Sashe 159
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rai Sagir ko ta kansa bai bi ballatana ma ya Tsaya Tambayansa. Bayan La"asar su Inna Maimunatu duk suka dawo Gidan Abba sai gobe zasu Tafi su Maman Nasara kuma Gidan Mama suka yada Zango suna sai gobe zasu tafi Su Munari suka bari agidan dsu Anty Aneesa itama Anty Safiya ta koma Data Raka Mommy da Anty Saratu Tasleem dai Tana Gidan Amarya sai an juma Zata dawo. Su suka Hadu suka kara gyara Gidan suka Share suka Turare gidan Turaran Wuta masu kamshi da Sanyaya rai Wanda Maman Nasara tazo ma da Inteesar da yawa kala kala bayan na Jiki harda na Daki dana Turara gida.. Sai gabda mangariba suka yi Shirin Tafiya Fareesatu sun fasa Tafiya suma sai Gobe Mazajen nasu suka zo Daukansu zuwa Gidan Abba abar Amarya Ta Huta kafin Ango ya Shigo. Inteesar da Farko bata Damu ba sai da Taga Tafiyar zasu yi da gaske kana ta Fara Kuka Tana Rike Munari Duk Dauriyan Munari Sai da tayi kukan Sabo hawaye shabe shabe aka Bambare su Daga Jikin juna aka yo Waje da Munari Hafsah ma da Tasleem da Nasara sai kuka, Harda Umaima itama Haka suka Shiga Mota suna Sharan Hawaye Inteesar kuma Ta Kudundune kan Gadonta Tana ta kuka kukan da kowacce mace take yinsa Ranar da aka Kaita Gidan Mijinta Za"a Tafi a barta. Gashi kuma suna da Jarabawa Allah yasa Munari ta Dauko mata Wasu Li ttafai da Zata Bukata Ba mganar Amarci mganace ta Karatu kawai ba kama Hannun yaro,Sagir ma yazo Daukan su Hafsah aMotan Imran din Tunda ya iya Tuki Imran ya koya masa,Dukkansu agidan Abba sukayi Sallar mangariba aka Zauna anata Labarin Biki da maida yadda abubuwa suka Kasance Imran na Cikin Dakinsa ya kasa Tabuka komai Kewa yake jin kewa zai yi nesa da Abba da Ya Yusuf da Gidansu Daya Saba Dashi Fiye da ko"ina zai Tafi yau ya Kwana ainda bazai ji Motsin Abba ba Rauninsa yaso ya Tabasa Raunin Tuna Anni a wajensa Yau yayi aure zai Tare a Gidansa ammh Anni bata Wannan Duniya yana Tuna kalamanta Imran Duk Ranar da kayi aure ni da kaina Zan Rakaka Dakin Matarka ba Kai ne Zan bama Hakurin Zama da ita ba kai zan bata amanarka na kumace Tayi Hakuri Domin ba karamar Jaruma bace Macen da ta yadda ta aureka.. Alokacin Tabe baki kadai yake yi baya Mgana ammh yau sai da Zafafan Hawaye suka Zubomai acikin Kwarmin Idanuwansa ya Hade kansa da Gwiwa yana ta kuka kukan mai Cinrai da kewa da kaunar Uwa acikin Ransa. Abba ne yake ta Cigiyansa kan abar Inteesar ita kadai achan Gida Sagir aka Kira kosuna Tare yace shima Nemansa yake yana ta Kiransa bai Dauka ba Yusuf ne yasan ba inda Za"a Gansa sai Cikin Dakinsa Halin Daya Samesa ne yasa ya Kira Abba Shi kanshi Abba sai da ya Fitar da kwallah Shima yayi kuka a irin wannan Ranar Allah ya jikan Zuwaira da Sauran ya"yanta Allah yasa suna Cikin Aljannah Haka Abba ya Rungume Zaratan ya"yan nashi yana Sharan kwallah yana Lallashinsu sun yi ma yan"uwansu da Mahaifiyarsu addu"an Dacewa da Fatan Allah ya jikansu da Rahma. Yusuf shi ya Hadama Imran Kayansa da Zai Bukata Tunda bai Dauki Hutu ba Mr Tunde da Mr Sulaiman sun yi Dashi ya Dauki Hutu yace bazai Dauka ba Duka Duka yaushe ya Fara aikin Da wannan kuma don wannan Dole suka kyalesa Har Khalil ma yamai mgana shima wannan Hujjar ya kawomai kuma shima ya yarda yace ya bari sai nan gaba sai ya Dauka sai susha Honey moon Cikin Natsuwa Lokacin itama Intee ta gama Jarabawarta ba Streess na makaranta. Duk yadda Imran yaso kada Rauninsa ya bayyana kasawa yayi yau Rana ta Farko da kowa yaga yana kuka Ya Rumgume Abba kamar Wata Mace ba wanda bai Tsausayamai ba Abba ya Buga Kafadarsa yana Fadin"Ka Daina kuka..Jarumai kamar ka da Juriya aka sansu ba kuka ba..Kaje Ga.Matarka Allah yayi maka albarka ka Riketa Amana Kanwa take gareka Ta Kowani bangare ta Chanchanci Kulawarka..Sannan Rokona na Karshe ka Rage Zafin Rai don Allah Imran kuma ina Rokon Allah yasa wannan auran ne Sanadiyar Dukkan Wasu alherai Allah ya Zaunar daku Lafiya! Gabadaya aka amsa da Ameen Ameen Sagir ne zai Tukasa zuwa Gidan bayan an gama Saka kayan nashi a Mota ya Shiga Gidan Gaba Sagir yayi Riverse ya Fice Daga gidan su Abba na Dagamai Hannu Yusuf bai san yana Kwallah ba sai da yaji Abba ya Saka Hannu ya Sharemai ko da Imu ya kasance bamai Hayaniya da shiga Mutane ba Akwai Shakuwa Tsakaninsu Sosai Kuma shi Sabo ai ake yima kuka Su Sa"id suna ta bama Yusuf baki suna Fadin suma fa Tare koda yaushe suka so zasu ga juna ba"a Rabu ba Har Abada. Shi kanshi Sagir Jikinsa ya Mutu da yanayin Imran din kuma shima wannan kewar na Damunsa Bai fi Shekara uku Dayasan Imran ba Ammh Sun yi Sharing din kauna da Shakuwa a Tsakaninsu suyi Fada su Shirya ammh kuma basa iya Rabuwa da juna Ammh yau aure yakai Imran wani Mtsyin da zai bar anguwan Gabadaya sai dai Waya ko kuma in ya Lekosu shima Tuni jikinsa yayi sanyi Har suka kai Gidan ba wanda yayi ma Dan"uwansa mgana.. Gidan bamai gadi Imran ya Sauka ya Bude Get din Sagir ya Shigo Ciki Shi ya Tayasa suka Kwashe kayan zuwa Cikin Gidan Har Cikin Dayan Bedroom din da zai zama mallakin na Imran ne. Sagir ya zauna Saman Daya Daga Cikin kujeran Falon yana Fadin"Ango ba Kazan Amarci haka zaka shigarma Amaryan taka Hannun Rabbana..! Imran na Tsaye yana kallon Wani Barayin ya Karkace kai Idanuwansa sun kala yace"Uhm..! Daga haka bai kara cewa komai ba Sagir ma sai bai kara cewa komai ba yana Bin Falon da kallo yace"Baffa Kabiru yayi Kokari..Allah ya Biyasa..! Imran na Jinsa bai ce komai ba Tunaninsa ya Tafi yadda Rayuwa Zata Juyamai na Rayuwa shi da Inteesar a Inuwa Daya a mtsayin mata da Miji. Anya zai iya Daukan wannan Nauyin..?shifa ba Daya yake da kowa ba Kansa ma bai Damu dashi ba ballatana Nauyin wata..?wata zuciyar tace mai ai ita Zatta kula Dakai kaima ai Zaka kula da ita Tunda itace kadai Zuciyarka bata manta da ita ba..! Yana Cikin wannan Tunanin Sagir yace"kamar Tashin kuka fa nake ji aciki..?ko Inteesar ne bata Daina kukan Rabuwa dasu Munarin ba..? Sai alokacin Imran yaji dan Tashin kuka Kofar Bedroom din Dayake Kyautata Zaton tana ciki ya sakama Ido Itama Tana kuka ne..? Shi tasan meya sa yake kuka..?saboda yau zai kwana inda ba Yusuf ba Abba ba Munari wadanan sune Ahalinsa da baida Kamarsu duk Duniya ko"ina Yaje ya dawo Su din kamar wasu Garkuwa ne a garesa yana kukan yau ya bar Gidansu Wata Rayuwa ta kawosa Wata gabar da bai Taba Hasashe ba ko Fatanta nan kusa ba bai Taba ji aransa zai iya aure nan kusa ba sai gashi shigowar Inteesar Rayuwarsa ta sauya komai. Sagir ne ya Katsesa Yana Fadin"Bari na Tafi..Tunda naga anko kuka kai da Amaryan taka kai kuka ita kuka..Kawai ka shiga Ciki ne ku Hada kai kuyi ta Rafzan kuka sai gobe da asuba sai ku Dakata..! Yafada Lokaci Daya yana Mikewa Tsaye Imran ya Murmusa Lokaci Daya ya saka Kafa ya Daki Kafar Sagir yayi Gaba da Sauri yana Fadin"Bakomai na yafe Maka duk cikin Nishadin Ango ne..! Yafada yana jin wani kewa na kamaaa sa bayaso ya waigo Hawayen Dayake ta Rikewa ya bayyana Imran ya Taka ya Bisa yana Fadin"bazaka Tsaya mu yi Sallama ba..!? Sagir na Ficewa yana Fadin"Wani Sallama.?bayan wacce mukayi..Sai da Safe a gaida Amarya sai an kwana Biyu indawo cin Girkinta ka Fadamata tayi Hakuri haka auran yake kaima Allah ya baka Hakuri Imran Allah ya baku Zaman lafiya..! Yafada Lokaci Daya yana Dauke Hawayen da suka Cikomai ido Imran ya Tsaya Cak yana kallonsa juyowa yayi yana Mikamai key din Motarsa yana Fadin"Sai da safe..! Imran ya saka Hannu ya karba yana Fadin"Zaka Samu abun hawa kuwa..? Sagir ya Gyada kai yana Fadin"Insha Allahu..! Imran yayi gaba yana Fadin"Muje na Taka maka! Yafada yana Tusa Key din Motar Cikin Aljihun yadin Boyel din da Sagir yayi musu wanda suka sanya yau din Yana jin Wani abu Daga Karkashin Ransa Sagir yabiyosa suka jera kowa na Sauke Ajiyar rai Imran acikin Ransa yana Fadin Waye Sagir a wajena..? Sagir Dan"uwa ne kuma Abokina aminina wanda bani da kamarsa acikin Wannan Duniyan ya Zauna Dani Da Dadi ba Dadi duk abunda na Zama yau ko na Taka da Gudummuwarsa Abokina Wanda Samun Irinsa sai an Tona Inda Haka abokai suke kamar Sagir da Mutane da Dadama sun ji Dadin abota bazai Kirasa aboki ba ya Zama Bangaran Dan"uwansa da Kokarinsa akaina bazan Taba mantawa ba. Sagir kuma Tuna Alheran Imran yake a garesa Duk da yana da Murdaddun Halaye ammh shi ya Fi kowa Fahimtarsa yana da kyakyawan Zuciya da Tunani mai kyau mai Kirki ne kuma mai Nagarta ne bai Taba Haduwa da aboki kamarsa ba ya wuce aboki ya wuce amini Shi din Dan"uwane a Wajensa Suna wannan Sake saken suka isa Bakin Titi Cikin Sa"a Sagir ya samu mai adaidaita sai ya juya ya mikama Imran hannu sukayi musabaha yana Fadin"Ka koma ka bar Min kanwata ita kadai..Kuma Mallam ka Sauke wannan Ego din naka da wani Kukan ka agefe in ka koma ka Lallasheta Ta Daina kuka Haka ango kema kowacce Amarya sannan Tell Her sorry Kazanta Tabini Bashi Khalil gabadaya Nauyin ni ya Doramawa kuma yana kaina Zan Biya bashi..! Imran kallonsa kawai yake bai ce komai ba sai da ya gama yace"Shirme..! Yafada yana wani Dakuna Fuska,Sagir ya Daki Kafadarsa yana Fadin"Ko da yake na Tuna..Ranar Lallashin bata zo bane ko Imran..? Yafada cikin Dariya Shima Imran din Dariya yake suka Rumgume juna Kowa na Dauke Hawayensa Imran ya Dago yana Jinjina Hannun Sagir lokaci Daya yana Fadin"Tanque....Nagode kwarai..Bansan da wani baki Zan gode maka ba..! Sagir yace"Ni bana Bukatar Godiyarka mallam abu Daya zakamin..? Imran ya Kallesa yana Fadin'menene shi..? Sagir yace"Ka so kanwata..Ka bata Kulawa kuma don Allah kada ka bari wannan Girman kan naka ya Bata Wahala..! Yafada yana Dunguremai kai Dariya suka saka