← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 190

Sashe 28

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

******
Mama ita da kanta ta Shiga da Safiya Har Cikin Falon gidansu Imran,bayan ta Umarceta Data Shiga da kafar Dama Ta kuma yi addu"an Neman kariya da Zaman lafiya,Yusuf na Biye Dasu Dauke da akwatin Safiya yana Jinsa kamar yana Yawo a sararin Samaniya saboda Farinciki.
Gefe Daya kuma kukan Safiya na Tayar mai da Hankali,Sai kuka take Cikin mayafi kukan da bai isa ya Hanata yinsa ba yanzu.
Afalo yace su Zauna kafin yace bari ya Shiga Ciki ya gayama Abba Mama tace toh..Lokaci Daya Tana Zaunar da Safiya kan Kujera Itama ta Zauna Gefenta Tana kara Bin Falon da kallo Ko"ina Shuru da alamu babu kowa Babu dai abunda ya Sauya Daga yadda tasan Gidan
Ba jimawa sai ga yusuf ya fito Fuskarsa Cikin Fara"a yace"Mama Abba yace ku shigo..!
Mama ta mike Tana Fadin"Taso muje Safiya..!
Tafada Lokaci Daya tana Rikota Mikewa Tayi Kanta Har Lokacin Yana Cikin mayafinta shi yayi musu jagora Har zuwa Dakin Abba.
Yana Zaune gefen Makeken gadonsa,Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara ya Rame sosai gemunsa ya dan Taru Da Farin gashi,Yana Rike da Charbinsa yana ja Da alamu Alwala yayi Domin Fuskarsa akwai Dashin Ruwa.
Yusuf ne akqn gaba Mama dake Rike da Safiya na Binsu a baya,Gefen Abba ya Zauna yana Fadin"Abba gasu nan..Mama ku zauna don Allah!
Mama ta zaunar da Safiya saman Cafet a gaban Abba itama ta Zauna Gefenta Tana gaishe da Abba ya amsa mata cikin Sakin Fuska,Duk da bai da lafiya ammh yasan mai Gaisheshi Duk da bai taba Tsayawa ma ya kare ma Maman kallo ammh Tabbas yasan Maman Sagir abokin Imran Tazo Gaisheshi ba sau Daya ba Shiyasa ya amsata Cikin kulawa Duk dama Yusuf yamai Bayani komai.
Mama ce ta Dafa kan Safiya Tana Fadin"Ga Safiya nan na rakota..gidana kanin Mahaifinshi Shi Sagir din da Sukaje suka sama da mganar Nema ma Yusuf din aure ya kawo ta Bayan Mahaifinta ya Riga ya Daura auran kuma ya Hadosu da ita..Shine nace bazan barta Tazo ita kadai ba bari na Rakota..!
Abba ya jinjina kai Shuru kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Bakomai yusuf yamin bayanin komai..Mungode kwarai kiyi ma Kanin Shi Mahaifin yaron naki Godiya,Nagode kwarai Daya Tsaya ma Dana bawai Domin yq rasa masu Tsaya mai bane..A"a sai Domin wasu Mtsalaloli na Rayuwa..!
Mama ta Murmusa kafin Tace"Ayya Bakomai..Ai ya"ya na kowa ne Alhaji..!
Abba ya gyada kai yana Fadin"Hakane Duk da hakane Dole Zanyi Godiya Sabodq yayimin ni abunda ina da Rai na kasayi Saboda Rashin Lafiya ammh da Izinin Allah da Taimakon Ya"yana dana Likitan Dake Dubani na Fara Samun Lafiya na Dawo Cikin Hayyacina da Yardan Allah komai ya kusa Zuwa karshe..!
Mama tace"Allah yasa..Allah ya kara Lafiya..!
Yusuf ya amsa da Ameen Kafin Abba ya kalli Safiya Dake Duke kanta Cikin mayafinta Tana kuka Abba ya kalli yusuf kafin yace"Ya sunanta...?
Yusuf na sosa keya yace"Sunanta Safiya Abba..
Abba ya maida kallonsa kan Safiya ya Daga baki ya kira Sunanta Har sau Biyu ta amsa Cikin Dattako yace"Dago kan ki nan yata..Dago kanki ki kalleni Dakyau ni ba Surukin ki bane..Daga yau ni UBA nake gareki Safiya kamar yadda nake Uba ga Yusuf da imran da Maimunatu..!
Ba Safiya kadai ba Hatta Mama kalaman Abba sun kashe mata Jiki Cikin Sanyi Jiki Safiya ta Dago kanta ta yaye mayafinta Tana kallon Abba da Jajayen Idanuwanta,Lokaci Daya Tana ganin kamar Yusuf ne ya Tsufaa ga kuma Yuauf din a gefensa Tabbas wannan kamar har ta baci bazata iya Juran kallonsa ba sai ta Sadda kanta Dan Mirmishi Abba yayi kafin yace"Allah ya albarkaci Auranku..Dukkanku ya"ya na ne..Saboda Haka tare zanyi muku Faada..Ku Rike amanar Junanku Yusuf ka Riketa Amana Domin Tayi maka Hallaci,ni kuma nayi miki alkwarin Zan Tsaya Miki mtsayin Uba koda watarana Yusuf yayi miki Wani abu kada kiji komai kizo ki Fadamin Daga Rana mai kamata ta yau ni zan Dinga Tsaya miki Har karshen Numfashina..!
Kawai sai Safiya ta Kara Rushewa da wani kukan,Kukan Farimciki da wani yanayi Domim kalaman Abba Dagaji Daga Cikin Zuciyarsa ne.
Mama ne Tana Mirmishi tace"Ai kagama Mgana Alhaji..Allah ya basu ZAman lafiya..!
Abba da yusuf suka amsa da Ameen Ameen.
Abba ya kalli Yusuf yana Fadin"Yanzu ina Zaka sakata..?.dazu na Fita na Zaga ko"ina Gidan yana da Girma sai dai ba plan akan ginin.."
Mirmishi Yusuf yayi kafin yace"Komai zai koma Daidai Abba..Zamu zauna da ita adakina..Kafin na gyara mata Falo da Bedroom din Dake kusa dana Munari..!
Abba ya jinjina kai kafin yace"Hakan ma yayi kyau..Ammh dai Zaki Rakata Har Dakin Mijin nata ko..?
Mama tace"Me zai hana..? Sai na mikata.."Abba ya Gyada kai kafin yayi ma Mama Godiya ta mike ta Riko Safiya suka Fice yusuf yabi bayansu Abba ya bisu da kallo yana kokarin Shanye Hawayen Dake kokarin kawo mai.
Sun Fito kenan Falon Yusuf ya Dauki Akwatin Safiya yayi Musu Jagora Zuwa Dakin nashi Imran ya Shigo Kamar an jehoshi Ransa a bace yana Tafiya yana Wani Buda Jiki Daga Yusuf Har Mama ba wanda ya kallah Balanta su suka ran zai yi musu mgana,yusuf ne ma yake kiran Sunansa yayi kamar bai ji ba ya Tura Kofar Dakinsa ya Shige ya banko Kofa Baya ji,sai karan Ta"awizin Inteesar Dake mai amsa kuwwa cikin kunnuwannsa,Sai kuma ganinsa Gabadaya na Hasashomai Lokacin Data toshe Hanci ne da Lokacin Data
Zubar da Miyar Ransa ya gama Baci.
Bango ya Daka da Hannuwansa yana Fadi"Who is she..? Who is d Hell is Her...? Da har zata Toshemin Hanci ta kuma Zubarmin da miyau bayan ta Kirani Shadani..!
Waye ita.? Haka yake Fada Zuciyarsa na Tafasa yana Daga Tsayen ya Zaro Sigari ya kunnata ya Yi mata kyakyawan Zukan da sai da yaji Ya kware da Hayaki kana ya Dakata ya koma yana Tari Idanuwansa sun kala sunyi Jajir,Kan kujeran Kwara Daya Dake Dakin ya Zauna ya Dora Kafa Daya kan Daya yana Girgiza ta Hannu Daya kuma yana ta Zukan Sigarinsa yana Fesae da Hayaki.
Yana Tuna Ko Lokacin da yake amsa Sunansa na Natsattsen Imran Abubakar Malami ba wata macen Data Taba kallonsa Tayimai wadandan Abu uku da yarinyar tayimai ba..Tun ba yanzu ba ya Tsani Raini Shiyasa baya Hulda da mata Sannnan su da kafara Sakarmusu Fuska Zasu Samu Hanyar Rainaka..Ballatana da yanzu yake jin kansa na ya Ishi kowa Riga da wando..Ya ke jin kansa a Mtaayin roban Wando Daidai da kugun Kowani Shege bama shegiya ba..Shine wata Yarinyar karama Zata Kirashi Shedanu ta kallesa ta Tsitar da Miyau ta kuma Toshe mai Hanci ba bu Wanda ya taba cimai Zarafi irinta,Duk iya kokarimsa Na ya Cire Abun aransa ya kasa ji yake koda waasa abun bazai iya Wucewa a wajensa ba Har Abada.
Sai da aka kira Salla ya tashi Bayan ya gama karar da kwalin Sigari Duka Ya Fada Tiolet aranshi Yana ji in Sagir ya bari suka Hadu Wlh sai ya Nausheshi a Bakin da sai Hakoransa na gaba sun kama gabansu Saboda ko yayane Shi yajawomai Raini wanchan wannan kwailar yarinyar inda bai Ganta yayi mata mgana ba ba yadda Zatayi ta Tsaya Har ta Cimai Zarafi ba.
Yana wanka yana kwafa,ji yake kamar ya Daki kansa yana jin Haushin yadda ya iya kyaleta bai Tsinkamata marin Da Sai ta ga Taurarin Wuta Wanda nan gaba Ko bashi ba Bazata kara Kokarin Raina ma wani wayau ba ballatana taci Zarafinsa ba.
Chapter 28 · 0% Book details