Sashe 14
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Tana cikin wannan Tunanin Taji sallamarsa Cikin Muryansa din nan mai Cike da Amo da Haiba kamar ta Dan"uwansa wanda yasa sai ta waigo da Sauri Tana kara ware idanuwanta akansa Cikin Bugun Zuciya ganin ya Duka Ya Cire Takalman kafarsa sau Ciki ya Fara tako laulausan Cafet din Daya malale Dakin da Safarsa yasa ta Tabbatar ma kanta Shi kadai ne Ba Hasashenta bane kanta ta maida kawai ta Cigaba da jan Casbahanta Lokaci Daya Tana amsa Sallaman nashi a saman Labbanta.
Gabanta ya kariso ya Zauna yana Tankwashe Kafarsa Dogon Namiji ne ingarma mai Zati da Haiba,Akallah a Shakarunsa bazai wuce 65 haka ba,Fari ne Fatarsa mai Cike da Jin Dadi da Hutu kallon Farko zakamai kasan Jininta ne saboda yadda karan Hancinsa ya Fito Zur akan Fuskarsa.
Yana sanye Cikin American Suit Ruwan Toka ya Daure Wuyansa da Tektie, *BARRISTER KABIR HAMISU DUKKU* kenan Babban D'a na farko Wajen Daada(Maryam)
Mirmishi ya sakar mata kafin ya saka Hannunsa ya Riko Tattausan Hannunta da suke Tubus dasu Saboda Samun Hutu da kuma jin Dadi yace"Haba DAADA..taya baki da lafiya kuma ke baki kiramu ba kuma kika Hana Baba asabe kiranmu..?
Yafada yana Kafeta da Kaifaffun Idanuwansa kamar na Mahaifinsu marigayi mallam Hamisu Dukku,gabadaya ya"yan nata Zaratan mazan Duka idanuwan mahaifinsu suka Dauko Gwara ma matan sun Dauko nata Idanuwan.
Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin ta Zame hannunta Carbin Dake hannunta ta ijiyeshi nan Gefenta saman Darduman Datake kai Cikin Muryanta mai Cike da Amo da Tsufa adan shake tace"To kabiru ko na kiraku me zakumin..? Ina da mganguna nasha..Daman jiri ne fa kawai DanaTashi jiya da Daddare ya Kamani kuma zuwa yanzu kaganni Alhamdulillah..!
Girgiza mata kai yayi yana Fadin"Ba shi kadai bane Daada..Akwai wani abu..Duk kin kara Ramewa Daadarmu taya ya kikeso mu kwantar da Hankalinmu achan inda muke Zaune muna aiki da iyalanmu Ahalin ke kuma kina nan kina ta Fama da Tunanin Dayake Haddasa miki Ciwo..? Haba Daada ya kamata ki Fahimci wani abu Tunani da Damuwa bashi bane mafita ki kuma sani Bayan Malami kina da wasu ya"yam da Jikokin da suke Bukatar ganinki a Raye Cikin Koshin Lafiya!
Jin ya famo mata inda yake mata kaikayi yasa kawai ta Fashemai da kukan Data ke rikewa Tun Dazu Tuni ya Rikice Ya Rikota yana Fadin"Haba Daada.Don Allah ki Daina kuka..Kada nima ki sani kukan..!
Yafada Daidai Lokacin da Baba Asabe ta yi sallama ta sawo kanta Dakin Dauke da Faranti Mai Dauke da Ruwa da Lemo itama Kamar Daadan take sai dai Daada Zata girmeta ba sai dai ita Baka ce mai Jiki ammh bata da Tsawo.
Ganin Daaada na kuka yasa Bayan ta ijiye Farantin Hannunta gaban Alhaji Kabir ya Zauna tana Fuskantarsa tace"Lauya sai fa kunyi wani abu akwai..Kwanakin nan sam Daada bata samin Ishashen Barci..Koda yaushe sai dai ka ganta Cikin Damuwa ko wanchan Da Dr Madina tazo ta Dubata sai da tayi mata korafin Rage damuwa da Tunani..Kayi mata mgana kila ta Rage..Ka gayamata ta Taimakemu ta kwantar da Hankalinta muna Matukar Bukatarta..!
Baba Asabe ta karishe Fada itama Tana matse kwallah Alhaji Kabir bai samu Zarafin Mgana ba Baba Asabe ta Fita da Sauri Tana kuka yau in suka rasa Daada ina Zata saka kanta matar da Tayi mata komai na Rayuwa ita da Iyalanta Tun zamanin kuruciyarta Tazo gida nan a matsayin yar aiki Daada ita da marigayi mijinta sun mata komai a Rayuwa,Duka ya"yann Daadan ita ta Renosu Domin ita Allah bai Taba bata Haihuwa ba Duk da Auran Wuri akayi mata auran ta Biyu,Dayake ita yar Minjibir ne Dake Jahar kano.Kuma ba wani Cikakkun Dangi Tunda uwa da Uba Duk sun Rasu Da Taimakon wata Hajiya Lanti mai kai mata aikatau gari gari ta Sadata da wannan gidan..Gidan Alheri da karamci kusan Shekaru Arba"in da wani abu Tana Tare da Daaada da iyalanta bata Taba kukan wanu abu ba sai dai Taje chan garinsu Minjibir takai musu alheri Daga Cikin Alheram Daada da Ahalinta Dole ta Rika Shiga Damuwa in taga Daada a wannan Halin.