfofi da Materials,Sai kayan Barci Da mayafi da Hijabi da Takalma bada yawa ya Siya mata saboda bai da kudi yace Sai sun kara Dawowa..
Suna Shagon Munari ta Kira Yusuf Take gayamai ga Masu kayan sun kawo nan yace Ta Nuna musu Shashen Dake kusa da Dakinta anan Zasu Jera Kayan Ta tayasu a Share Dakin,Munari tace ai Ta riga ta Share Dakin Bayan Fitansu Tayi Mopping Abba yace tagyara,Yusuf yace Shikenan ta Nuna musu su Jera komai suma gasunan zuwa..
Toh basu Dawo da Wuri ba Tunda sai da suka Biya suka kai Dinki Wajen Telan Da Safiya take kai Dinki Tun Tana Gida Kana suka Dawo sun Iske Tuni har kamfanin Tagama Hada komai sun Tafi..
Waje yayi matukar kyau sosai Munari ta Tayata dashi kanshi Yuauf din suka Kara gyara ko"ina Har Tv aranar aka Hadashi,Munari sai santi take Ita ta Tayata suka Kwaso kayansu Daga chan dakin suka Maidasu nan,Har Abba sai da yazo ya gani ya saka albaeka Imran ne dai bai Shigo ba,Daga bakin Koridin kawai ya Tsaya Daganan yayi Waje Shagon Sagir yaje Domin yanzu Chan yake Wuninsa,Tun Mganar nan da sukayi da Sagir na Zai bashi Sana"a Shikenan ya addabeshi Da kira wai yana Jiransa Dole yake zuwa ba Domin komai ba,Sai Saboda Sagir bai zai iya Ture alfarmansa ba, ammh ba wai Domin Ya koyi Dinki kamar yadda Sagir din yake Bukata Shi Aikinsa Daya ne aikin Banki ya Zauna kan kujera tana Juyawa dashi Lokaci Daya yana Sarrafa Computer shi aikinsa akwakwalwa yake,Bazai iya yima Sagir din gaddama ba Shiyasa yake Zuwa Sai dai Fara Zuwansa Shagon ya Takurama Yaran shagon basu da Damar Sakewa ko Hira ko Dariya in Har Imran na Shagon ba umh ba Umh ne ko Mganar Rada kayi sai yace ka Dameshi ka Fita yanzu yar Yar wakar ma da suke kunna Saboda Nishadin Dinki ba wannan Damar domin Ranar da suka Kunna Mp3 Din gabadaya Imran ya Rotsata da kasa ta Fashe,Tundaga lokacin Shagon ya Zama sai a Hankali,Yaran Sagir din Haushin Imran suke ji sai dai ba Halin su Furta Shi kanshi Ogan zai iya Bata Musu rai kuma ba komai yake yi ba
Illah ya Zauna Kawai yana bin Wuri Daya da kallo in yaji Nishadinsa ya Busa Sigari ko baka san Warinta baka isa ka Fita ba kuma baka isa ka Toshe Hanci ba Dole ka Shaki Hayakinta.
Shi Kanshi Sagir din yayi Nadaman Gayatton Imran din Domin ba yaransa Kadai ba Hatta shi ya Hana mai Rawan gaban hantsi ko Dinki Costumer suka kawomai Cinikayya sai dai su Fita Waje,Indai Imran na Shagon bayason Hayaniya da Takura,Sai dai ba yadda Zai yi Dashi Fada ne Kullum Kaca kaca suke Rabuwa,Bai kuma Hana gobe in Sagir yaji Imran din Shuru ya Kirasa
Har kuma zuwa yau bai kara ganin Inteesar ba,Har ma ya manta da Babunta.

******

*Kaduna..*
Da misalin karfe 8:00pm na Dare.
Chapter 42 · 0% Book details