← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 190

Sashe 167

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mgana Munari na Kallonta sai ta bata Tsausayi ya Imu naWahalar da Inteesar ta rasa ta yadda Zata gayamata ta gane komai itama Ta Dauki Hanyar Ramawa bata karance karance bata damu davSocial media ba ballatana ta san wasu abubuwan gata kadai ta sani ita Tana Karance karancen Littafan Hausa Dana Turanci Tana kuma Mu"amala da Social media Tafi Inteesar Bude ido sosai kuma ta Fita Shiga Mutane.. Ganin ta Damu yasa Munari taje ta Fadama Abba yadda akayi Abba bai ce komai ba Daman yasan Za"a Rina Ya Yusuf na gefe yana Fadin"Shi yama yi Auran Har yau bai yi Hankali ba..? Abba ya Daga waya ya Kirashi bai Daga Kiran ba sai da ta Katse kana ya Kira Daga baya Abba bai ma Tsaya amsa Gaisuwarsa ba yafara Fadin"kana ina..? Imran ya Dakuna Fuska yana Tsaye a Falon gidansa Roban Ruwa Hannunsa Guda Dayan kuma yana Rike da Waya yace"Ina Gida Abba..! Abbba yace"Ka manta da Matarka ne ka wuce gida baka zo ka Dauketa ba..? Imran yace"kafar da ya kawota sai ya Maidota Abba..ni ai ban aikota ba..! Abba yace"Ni kake Fadama haka Imran..?wato Kafarta ta maidota ko..!Nagode..! Imran yadan Bude ido yana Fadin "Abba kada ka Dauki mganar nan da Zafi..Ba dakai nake ba..Ni ban ce tazo ba ta Raina ni ne Dole ne sai abunda Take so zan yi akoda yaushe..?nace mata Kada taje bataji mgana ta ba ta Tafi ai tunda ta iya gaban kanta sai ta Dawo da kanta..! Abba yace"Kayi mata hankali Ita yarinya ce..! Ran Imran ya kara baci yace"In ita yarinya ne sai ni kuma Shikenan sai na Lalace akanta..?Ni Bata mata Rai zan yi bana son wasa meyasa batajin mgana ne..! Abba yace"Kayi Hakuri kazo ka Dauketa..Yaushe Zata rika Fahimtar ka kana mata mgana Gatse gatsen ka Kwata Kwata kai Imran baka Laushi..! Imran yace"Abba nayi Laushi Saboda ita..Bata Samu Compt Imran ba Half Ta samu..kuma na riga na Rantse ni ban Zo na Dauketa ba kuma bata isa ta Sani Kaffara ba..! Abba ya Bude baki kafin yace"Har nima ko..! Cikin Dakuna Fuska yace"Ni fa Abba ban ce kai ba..! Abba ya gyada kai yana Fadin"Ka dinga dai Hakuri kai Babba ne ka Girmeta..Ka Rika Tunawa sai ka Sadda kan ka wani Lokaci ita yarinya ce akwai kuruciya Tare da ita..! Imu Hade rai aransa yana Fadin Wato ya Sadda kai ya Zama Sakarai Allah ya Tsareshi..! Abba yace"Yusuf zai kawota..Zan mata Fada kada ka mata wannan Hargagin naka nasan Halinka..! Imran ok kawai yace ya Katse Kiran Ransa na baci kokarin ma Daidaita kansa yake In yace abu baya so kuma ana Damunsa akai Abba fa da kansa yace kada su dawomai Gida nan kusa Shi mutum ne Dake Daraja Kalaman mutane masu Daraja awajensa Musamman Abba Shi bama da Wata Manufa yace mata kada taje ba ya bari ne sai Abba ya nemesu da kansu suma su Rama bacin Ransa Daya daya Dawo bai ganta ba wato ke je din Taje din Sai Taga abunda zai Faru..! Abba Fada yayi ma Inteesar Sosai Tayi Narai Narai kana Abba ya Umarci Ya Yusuf Daya maidata Gida Tace Munari Tazota Rakata Munari tace Allah ya Tsareta Ta Rakata Ya Imu ya Hada da ita,Tana ma Rokonta Kada ma a bayaninta ta Kira sunanta Inteesar dai Tasan yau sai ta sani da Fada Ya Yusuf ya Dauketa ya kaita Gidan ya kulle gidan ta Ciki sai da Ya Yusuf ya Kirasa a waya kana ya Fito ya Bude mata bai Shigo da Motar ba Daganan yayi musu Sallama ya Juya Imran yana wani Cin mgani aransa yace Yau Inteesar ta Zama nama kenan.. Shi ya Tsaya Rufe Gidan ita kuma Tayi Sadaf Sadaf ta Shige Cikin Gidan Tana Kokarin Shiga Dakinta ya Shigo Falon Cikin Dakiyarsa yace"Zo nan..! Cak ta Tsaya gabanta na Fadi kafin ta Juyo bata iya Dagowa ba kanta na kasa Tana wasa da adon Gyalen dake Jikinta Daga sama Har Kasa ya Kalleta Kafin yace"Sagir bai baki Sako ba..? Kai ta girgizamai Cikin Dakuna Fuska ya Danna ma Sagir Kira ta Wayar Dake Hannunsa Buga Daya ana Biyu ya Daga Yana Fadin"Ango kasha Kamshi..! Imran yayi Tsaki yana Fadin"mallan ina Aikin da na baka..? Sagir yace"Wani aiki kuma da Daddaran nan..? Imran yace"Hijabin da na baka kudi a Dinkama MARYAM..! Sagir yace"Au na manta kasan bani ke yi ba Kasuwa nakai Wajen wani abokina yana Dinkasu kala kala bari gobe zan Tabosa naji ko ya gama Hala Baka son Tana saka Mayafi ne..? Banga Laifinka ba kada Maxa su kalle ma yar babynka..! Imran Tsaki yaja ya Datse Kiran Yabar Sagir da Dariya Inteesar na Gefe Tana Sauraransa Zama yayi saman Kujera ya Dora Kafa Daya kan Daya yana Sanye da Riga da Wando Fari da baki. Kallonta yake yi yana Kokarin Daidaita kansa Cikin Kaushinsa yace"Yaushe kika Fara rainani da Har Zan ce kiyi abu kiki yi..Sai abunda kika ga Dama Zakiyi..? Yauahe muka Fara wannan Dake..? Ya Fada Cikin Tsawa da Daga Murya Inteesar da Tuni Idonta ya Ciko da Hawaye ta ce"Kai fa..kai fa kace naje..! Cikin Hararanta yace"Yaushe nace kije..?cewa nayi ki je din Shine kuma Saboda Tsabar kin Raina ni sai kika je din ko..? Inteesar na Sosan Idonta tace"Naji to kace naje kuma...! Ransa ne ya kara baci ya daka Mata Tsawa yana Fadin"Shup up anan Wajen in kika kara mgana Kika Harzukani Zan tashi nayi kasa kasa Dake anan Wajen..!. Jin haka yasa ta Toshe bakinta da Mayafinta Tana Hawaye bata son Fada a Rayuwarta. Cikin Fushi yace"Bana so..Bana so..Ina mgana kina mgana Raini ne..Zaki cemin ke bakisan gatse bane..?da zaki kwashi Kafafu ki Tafi..?Kina Biyema wannan yarinyar ko..?munari Daya kuke da ita..?ke fa matar aure ce nan ne gidanki itama Chan ne gidansu Ammh baki da aiki sai Biyemata sai anyi mgana Kice Munari Munari kaza kaza..Munarin Daya kuke da ita nace..? Yafada Cikim Tsawa ai Sai Inteesar ta Saki kukanta cikin kukan Tace"Ni bansani ba..Wlh bansan Gatse kamin ba..kana ta min Fada..Ni bana son Fada..! Take Fada kafin ta Shige Daki da Gudu Tana kuka Baki ya Saki yana kallonta Wato ita batasan Fada..?to ya barta ta Cigaba da iskanci kenan bai Mata Fada ba,daya Daga Cikin Illan Auran yara kenan Yanzu in babba ce Taya ya Zaka Xauna ma kana mgana..?ai tasan abunda ya Dace da ita Soyayya batayimai adalci ba Data saka ya Fada soyayyar yarinya karama Datake Neman ta Sauya shi Daga Imran dinsa Zuwa Wani Imran din na Dabam Yana Jinta Tana kuka yayi banza da ita In bai rika mata haka ba Watarana Da mganarsa Zata Rika ja tana yarda taga Dama Kwanjinsa bai Hana in Anyi ba Daidai ba ya magantu Soyayyat taci kaza kazanta alokacin in Komai ya Dawo Daidai sai a Tuna. Yana Aiki Bisa Laptop dinsa yaji Har Tana jiniyan kuka kamar Wata karamar Yarinya. Da Sauri ya Mike Ransa na Baci ya Shiga Dakin afusace kan gado ya ganta ta Dunkule Tana kuka kamar ya Daketa Cikin Fusata yace"Na Dake ki ne..?Kukan Dadi kikeyi kinsan Allah in baki min Shuru anan Wajen ba Na Tako Inda kike sai nayi kwallo Dake Nagani kukan Jini Zaki yanzu ko na Hawaye..! Ai jin haka yasa Kaji Inteen Daddy Tsit Tasan zai aikata Kyafci yayi ya Fice Daga Dakin Ta rakasa da Harara Damam kukan Tabara ne afili Tace"Ko ma ya Lallasheni ina kuka.!.tafada Tana Tura baki Ranar Bai kara ganinta ba da Safe mahar ya Fita bata Fito ba aransa yace in na Nemeta zata Rainani ne gwara na Kyaleta ai itace Tamin Laifi da Wannan Tunanin ya Fita Batunta mai Dade a Office Dayake asabar ne wani aiki ma ya karisa Daganan Shagon Sagir yaje suka sha Hira bai bar Sagir yayi Salama ba sai da sukaje suka karbo Dinkin Hijaban Inteesar matar mallam Imu ce yadi Hudu Hudu ne Har yana jan kasa Mama Tayi Danwake ya Shiga Har Ciki Suka gaisa suka ci Danwake shida Sagir yana ganin Gidansu yaso kamar ya Shiga sai kuma ya fasa kada Intee taji tace Ita ya Hanata Shiyasa ya Fasa shiga ammh sun Hadu dasu Abba a Masallaci Ya Yusuf nata yimai Tsiyan mai Yaji ya Daka Borkunu Imun Abba.. Bai ce komai ba ya Kara Hade rai kamar an aikomai da Sako mara Dadi a an anguwar yayi sallar Isha"i kafin ya Koma Gida Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba ya Damu Yana so yaji Lafiyarta ya barta itaa kadai agida Tun Safe. Ya Kirata bata Dauka ba ya Turamata sako. "Kina lafiya..?. Ta karanta Ta Sharesa Wata Zuciya Tace ka kama kanka Imran da Girmakka Yarinya na neman janka a kasa da wannan Tunanin ya Fita Batunta ammh fa Tana Ransa Ranar Lahadi ba aiki yana Gida yana Daki yaji Fitowarta da Safe ta Shiga Kitchen yana jin haka ya Fito Falo ya Zauna Saboda yaji kamar Girki take yi Sai da Ta gama ta Fito Dauke da Filet Shake da Indomie,Ko Gaisheshi batayi ba Bakinta agaba ta Shige Daki Dauke da Goran Ruwa ta kasan ido ya Kalleta Dariya ta kamsa afili ya Furta"Imu ka Tabo Autar Daddy sai Allah..! Kitchen din ya shiga yaga iya Cikinta ta Dafa,Cikinsa ya Shafa ya Lafe sosai yana jin yunwa Inteesar Muguwa ce ko Ta Dafa dashi in bazatayi mai mgana ba ko acikin Kitchen din ta ijiyemai yazo yaci bakomai. Hakanan ya Dafa Ruwan zafi yasha Tea sama sama ya Dawo Falo Laptop dinsa ya Dauko ya Fara aiki Domin ya Daukemai Hankali. Ranar haka suka Wuni Inteesar Har Kai take kaudawa bata son kallonsa Imran shima ya Mazaye baya bari Ta gane ya ganta shima ya nuna mata ya Fita Zafin kai. Washagari Monday Ranar ne Last Paper dinsu,Karfe 10:00am suke da Jarabawan Zai Rigata Fita Shiyasa da Safen ya Taka Har Dakinta tana Kudundune Cikin Bargo ta Rufe ido kamar mai barci batasan ya ganta ba Tana Danna Waya tana jin Sallamarssa Ta Tusa wayar Cikin Bargo Tana Barcin karya. Bai bi ta kanta ba ya Ijiye mata Ledan Hijaban yana Fadin"Ki yi amfani dasu..Bana son na kara ganinki da Mayafan nan..! Yafada Lokaci Daya yana Dora mata Dari Biyar saman ledan Ya kama Hanyar Fita yana gyaran Zaman Briefcase din Dake hannunsa. Yana
Chapter 167 · 0% Book details