Sashe 82
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yau itama bataje ba tasan gajiya ne na makaranta sai dai zuwa gobe zasu Hadu.. Tana ganinsa tayi wanka ta gyara Jikinta tazo ta saka kayan Barci ta kwanta sai dai mai Tun tana ganin abun wasa wasa har ya Fice Tunaninta ta Fara rike ciki tana wayo Wayyo Allanta Tun tana ciki a Hankali har ya fito Fili Mama Dake falo taji Da Sauri ta shigo Ciki ganin Inteesar kan gado ahannunta kan cikinta Tana Birgima tana kuka Lokaci Daya sai ta Rude ta isa gareta ta Tarairayota Tana Sallami Cikin Kaduwa take fadin"Na shiga ni Amina Maryama meke damumki..? Meya sameki..? Inteesar na kuka Hannunta kan cikinta Tace"Mama ci..Cikina..marana ciwo..! Hankalin Mama ya tashi ta Rude Tana Fadin"Daman kina ciwon mara ne in zaki jini..! Kai Inteesar ta Dagamata Bata samu bakin mgana ba.. Mama ta rasa yadda zatayi Fita falo tayi ta Kira Sagir a waya Tana Fadamai Halin da ake ciki shi kuma Lokacin suna Tare da Imran awaje sai da yagama wayar ne yake fadamai Inteesar ce ba Lafiya Tuni yaji Hankalinsa ya tashi kamar yabi bayan Sagir din sai kuma ya kasa,Ya fara Safa da marwa a waje yana Jiran Fitowarsa shi kuma Sagir yana Shiga ganin Halin da Inteesar ke ciki yasa yace Mama ta sakamata Hijabi bari ya Sami adaidaita su tafi asibiti ta amsa mai da Sauri ta Bude Akwatin Inteesar ta dauko mata Wani jan hijabinta ta kamata ta sakamata. Shi kuma Sagir yadda yaga Imran ya Rude ne ya kara bashi mamaki bai ma Tsaya yaji wata mgana ba ya fara Tambayansa ya jikinta..?shi kuma ya Fadamai tana jin jiki Adaidaita zai sami su tafi asibiti da Mama kai Tsaye Imran yace basai Mama taje ba Bari su samo adaidaitan sai su kaita bai iya cewa komai ba Sagir sukaje bakin Titi suka sami mai Adaidaita zuwa Kofar gidansu Sagir din kana ya shiga cikin gidan ya Iske Mama ta shirya tana Jiransa Lokacin Inteesar din taji Sauki ta Daina Rike cikin,Nan ya fadama Mama ya samo mai adaidatan yana Waje ammh Imran yace basai taje ba Shi zai rakata su kaita tare . Mama tace taya zata barta su tafi da ita dukkansu fa Maza ne sai dai suje tare,Inteesar na jin haka tace ma Mama ta zauna saboda Dare zata iya Zuwa Insha Allahu jin haka yasa Mama bataso ba ta barsu suka tafi har Waje ta Rako Inteesar tana Rike da Hannunta,Mama dai taga Dare yayi kuma Inteesar mace ce Sagir Namiji ne Imran ma haka sai kawai ta ce bari ta Rufe gidan tare zasu tafi ba wanda yace mata wani abu.. Tunda Mama ta Rikota yake kallonta Bata ma iya Tsayuwa sai da ta Jingina da Bango Tana Halin ciwo ne ammh Ganinsa yasa taji wani Sanyi Mama ta kulle gidan ta Kamata suka Nufi adaidaita,Mama da Inteesar suka Shiga Baya Sagir da zai shiga bayan sai Imran yayi Sauri ya Shige shi kuma sai ya zauna agaban adaidaita Wani asibitin kudi Sagir yace mai adaidaitan yakaisu. Inteesar tana kan Kafafun Mama ne da Farko ammh da Ciwo yayi ciwo ta fara Mirginawa tana Rike da Cikinta Tana kuka tana Fadin wayyo Allah zata Mutu Tsausayinta ya kamasu Mama ta kamata ta fashe da kuka Tana fadin mai adaidaita ya yi sauri Imran kuwa yana Zaune ne kamar ya Ciro ciwon jikinta ya maida akansa Rabin jikinta yana jikinsa ne,domin ta kasa Zama waje Daya Hannunta Guda ya Rike gam yana mata addu"an samun Sauki acikin Ransa. Tana Halin ciwo ammh Rikons na Dabam ne Idanuwanta cike da Hawaye take kallonsa Cikin so da kauna mai Zafin data shigets bata sani ba... Koda suka karisa asibitin ta galabaita Suna zuwa aka amsheta ganin yanayinta Direct gado aka bata ma,aka sakamata Drip da allurai sai barci Lokacin ta samu sauki ba kamar yadda suka zoba,Likitan yace sai dai ta kwana sai zuwa gobe sai su sallameta agaban Mama da Sagir da Imran yayi ma Mama bayanin ciwon Mara ne ya Sarketa mai Tsanani In Jinin ya Zuba sosai zuwa gobe zataji Dama,ammh ya mata alluran zuwa Gobe in ta Farka zata wartsake. Dole Mama ta zauna ta kwana da ita Sagir da Imran sai 11pm suka koma Gida,Sagir ya Tsaya gidansu Imran ya wuce gida koda yakoma Abba da Ya yusuf basu iya Runtsawa ba Saboda susan baya taba kaiwa Dare kuma suna ta Kiran wayarsa bai Dauka ba Shi kuma yaga Kiran sai dai lokacin suna asibiti ne. Yana Dawowa Yusuf ya faramai Tambayan ina yaje..? Bai iya karya ba kai tsaye ya fada musu Inteesar suka kai asibiti bata Lafiya sai jikinsu yayi sanyi sosai Suka Tambayesa ya Jikinta..? Yace taji sauki tana chan asibitin Daganan ya shige daki Baida wata Natsuwa bai yi wani barcin Kirki ba sosai saboda Zullumi. Washegari Munari taji labari Hankalinta ya tashi ita da Anty Safiya suka tafi asibitin Da ya yusuf harda Abba koda sukaje Inteesar ta farka Taji Sauki sun iske Sagir yazo da ruwan da Zafi da kayan Tea Mama ta taimaka Inteesar ta wanke baki tana bata Tea. Hankalin Munari ya kwanta saboda Taga Inteesar tasamu sauki Mama tace likita yace anjuma zasu koma gida tunda taji Sauki,Imran yaki zuwa asibitin tunda yaji suna chan,to suna ma asibitin aka sallameta sai Yusuf ya kawosu zuwa Gida kana ya koma ya Dauko Abba da Sagir. Munari nan ta wuni gidan Mama tana kula da inteesar wacce taji Sauki Sosai Shiyasa tace ma mama kada ta Fadama su Daddy tasan Halinsa yanzu Hankalinsa zai tashi,Tana asibiti yana ta Kira mama ta Dauka Tace mai sun shiga makaranta ta bar Wayar agida,Sai davta dawo ta Kirashi Jin Lafiyanta kalau yasa Hankalinsa ya kwanta. Imran Tunda yaji an sallamo Inteesar sai hankalinsa ya kwanta bai Je ya Dubata ba sai dai ya kirata a waya yayi mata sannu da jiki yace ta Rika shan ngani ita duk kunya ya kamata Saboda kowa yasan Mtsalanta.. Monday bata samu zuwa makaranta ba sai Munari ne ta leka sai Ranar Talata data samu sauki sosai ta shirya suka Tafi tare. Ranar alhamis da suka tashi makaranta basu dawo gida ba gidan Ya Sadam suka sauka gaida Waleeda Data ke ta Zazzabi sunyi waya da Aneesan take fadamata sun iske taji Sauki waleedan har tana wasanta. Sunyi sallar la"asar sunci Abinci Daman koda suka zo Sadam baya Gida suna Shirin Tafiya sai gashi yazo Aneesa ta dinga Kiransa ta mtsamai sai yazo yaga Munari. Yau ta kara tabbatar ma kanta Munari ce ta Hoton nan saboda ta kara Duba Hoton wayar Sadam,Shine dai bai ganta ba saboda wayar nan tata bata tashi ba wata ya siya mata Shiyasa bai samu ganin Hoton ba,Daman Waleedan taji sauki ita Aneesan abun na Ranta ne yasa ta mtsa sai Inteesar din tazo ita da munarin don Sadam ya ganta da idanuwansa. Tabbas Shima daya ganta Sai da yayi Shock,ita kanta Munarin taji wani iri Data gansa,Sama sama suka gaisa dasu yaja Hannun Aneesa zuwa Cikin Dakinsu. Sai da suka Turo kofa kana ya Saketa Cikin Sauri tace"Kaima ka ga..! Bai bari ta karisa ba ya Fiddo da wayarsa yana Fadin"Aneesa kila Wahala ce tazo karshe..Tabbas wannan yarinyar jininmu ce..!. Yafada yana Binciko Hoton sai gashi ya gani Daidai Munari yayi Zooming yana nuna ma Aneesa lokaci Daya yana Fadin"Indai kuwa ba itace bace suna mugun kama..! Aneesa tace"nifa inaji ajikina itace..Ka duba kaga kammaninta duk da bata kai haka alokacin ba kamminta bai bace ba..! Sadam ya gyada kai yana Fadin"Meye sunanta..? Aneesa tace"Maimunatu..Suna Kiranta Munari..! Ido ya waro yana Fadin"kai..Kin manta Daman Daada tace Karamarsu ita ce taci sunan Mommy..Ina da kyakyawan Zato yarinyar Diyar Kawu Malami ne..! Aneesa tace"Nima ina da wannan Tabbacin Tun ranar dana fara ganinta..! Kansa ya dafe yana Fadin"Ina ne gidansu..? Kenan suna garin kano ba wanda ya sani..! Aneesa tace"Bansan gidan ba Inteesaar tace kusa da inda take zaune ne..! Wayarsa na Hannunsa yace"jeki falo ki Tsaida mun su bari na kira Sa"id a waya muyi mgana..! Tana Kokarin Fita tace"Shi kadai zaka Kirafa..Ka mu kira mu fada yazo ba Haka bane..! Kai ya gyada mata yana Fadin"Nasan Abunda nake yi Aneesa..! Daga haka ta Fice ta barsa yana Kiran Wayar Sa"id kira Daya cikin na Biyu ya Daga kiran ko sallamsa Sadam bai amsa ba ya Shiga Rattafamai abunda ke Faruwa. Yana zaune a office ne sai da ya Mike Zaune cikin Firgici yace"Sadam kada ku bari ta subuce muku.Tunda kuka Tabbatar da kammaninta da sunanta am Very sure itace.! Sadam yace"Nima ina Tunanin haka..ammh yanzu ya kake ganin za"ayi..? Sa"id yace"Ka kira su Kawu ne..? Sadam yace"Ba wanda na kira sai kai..! Da sauri yace"Yauwa..kada ka fadama kowa yanzu kada kabari su tafi su kadai ka Tsaida komai ka kaisu kada kayi sanya kasan yadda Zakayi ka Shiga Har cikin gidan nasu domin ka Tabbatar da abunda muke zato..! Sadam yace"Shikenan yanzu daman koda Aneesa ta Kirani zasu tafi..Bari na fita nace zan kaisu gida..! Sa"id yace"Good..Yadda ake ciki ina Jiranka sai ka kirani..! Daga haka suka yanke kiram Jikinsa na rawa ya Fice Saboda Rudewa Cikin Bedroom din ya manta da key din Motar sai da Aneesa ta shiga ta Daukomai nan yace shi da Aneensa da yara zasu kai su domin suga inda Inteesar ke zaune. Ba wani bata Lokaci Aneesa ta Sako mayafinta,waleeda na Hannun Munari Inteesar ta riko ma Waleed hannun suka Fice ta kulle kofar Falonta. Inteesar da Munari da yaran suna Baya su kuma suna gaba Sadam yana Driving yana kara kallon Hoton nan na wayarsa yana kara Kallon Munari ta Madubin Motarsa Har sai da ta Fara tsarguwa Tasbihi kawai yake acikin Ransa domin ya gama Tabbatarwa wannan itace Maimunatu diyar kawu Malami. Sa"id sai kiransa yake bai dauka ba Sai dai ya Turamai sakon suna Hanya ne basu isa ba,In sun isa komai kenan zai kirasa. Sun shigo gadan kaya Sadam ya Juya yana kallon Inteesar yana Fadin"Bari mu fara kai kawarki gida mu shiga mu gaisa da mahaifinta sai mudawo mu shiga inda kike zaune agaisa kafin mu wuce..! Inteesar tace"To ya Sadam..! Munari kuwa haka kurum taji gabanta na Faduwa kwata kwata bata yarda da zuwa gidansu ba sai dai ta kasa cewa komai. Tafe