Sashe 112
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
kara Tabata sai namai Abunda yafi wannan Sakarai kawai..! Yafada yana cije bakinsa Cikin bayyana yadda Ransa ke kuna. Sai kowa ya koma Binsa da kallo Umma Tayi kasake tana kallonsa Ranta yayi mata Fari domin da Farko Ranta ya baci yadda Mami Asma"u take nuna bakomai bane Abunda Khamis din ya aikata Hakama Daddy sai da ya Murmusa Abba zai yi mgana Daddy ya hanasa Domin kalaman Imran mganace mai kyau kuma yaji Dadinta Inteeear y'ace mafi soyuwa gareta Bazai so wani yaci Zarafinta ba ya Tabbata Indai Tana da Dan"uwa irin Imran bai mai iya cin Zarafinta bai Rama mata ba Hakama Ya Basheer aransa yana Mamakin Wasu Mutane meye na rike mata hannu? Har yana nuna ba wani abu ai koda take yar"uwansa hakan bai dace ba. Sajida kuwa kallon Imran take shi baima san da ita ba,Tana Fadin acikin Zuciyarta Meyasa shi ya Rike ma Inteesar hannu jiya..?Shi din Muharraminta ne inda zata iya da sai Tayi mai wannan Tambayar sai dai bata da wannan kwarin gwiwan. Daada ita kanta taji Dadin mganar Imran Dole ta hana Mami Asma"u mgana Tayi ma Khamis fadan Abunda yayi bai kamata ba kansa na kasa yace"Daada nifa bada wata Manufa nayi hakan ba..Ina son Inteesar..Kuma neman Damarta nakeyi ta amince na gabatar da mganarmu wajenku A tsaida mana Lokacin Aure..! Gabadaya sai Falon ya Dau Shuru Mami Asma"u baki ta saki Cikin Takaichi Tana kallon Khamis Baffa Kabiru baice komai ba Domin kansa ya Kulle,Abba ya kalli Daddy shima ya kallesa Umma ma ta Dago Tana kallon Daddy domin taga yaya ya karbi mganar sai dai Inteesar ta bata amsa Domin Cikin kuka ta Bude baki tace bata son Khamis kuma bazata auresa ba Daddy ne ya tsawarta mata abunda bai Taba mata ba Tsawa Dole tayi shuru ta koma Tana sheshhekan kuka. Daada ta Dade batace komai ba Sai Daga Karshe tace Khamis ya Nemi so wajen Inteesar in ta amince su basu da Mtsala saboda acikin Ranta Taana Tunanin kada ta karayin kuskuran da tayi yau dinnan na Hada Auran Imran da Sajida Saboda a abubuwa su Daidaita sai dai Tun Daga jiya zuwa yau abubuwa suna Faruwa marasa Dadi wanda suka sata ta Fara Tunanin anya batayi kuskuran Hada wannan auran ba..?Tana ganin kamar wasu abubuwan marasa Dadi zasu kara Faruwa nan gaba Shiyasa ta ce Khamis ya nemi Yarda Daga Wajen Inteesar in haka ta Faru zata fi kowa jin Dadin Jikokinta sun hada kansu. Baffa Kabiru ya mike ya nemi Izinin Daada na komawa bakin aiki gobe tace ta bama Kowa Damar tafiya gobe in Allah ya kaimu sannan mganar Sajida da Imran kuma wannan yana Wuyan Imran din. Mami Asma"u ta Bude baki tayi mganar Karatun yarta Tana Fadin bamai yanke ma yarta Karatu Daada tace Ai ba wanda yace zai yankemata Duka wadannan Tsaran Tsaran za"ayisu Daga baya. Daddy ya mike yace Sati mai zuwa sun yi mgana da Daddy zasu je Lagos chan gidan da suka baro dashi da Yusuf da Imran din sannan zai Tura Cv dinsa anan Jami"ar Bayero Ko Allah zai sa za"a Dace Tunda Abba ya Nuna yafi son Zaman kano Fiye da Lagos.kowa yayi na"am da mganar Daddy saboda Abba da Sauransa Tabbas Jami"a zata amfana da iliminsa Ita da Dalibai. Kana Daga Karshe Daddy yace Imram ma ya kawo Takardunsa yana da wani aboki Dake aiki a First bank nan Resshen kano kuma Manager ne insha Allahu komai zai yi Daidai agaban kowa da kowa nan take Imran yace shi bayaso bazai yi aiki kuma baya Bukatar Taimakom kowa Sai da Abba ya Daka mai Tsawa yace kada ya kara Mgana Dole yayi shuru. Daada taji Dadin mganar Daddy ta Dinga sakamai albarka Mami Asma"u sai Hararansa take gani take duk wannan abubuwan Dayake yi na Munafunci ne,Ta kalli mijinta Dayayi Shuru bai ce komai ba ita hakan yayi mata Daidai Kada ya ce komai Suje su karata,Gabadaya zuwansu Dukku ba Alheri bane a wajenta Gabadaya Ranta yana bace ne,Allah Allah take Su bar Dukku kamar tana kan kaya. Daada bata yarda Taron nan ya Watse ba sai da Ta Saka Khamis da Imran suka Nemi yafiyan juna Bayan tayi ma Imran Fadan Kai ma Khamis hannu Da yayi har suka Fara kokawa ta saka Sunyi musabaha da junansu Azuciyar khamis yaji komai ya wuce ammh banda Imran Da abun ke cikin Ransa. Koda Taron ya tashi Zuciyar kowa ba Dadi,Inteesar da su munari suka Kule Cikin Dakin duk Tambayan duniyan nan sunyi ma Inteesar taki yadda ta Fada musu komai Dole suka kyaleta. Mami Asma"u kuwa ita da ya"yanta Tayi ta ma Khamis Fada kamar ta Dakesa sai da Baffa Kabiru ya tsawarta mata kana tyi shuru Sajida na gefe ita da Umaima Mami Asma"u ta Umarce su da su hada kayansu gobe da Sassafe zasu Dauki Hanyar Abuja Har garin Allah ya waye Zuciyiyon kowa ba Dadi suna ta shirin komawa Inda suka Fito,Mami Asma"u da ya"yanta kamar suna kan kaya ko Breakafsat bata yarda sun Tsaya sunyi ba Ta mtsama Baffa Kabiru yayi sallama da Daada da Sauran yan"uwansa suka mika Hanya ko Sajida da Daada tace ta bari su gana da Imran bata bari ba ta Tarata suka Shige Mota sai da suka bar Dukku Taji ta Samu natsuwa kadan. Daga Su Mami Asma"u Sai Inna Maimunatu ita da ya"yanta suka Wuce Bauchi,Sai Hamidan Inna Bintalo itama ta wuce katsina Sai Sa"id mutanen Dutse suma suka Dauki Hanya da Hafsah da suka yi kamar suyi kuka ita da Munari da inteesar Su Abba ne kusan karshen Tafiya Domin sai da Daddy daya Basheer da Umma suka mika bayan sun bar musu Inteesar zasu koma kano da ita saboda makaranta. Suna wucewa suma sukayi Shirin Tafiya Imran dai Tun Abunda ya Faru jiya bai kara ma kowa mgana ba kamar Wanda aka Dinkemai baki Sagir har gaya gaji damai mgana ya kyalesa Kowa yayi sallama da yan"uwa banda shi,Ko Daada bai ma Sallama ba gani yake duk itace ta jamai wannan Bacin rai baima son ganinta Haraban gidan ya Fita yana Rataye da Jakarsa yana cika yana batsewa. Abba tare da Sadam Zasu mika Tunda duka kano zasu nufa,Sadam da Imran Dake gefensa agaba Matarsa Aneesa da ya"yansu Waleed da Waleeda sai Sagir suka Fara Mikawa sai Yusuf Dake driving Abba na Gidan gaba,Sai Munari da Inteesar da Anty Safiya Dake gidan baya Imran yana ganinsu yace bazai shiga Motar ba ya gwammace ya shiga ta Sadam ba ya son ya Zauna kusa da Inteeaar Baya son ganin kwanyan idanuwanta kallonta kadai kasala yake sakamar so yake yayi yaki da koma meke Damunsa bazai bari a Fahimci Rauninsa ba. Su Imran su suka fara yin gaba kuma sun Riga su Abba isa kano,Har Gida Sadam yakai sa har sai da yadan Jira su Abba suka kariso kana sukayi sallama ya kama Hanyar gidansa Dauke da matarsa da ya"yansa. Tuni imran ya shige Cikin Gida ya Fada Dakinsa ya maida koda Sagir bai shiga ba Daganan yayi ma su Abba Sallama ya wuce gida Domin ya Shaida Mama, Dawowarsu Inteesar bata Bisa ba Tunda itama yanzu Gidan su Munari kamar gidansu yake Munari tabi Zuwa Dakinta gabadayansu duk sun gaji ammh Inteesar Rabin Hankakinta na kan Imran Data gansa wani iri Har Sako ta Turamai kuma yagani bai bata amsa ba gabanta Fadi yake tana Fatan Allah yasa Fushin Khamis bai shafe ta ba. Sai da sukayi wanka suka yi salla suka Huta kana munari da Inteesar suka shiga suka sama musi Abunda zasu ci. Zuwa Dare kuma Kowa ya isa Gidansa Lafiya. Ta wayar Yusuf Abba ya Kira Baffa Kabiru da Daddy yayi musu ban gajiya Harda Inna Maimunatu itama ta isa gida Lafiya Inna Bintalo Tana Dukku sai gobe zata koma ita. Daddy da Abba sun Dade suna Tattaunawa kan Tafiya Lagos Sati mai Zuwa da yardan Allah Rayuwa Zata Inganta Ranar da Daddare Mama Sagir ya Rakota tazo ma Abba Murna da ban gajiya,Taga kowa banda Imran wanda tunda ya shiga Dakinsa bai Fito ba ko Sallah aciki yayi abunsa Da Mama Zata tafi ta Dunga ma Inteesar tsiyan Taga Gidan Abbanta Ta gujeta Inteesar na Dariya tace gobe Zata dawo Munari ta Daka Tsalle tace kafarta kafarta Abba yace ko"ina suka zauna Duka Gida ne shi bai da mtsala. Washegari da Safe Yusuf ya Tafi aiki Munari da Inteesar suka shiga makaranta saboda ana ta Karatu an Wucesu Safiya kadai ce agida Tana aiki sai Abba Imran na Daki sau Daya ya Fito da Safe ya Hada Tea yasha yagaida Abba ya Dauki Ruwa ya koma Cikin Daki. Da wuri Yusuf ya Dawo Daga Wajen aiki ya Siyoma Abba Sabuwar waya Saboda ya fara amfani da ita Abba yaji Dadi ya Dinga sakama Yusuf albarka suma su Munari sai yammah suka Dawo Daganan wajen Mama suka Sauka Munari ta Kira Ya Yusuf ta Fadamai yace bakomai.