Sashe 89
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai damu da yanayin kallon da ilahirin falon suke binsa dashi na mamaki ba banda Yusuf da Abba da su munari wadanda suka sansa suka san zai iya aikata abunda yafi haka. Mami Asma"u cikin mamaki da al"ajabi ta juya tana kallon Baffa Kabiru bata samu bakin mgana ba,Imran ya kara gyara tsayuwa Hannunsa guda daya na cikin aljihun bakin wandon dake jikinsa dayan hannunsa kuma yana rike da karan sigari kansa Tsaye idanuwansa basu Rusuna ba yake bin Fuskar kowa da kallo kai Tsaye Fuskarsa bata bayyana Fara"a ko sakewa ba,ya hade ran ya dakuna Fuska kamar an aikomai mala'ikun mutuwa. Daddy ya kalli Baffa Kabiru cikin mamaki shima ya kallesa,Kafin su maida kallonsu kan Abba wanda ya Dafe kai cikin Takaichi. Imran ya kara Kausasa Muryansa yana Fadin"Eh da gaske nake yi..ba inda Zamu je bama bukatar zuwa ko"ina wannan shine gidanmu..! Yafada yana Kai sigarin bakinsa ya zuka ya sake Fesar da Hayakinta Cikin kwarewa. Yusuf ne ya mike da Hanzari ya isa garesa Lokaci daya yana Fadin"Imu..Imu saurareni..! Kallonsa yayi ido cikin ido ganin haka ya sa Yusuf yace"Ka koma Dakin ka wannan ba mganarka bace..Mganar Abba ne da yan"uwansa bakai bama ko mu da muke gaba dakai bai dace mu ce wani abu ba..So ka koma cikin dakinka don Allah..! Yana mganar ne Imran namai kallon Tara saura kwata gira daya ya Dagamai cikin Salon rainin wayau kafin yace"Oh Really..Sai yanzu ne su sakansa shi dan"uwansu ne..? Meyasa lokacin dayake bukatar Taimakonsu suka Juyamai baya..?meyasa alokacin basu nuna ma Duniya su din Ahalinsa bane suka yasar dashi,suka Kyalesa suka Rika aibatasa da kaddaran da bashi ya Dora ma kansa ba wani kokari ko Himma sukayi wajen Sauya wannan al"amarin nace ka Fadamin wani kokari sukayi..? Yafada cikin Tsawa Ransa ya fara baci Idanuwansa sun sauya Launi Tuni jijiyoyin kansa suka Mike Radau suna Harbawa. Gabadaya kowa shi ya zuba ido yama kallonsa yana Sauraransa,Daddy ya sunkuyar da kansa aransa yana Fadin anzo wajen dayake ta gudu Tuntuni Baffa Kabiru kuwa mamakin Rashin kunya irinta Imran kadai yake,Matan kuwa kowa sai mamaki Mami Asma"u kuwa bawai ta kasa mgane bane mamakin al"amarin ne ya isheta Abba Take kallo Tana ayyana Abuubuwa da dama ganin yadda ya zauna yayi Shuru Yaronsa na Diban albarka ya kasa mgana. Yusuf dayasan Imran in ransa ya baci zai iya Fadar komai yasa ya Rikesa Gam yana Fadin"Is ok muje ciki don Allah Imran..! Kwace jikinsa Imran yayi yana Fadin"Wlh ba inda zan je..ai da Farko bam ce komai ba saboda ba"a kawo gabar da zan yi mgana ba yanzu ne Lokacin da zan ce wani abu..Daman Tuni ina jiran wannan Ranar da wani Daga cikinsu zai zo yace Mu koma Gida to bazamu koma ba..Naji dadin da kuka zo kuka ga Abba ya warke yasamu Lafiya yanzu kun Tabbatar da Ko da ku ko bako zamu iya Rayuwa..?kun tabbatar da Abbanmu ba Mahaukaci bane kaddarace ta Fadaamai kuma cin jarabawa da Daukan kaddara duk na Allah ne wanene acikin ku zai iya jure daukan Girman Raunin da muka Dauka? Abba ya rasa Anni mata take garesa Uwar ya"yansa ta rasu ko gawanta bai gani ba Ya rasa ya"yansa uku aLokaci daya acikin ku waye zai iya daukan girman wannan Raunin..?waye zai iya Tsayuwa da kafafunsa in wannan Jarabawan ta Fadamai ehe?Masu cewa Abba yaki yarda da kaddara su in haka ta faru dasu zasu iya daukan..? Masu cewa Abba ya zama Mahaukaci su in haka ya faru dasu waya sani ko zasu kashe kansu ne..? Masu ce mana muma bamu da amfani muna kara Raunana Abba su din sun manta Muma Uwa muka rasa da Ginshikin Ahali har uku..?sun manta muma muna sonsu ko sun manta muma muna da Zuciya da kwanjin in muka rasa namu mu nuna?ko shikenan mu ba Mutane bane Dabobbine da zamu yi wannan Babban Rashi kuma mu dawo muna Dariya Lokaci daya..?meyasa baku jamu ajiki kun Lallashemu ba..? meyasa baku nuna mana gata da soyayyah ba..? Meyasa baku rika nuna maana amfani Hakuri ta Lallashi da nasiha da ban baki ba..? Wlh har yau har gobe ina jin kunar kalmar Mahaukaci da wannan Mutumin ya Kira Abba dashi ina jin zafin hakan zafin daya kan kusa kona Kirjina in na Tuna Nayi ma Daada Uzuri yafi sau saba"in saboda Raunin Tsufanta ya bayyana kuma kamar yadda muke da Rauni haka take dashi itama Tana neman Mai Tallafamata ne in nayi ma Baffa Mustapha uzuri bai wuce Uzurin ya kasance mai Sanyi Hali kamar Abba kuma bai taba aibatamu saboda Kaddaran data Fadamana sai dai ina ganin Laifinsa na Hana Baffa Kabiru Aibata kaddaranmu na Hana sa Zagin Abbanmu da kiransa Mahaukaci Laifinsa na kin gayamsa gaskiyan kan Abunda yake Aikatawa abunda baitaba Tunanin yaya mu ya"yansa zamu ji acikin kirjinmu ba Ko ka manta Cewa Yadda ya"yanka suke awajenka Haka na kowa suke..?ka taba Tunanin ya ya Nauyin mganarka zata Kuntatamana..? Ka taba Tunanin yaya ya'yan Dan"uwanka zasu iya juran wannan Tozarcin naka..?baka taba Tunani ba Shiyasa kake komai naka kanka Tsaye shine yau zaka zo kace Abba ya bika ka kaima Daada shi Saboda tace ka dawo mata shi..? To ba inda Abba zai je Gari na wayewa kowa ya watse ya kama gabansa nan ne Gidanmu yanzu duk wanda ke son ganinmu sai dai ya tako yazo kamar yadda kuma kuka zo..! Ya karishe Fada yana Sauke Numfarfashi Cikin zuciya Idanuwansa sun kara sauya kala har sun cika da kwallah Saboda Tuna Abunda ya faru Baya,Gabadaya Falon kowa jikinsa yayi sanyi masu Saurin kuka Irin su Munari har ta Fara Inteesar na Lallashinta itama kwallar take ganin yadda Duk kafiyar zuciya iri nta Ya Imu yau Rauninsa ya bayyana Su kansu su Sadam jikinsu yayi sanyi basu da sani kan Abunda ya Faru Lokacin ammh indai Hakane Tabbas ba"a kyauta musu ba kuma suna da Ikon suce wani abu a wannan gabar. Baffa Kabiru ransa ya baci saboda kara kara Imran ya ambaci sunansa ya Nuna dashi yake cikin bacin rai ya mike yana kallon Abba Lokaci Daya yana fadin"Malami a gaban idonka kama ji kana gani D"an daka Haifa yana neman cin Zarafina ka kasa ceewa komai..? Yafada cikin mamaki yana kallon Abba Kafin Abba yayi mgana Daddy ya Rigasa cikin Kwantar dakai Yace"Barrister mganar gaskiya Imran gaskiya ya fada..Daman Ranar da nake ta Tsoron zuwanta kenan Ranar da wani Daga cikin ya"yan Yaya Malami zasu Tuhume mu da Laifi da kuskuran Gudumuwarmu wajen Nesanta kansa da yayi damu ina ta jin Tsoron wannan Ranar..Kada ka manta ko Zuwan mu dukku na Karshe kiran Daada kenan kuma ta fada ta kara Laifinmu ne laifin mu ne Ya Kabiru kaima ka sani..! Yafada cikin wani yanayi Umma ta Jinjina kai Batayi mgana ba,Sanin duk abubuwan da suka Faru,Baffa Kabiru yana da kaso mai tsoka kan Faruwar komai bai daukan abu da Muhimmanci indai bai Shafi matarsa da ya"yansa ba bazatace dai komi baa Saboda ba Huruminta bane bata taba mgana Kan Lamarinsu Daddy indai bashi ya tace wani abu ba. Mami Asma"u da mamakin kalaman Imran suka Daskaran da ita ta kasa wani Motsi tafa san gaskiyane saboda ai Da ita ake komai da gudummuwarta a Lokacin tana gayamai bai kamata ya zauna yayi ta Wahala da Abban ba ai ba yaro bane kuma baida ilimin sanin Mutuwa ce da zai zauna yana wani abu kamar mara Hankali Tana nunai ai da gangane saboda su ya rika Hanasu Harkokin gabansu da irem iren wasu maganganu alokacin koma meya faru da saka Hannunta ammh Dayake ita Macece mai son kanta bata iya ganin hakan ba sai take ganin kawai ana neman cin Zarafinsu ne. Mikewa tayi Tana Tafa hannu Cikin mamaki kafin tace"Au har dakai Baban Basheer..?Yau da bakin ka kake Bude baki kana Fadin Abban Sajid bai kyauta ba shi keda laifi kai ka cire kanka..? To Tunda shi keda alhakin komai meyasa alokacin daka Fahimci haka kai bakayi kokarin gyara komai ba tunda kai ka Fahimci shi ya bata komai..? Tafada tana kallonsa bai yi kaurin baki ba yace"Kin ji sanda na ce shi kadai keda Laifi Barrister Asma"u..? Cewa nayi dukkanmu munyi laifi ya sani na sani Kowa ma ya sani Tunda Daada gaban duka ya"yanmu ta fadi haka..! Mami Asma"u ta dagamai hannu Cikin Fusata tana Fadin"Bana son jin komai Mustapha..ai ka riga ka gama mganarka Abban Sajida kaga abunda nake Fada maka ko..?ai daman na fadamaka kune kuka damu dashi shi kam bai damu ba yana nan yana Rayuwarsa Kama gani Harda dan Shaye shaye ma ya samu cikin ya"yansa..Baya bukatar kowa..Ka taso mu tafi Abuja batamana Nisa ba bayadda zan zauna ina ji ina gani ana Tozarka ba..! Tafada Tana isa garesa Lokaci Daya ta kamo Hannunsa Shi dake tsaye ya kasa mgana saboda baida ta cewa,shi kanshi ai yasan bai kyauta ba to shima Selfish bazai barsa ya iya Daukan haka ba da kuma Ego irin nashi Daman dagashi har matar tashi They are d same. Maimakon ya nuna mata hakan datace bai dace ba sai ya kada kai yana Fadin"Yes hakane abunda ta Fada..Daman duk abunda nake yi saboda Daada ne..Tunda kuma shima Malamin ya nuna yana bayan mganar Da"nsa bani da tacewa..Ma"u muje..! Yafada suna Kokarin barin Falon kowa ya Bisu da kallo baki sake Abba Dai na Zaune duke da dakai bai cekomai ba Har wannan Lokacin. Daddy ne ya mike yana Fadin"Haba Barrister ya zaka Biye mata..? Itafa macece ya kamata ka zauma mu Fahimci juna..! Ko juyowa basu yi ba suna Shirin barin Falon Imran ya saki wata Dariyan Basawa Cikin Kaushin Muryansa yace"Ka kyake su tafi Baffa..Daman ai ba komai ya kawosu ba sai son kai irin nasu abunda kuma suka zo dominsa sun ga ba Nasara Abba bazai je ko"ina ba..! kalamansa yasa gabadayansu Juyowa kowa sai da ya jinjina mganar Umma ta kada kai aranta tana fadin yau an samu mai daidai da Asma"u Sa"id da Sadam suka kalli juna,hakama Matansu suna ayyana Tabbas Tsaurin Idanuwan Imran sun wuce Tunaninsu. Mami Asma"u ce ta nuna kansu tana Fadin"Mume kake kira masu son kansu..? Lalle shaye shayen ka yayi maka Rana..Tunda har kakiramu masu son kai.kuma kake Tunanin Daada ta tako kafarta ta Biyoku lalle Kwayarka bata Fadamaka daidai ba