← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 190

Sashe 81

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Alhamis tunda sai 6pm suka Dawo Daga makaranta tun safe sun Wahala daga Newsite suka tafi Class Oldsite,gabadayansu sun dawo jikinsu na Ciwo shiyasa yau kowa ta wuce gida. Inteesar sai dai tayi wanka ta gasa Jikinta kana ta iya shan Ruwan Tea domin Karatu bai barsu sun Tsayama cin wani abu yau a makaranta ba. Kwance take kan gado Tun bayan data idar da Sallar Isha"i take nan Zube kamar kayan wanki tagaji kafafuwanta Ciwo suke mata sosai inda zata samu mai mata Tausa da taji Dadi sosai ido kawai take Lumshewa ga barci Tana ji ga gajiya data Lullubeta ta Saukar mata da kasala. Wayarta ta Dauko Data Tuna da wani abu Dazu suna makaranta ta Dauki Wayar Munari ta saci Lambar wayar Imran Bata sani ba Kwanakin nan bata ganinsa koda gidan taje ballatana ta Rage zuwa saboda Wuni suke Zungur acikin makaranta.. Haka kurum take son ta adana Lambarsa acikin Wayarta ko bazata Taba Kiransa ba Zuciyarta ta aminta da Hakan sai dai me..! Yadda ta kurama Lambar ido haka take ganin Gilmawar Fuskarsa ta cikin Wayarta,Kurama Fuskar wayar ido Tayi kowani Dakika jikinta na kara Saki Cikin yanayin kasala..? Meke Faruwa dani ne..? Bata samo amsar tambayanta ba Hannunta ya kubce ta Danna ma Imran kira batare data ankara ba da Sauri ta Mike tana Shirin kashewa sai dai me...? Kiran Tuni ya shiga har ta fara Ringing gabanta ya yanke ya kanta ta Dafe kanta Dayake Saramata Jikinta ya Fara rawa bata da kwanan Amin taji ya Daga Kiran duk da kuwa Bai Taba Daga Bakuwar Lamba ba. Yadda take kwance Tana Tunaninsa Haka shima yake kwance yana Tunaninta Sai dai shi yana Rage ma kansa wasu abubuwan in ya Busa Sigarinsa yanzu ma Tabance a Hannunsa yana Busawa cikin kwarewa yana Kwance ya Kishingida da Filo,Dagashi sai bakin dogon Wandojikinsa bako Riga kwantancen Gashin Kirjinsa mai Santsi ya kwanta Sai kyalli yake.. Yayi mamakin ganin bakuwar Lamba Tana Kiransa shi ba wanda ya sani masu Kiransa Daga Sagir sai Yusuf acikin Contact din nashi ma Kwaya uku kadai garesa Daga ta Yusuf sai ta Sagir sai ta Munari ita da bai cika Kiranta ba sai Lambar Baba Manu kuma ya Dade da gogeta Tun sanda ya gama amfani da ita. Da farko kamar bazai Daga ba sai Zuciyarsa taki bashi Daman haka haka Kurum yaji ta Rinjayesa ya Daga Kiran sai dai bai yi mgana ba yayi Shuru yana Sauraran Bugun zuciyar Inteesar da yadda ta Dafe Kirji Tana Ajiyar Zuciya. Mamaki ya kamashi jin an ki mgana kuma yana jin Saukan Numfashi acikin kunnuwansa Ransa ne ya baci ya kashe wayar batare da yayi mgana ba Inteesar ta Rumgume wayarta Tana jin kamar Imran ta Rumgume saboda yadda Saukan Numfashinsa yasa Taji ta kasa Controling kanta. Zama ta gyara ta sake Kiransa bai Dauka ba Sai da ta kara Kira kana ya Daga Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Ko waye ke kirana yafadamin kai Tsaye.. kada ya bari Raina ya baci na Bincikosa da kaina..! Yafada Cikin Kaushinsa kamar yadda ya Saba maimakon tace wani abu sai taki ta Damke bakinta Tana Dariya Farinciki ya cikata dataji Muryansa ganin an ki mgana yasa ya Dago Wayarsa yana Bin Lambobin da kallo acikin Ranshi yana Tunanin wanene? Bai samu amsar ba yaja karamin Tsaki ya datse kiran Lokaci Daya Da kashe wayar nashi gabadaya Zai iya Zuwa Mtn office kan wannan lambar ya Tsani arainamai wayau,kuma abun da ba"a tabamai ba Dole wani wanda yashanshi ne ko dai Sagir ne...? Anya shine kuwa..? To in bashi bane Waye? Yusuf dai basa irin wannn Dashi Kodai Munari ce..?ai ita yana da Lambarta To kodai kodai yarinyar nan ne Mara jin mgana..? Zai iya Zama itace saboda yaga ta fara Rainasa Mirmishin Saman lebe yayi ransa ya tabbatar da itace ba wata ba zai bita a sannu zai kamata. Ita kuwa yana kashewa ta saka Dariyan jin dadi acikin ranta tace ko bazai daga ba zata kirasa sai dai ta kara kira wayar tana kashe,ta kasa Samun shi,sai ta Hakura zuwa Gobe ta maida wayarta ta ijiye ta koma ta Kwanta Hannunta Rumgume akirjinta,Bata Dade da ijiye wayar ba sai kira ya shigo wayarta da Sauri ta dauko da Murnan ko Imran ne sai taga Khamis ne karamin tsaki taja Lokaci daya tana ijiye wayar Wani Takaichi yana kara kamata bata san Dalili ba ta tsani Khamis din,Sau daya ta taba Daga wayarsa bata Kara ba data Fahimci shine achart kuwa ya Tura mata sako ba adadi bata taba Budewa ba. Messages kuwa ta waya ya turo ba adadi bata taba Budewa ba Bashi ke gabanta ba ita Mu"amala da ya"yan Mami Asma"u kwata kwata bazata iya ba Saboda basu da hali mai kyau har gwarama Umaima,ammh Sajidan nan ai tafi kowa Iskanci tama fi Uwarta Komai ta Damata ta Shanye,haka shekaranjiya Hafsah ta Kirata tana Fadamata Wulakancin data kirata ta mata saboda ta yi adding dinta a group din data Bude musu na mata Zallah Shine ta Fita ita kuma ta sake adding dinta shine ta fita ta Kira Hafsah a waya ta fada mgangun marasa Dadi kan kada ta kara adding dinta saboda ita bata da wannan Lokacin kuma ita ba sa"arta bace da zata Zauna tana wannan Shirmen kada ta kara mata haka bataso Daga haka ta kashe Wayarta ta kuma Sake Fita Daga group din Hafsah na gayama Inteesar taji Takaichin ba ita Sajida ta Kira ba da ta gane bata da wayau da sai ta Raina kanta ta rika ma Hafsah Fadan meyasa ma ta Sakata aciki..? Abu ne na Zumunci ba Dole aciki wanda ya dama ya shiga ayi dashi wanda bai ga Dama shi ya sani,ba wanda ya kara bi ta kanta su Anty Hauwa dasu Aneesa suna cikin Group suna Haduwa ayi ta Hiran Zumunci Inteesar ta kan Jefa mgana Daya biyu ba sosai ba. Tana cikin wannan Tunanin ne taji karan Shigowar sako Bata ma yi kokarin Dubawa ba,saboda tasan ko waye sai da asuba ta duba Khamis ne Yana magiya ta Daga Kiransa Tsaki Taja ta Share duka Sakonninsa bata ma Tsaya karanta su ba. Allah yasa basu da Class din safe shiyasa tasha barcinta ta Huta sosai sai 12pm suka shiga cikin makaranta ita da Munari,achan ma makaranta Haka Khamis yayi ta Kiranta taki Dauka Har yabama Munari tsausayi ta Roki Inteesar data Dauka tace mata Wlh bazata Daga ba sai ta Kyaleta.. Tundaga Ranar Inteesar ta samun Abun yi duk dare sai ta Kira Imran ko da bazai dauka ba sai dai yana Dagawa Dukkansu suyi shuru suna jin Numfashin juna,Har ya gaji ya katse Kiran sai ya kashe kiran Tayi da Dariya ita kuma batasan ya ganota ba Ya karbi Wayar Sagir ya saka lambar ya yana Danna kira sai ga Sunan Inteesar sai ga Lambarta ta bayyana Mirmishin Saman baki yayi shi ya sani itace ba wata ba.. Yarinyar nan ta rainashi wlh ammh zai yi mganinta Sai da sukayi wajen Sati Daya tana kiransa Ranar tana Kira ya daga tayi Shuru taki mgana shi kuma cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Yarinyar nan kin rainani ko..?! Ni sa"an wasanki ne da zaki rika kirana kina kin mgana..? Cartoom kika maidani ko karamin yaro irinki..? Yafada mata Cikin Kaushinsa Koda yaushe Tsoro ya kamata ya akayi yasan itace sai ta fara Kifta ido ta rasa abun cewa Mirmishi yayi kafin yace"Kina mamakin ya akayi na gano ki ko..? Duk abunda Imran yaci alwashin sani sai ya sani..! Kifta ido take yi kamar yana gabanta ta kuma kasa cewa komai Yasan daaman bazata iya mgana ba Ganin haka yasa yace"Oya jeki kwanta Tunda baki da abun fada..Ki daina Kirana kiyi Shuru bakya iya mgana Am not a Child kamar ki ok..! Daga haka ya datse kiran Yana Mirmishi har cikin Ransa baisan meyass ransa bai baci da duk Abunda take yi mai ba sai ma Nishadi Dayake jinsa Ciki. Ita kuwa yana Kashewa ta Fada kan gado tana Sauke Numfashi kamar wacce Tayi gudun Tsira,afili ta Furta"ya akayi ya gano ni..? Na bani..! Take fada tana Dariyan Nishadi. Tunda ga ranar bata kara Kiransa ba ya dauka ba sai dai ta Kira data shiga sai ta Katse kiran,ko kuma Daya Dauka sai ta kashe Imran baisan meyasa ba baya damuwa da abubuwan da Inteesar keyi da wani ne kemai Rainin wayau nan bazai Dauka ba sai gashi ita tana yimai bai taba Daukan wani mataki ba in ta Dameshi sai ya Kirata sai ta Dauka taki mgana Shi kuma sai yace"Kin raina ni ko..? Oya ki je kiyi karatu ki kwanta bana son wannan Shirmen.!.daga haka zai yanke kiran ko ahakan aka Tsaya He make her Night sosai,shima ana shi barayin hakane. Ta dubasa a Wsop taga bayayi saita koma Turamai sako ta Messages sai tana Zaune ta Turamai sakon"Ya Imu kaina na ciwo..? Ya imu ina jin yunwa..? Ya imu kana ina..?kaci abinci..? Allah yasa yau baka sha sigari ba..? Na dawo makaranta nagaji Ya Imu..? Yarinta kala kala take Zubamai mai shi kuma ya kasa Dakatar da ita in ta Turomai sakon zai karanta baya ce mata komai sai tace mai ta dawo makaranta ta gaji kanta na Ciwo sai yace mata tayi wanka tasha mgani ta kwanta,in ta Tambayeshi yasha Taba..?sai yace mata Eh yasha Koda Ranta zai baci sai ya gayamata Gaskiyansa Shiyasa yake kara Burgeta Dukkansu sun Shiga Tarkon son juna batare da sun sani ba. Ranar asabar basu da makaranta Tunjiya data dawo daga makaranta Taji Cikinta na ciwo kadan kadan sai dai bata maida kai ba bata taba Tunanin Period pain dinta bane yadawo mata wanda abaya Tana Fama Dashi sosai in zatayi kamar ta Mutu to Tana karban mgunguna sai abun yayi mata Sauki sanda Tana Kaduna sai ta shafe wata Uku Tana Period batayi mugun ciwon maran nan ba sai dai kadan kadan wanda bai Shahara ba Shiyasa ko Mama bata taba sani ba kuma ganin Tunda tazo bata Taba yi ba ko sau daya ba sai Mgungunanta wannan Hutun data koma gida ta maidasu. Abun yana mata Kadan kadan ne yasa bata Dauka zai yi Tsanani ba Ranar ita tayi duka aikin gidan,Tace Mama ta Huta Jinin bai zo ba sai Zuwa Dare,Munari bata zo ba
Chapter 81 · 0% Book details