Sashe 185
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama Gabadaya Kamfanin Marhaba suka zo suka kawata Bangaran sai wanda ya gani. Wannan Karon Mami Asma"u da Umma Baffa Kabiru ya bama Kwangilan Hadama Zaratan Mazan kayan Lefe,Mami Asma"u ta bada Shawaran su tafi Dubai su Hado komai haka kuwa akayi Dubai suka Tafi Harda Maman Nasara Saboda Tasan Wajen Tana zuwa Saro kaya Sati Daya sukayi suka jiyo da akwatuna Saiti Biyar cike da kayan alfarma,Dayake kafin su Tafi sun karbi Size din Ya"yan nasu A Abuja suka Sauka nan suka Fara baje kayan Baffa Kabiru yace nan Za"a Barsu Dasu Za"a Tafi Dukku Zai Dinka musu wasu kayan Fitan Bikin na Dabam Abun fa nayi ne Bakin Aljihu kadai ya Saki su Umma na amsa suna ta Shirinsu Daga Mazan har matan kala Biyar Biyar yayi musu na kayan Fitar Biki,Harda Abba da Mama suma Baffa Kabiru bai barsu abaya ba. Ana Saura Sati Biyu Biki Inna Maimautu tazo ta Hada kan Amaran Waje Daya ta tafi dasu Bauchi ta gyara su Inteesar harda kukanta taso taje Imran yace Ya Hakura da gyaran iya wanda ke Jikinta ma ya Ishesa jin Dadin in tatafi shi kuma ya Zauna da wa..? Dole ta Hakura Tunda Oga ya Hana ammh Kullum suna waya dasu suna Fadamata yadda suke shan gyara Ana ta Musu Dilka da kayan gyara na Da"a Daga Sokoto Inna Maimunatu ta bada Sako aka Kawo mata tana ta gyaran Ya"yanta. Mazan suma suna nan suna ta Shirinsu na kece Raini Imran dai Na Gefe bai Zakewa yace shi Babban Yaya ne sai dai Shawara ko bada Umarni sun Dinka angon Fitar Bika Kala Hudu Hudu wannan kuma Gudummuwar Yusuf ce yayi musu Gabadayansu har dasu Ya Basheer dasu Abba Ranar Daurin auran gabadaya ankon Farar shadda Zasu saka,,Manyansu da yaransu Matan ma sun Fitar da wani less shima mai kyau na Yinin Biki Hatta Daada ba"a bari a baya ba ya"yanta sun Dinka mata ita da Baba asabe.. Ana Saura Sati Daya Bikin Hajiya Barira da Sairan ya"yanta suka Sauka akano Fagge ta sauka agidansu Chan itama Zasu yi Taronta Dr.Ali argungu sai Saura kwana Uku zasu iso da Khalil sai bayan Biki zasu Tattara su koma Lagos har da Amarya Sajida. Da yanzu taji Sauki sosai kamar bata Taba Wata Cuta ta bar makaranta Saboda Daman ta rasa Shekararta ta Biyu Dole baya Zata dawo in taje Chan Lagos tace ma Khalil in Ta koma Cjan Zata Dora Daga Farko ne Tunda Lokacin ya gabato suna ta Shirin Tafiya Dukku ne bayan an gama Jerin Dakunan Amaram Daman kamfani ne suka zo suka jera komai sai abun da ba"a rasa ba Matan suka shiga Kasuwa suka kara musu Sajida ita sai sun isa Lagos din za"a siyamata komai Munari kuma bata Bukatar komai Saboda Gidan da aka bama Khamis achan Porthercourt akwai komai na More Rayuwa sai abunda ba"a Rasa ba Hafsah ce aka kawatama ta Shashenta Balle ya Hadu da Sabon Tsararran Ginin da Sagir ya Narka Dukiya aka narka mata Mama Tana Sabon Shashen mai Dauke da Bedroom guda Daya Kafin itama ta Tashi Zuwa Gidanta Inda Abba ya gama kawata mata. Tun ana Saura Kwana Uku Taron Bikin Matan suka Fara Sauka Adukku Inna Bintalo da Tawagan ya"yanta Inna Maimunatu itace ta iso da Tawaagan Amaran da suka Sauya Saboda gyara ko"ina suka Gitta sai Tashin Kamshin Fatarsu na Santsi da yarari,Ranar al"amis Sauran suka Iso Umma da Mama da Tawangansu Maman nasara da Anty Uwani sai Mami Asma"u da Umaima da suka Taho Daga Abuja. Inteesar Tawagan su Anty Safiya ta Biyo Ita dasu Anty Aneesa da Anty Faresatu da Tasleem sai Inna Kaltume matar Baba Manu, Nasara tana chan Daga Kaduna tabi su Umma,Mommy Tana Fagge su ke da Taron Bikin Bangaran Uwar ango Khalil Hajiya Barira. Tawagan angayen kuma Sai Ranar Jumma"a suka iso gabadayansu Yaransu da Iyayen Ciki Harda Kawu Manu da Alhaji Alhassan da Dr.Ali Argungun da suka iso kano Tun Ranar Laraba a Kaduna suka Hadu gabadayansu suka Dunguma suka kamo Hanya gabadaya sai dai aka Rufe Gidajen. Aranar da Yammah sukayi Fulani Day a Aharaban Gidan Marigayi Alkali Hamisu Dukku,Shigar Fulani gabadayansu sukayi matan su da Mazansu sun siya kayan banda su Abba Da suke gefe suna Kallon yayan nasu Cikin Alfahari Harda Daada sai da Ta Fito Bakinta yaki Rufuwa bata taba ganin Ahalinta sun Hadu waje Daya ba Tashin Hankali ba sai yau Ga Mami Asma"u da Yan"uwanta duk sun zo sai Shiga da Fita suke yi suna Raba Damammiyar Nono da Fura mai kyau da Aka siyo da yawa saboda irin wannan Ranar kowa kagani yana Cikin Farinciki,Amaren suna Waje Daya suma sun Cakare Cikin kayan Fulanin Kamar yadda Inteesar ma ta saka nata sai dai ta kara kiba Ciki ya Budata Kana ganinta Zaka Fahimci Tana da Shigar Juna Biyu Imran na Tare da ita yace ta kama Girmanta Duka wajen itace yayarsu har su Sagir da Khamis sudai Dariyansa kawai suke shi ala Dole sai an basa Girma ko ana so ko ba"a so Inteesar kuma Tana so ta samu Sake cikin Yan"uwanta susha Firansu Dukkansu achan akayi musu Kunshi da gyaran kai Sajida data maida Jikinta sai Walwali Take Bini bini kadan Tazo ta kawo karar Khalil wajen Babban yaya in yayi mata wani abu Shi kuma yaja kunnensa in kaga wannan ahalin Aranar sai sun baka Sha"awa kayi Musu Fatan zama cikin Farincikin nan Har karshen Rayuwarsu Sai wajen goma Dare suka Tashi Taron suka koma Cikin Gida Mazan Matasa da Su Abba duk suna BoyQuaters da aka Riga aga gyarashi Tsab. Gari na Wayewa suka Tasshi da Hidiman Biki da Daurin auran suka Tashi Gabdaya Girke Girken duka su suka Zage sukayi kayansu Kala kala sai wanda ka Zaba ballatana ga Dangin Uban Hafsah suma da Safen suka iso Harda Mijin nata da yan"uwansa hakama Mijin Inna Bintalo Gida dai ya Cika Sosai Gwanin ban Sha"awa. Da wuri gabadaya akayi wanka Kowa ya Cakare gabadaya matan Shigar iri Daya sukayi na Less din nan Amaran suma Shigar iri Daya sukayi suma na Less ammh kalar nasu dabam Harda Inteesar itama kamar amarya Domin tasha Kwalliya an Kashe mata Dauri kamar Amarya sai dai ana ganinta anga mai Matashin ciki. Mai kwalliya suka Kira tazo Tayi musu Daada ma ta Ci Wakanta Itama su Inna Maimunatu sun kashemata Dauri sai Hoto suke Daukanta Bakinta yaki Rufuwa. Mazan suma suna chan duk sun Shirya Cikin Fararan Shadda Kowa kuma da Babban Riga da bakar Hula da bakin Takalmi da bakin Agogo,Harda iyayen suma Shigar sukayi Harda yara irin su Waleed da Abidin Daurin auran karfe 12pm na Rana ne da an Daura za"ayi Walimar maza a Wani Restauranta inda zasu ci Abinci Matan kuma nasu sai gobe ne Lonching zasu Gudanar. Daddy shi ya bada auran Duka ya"yan nasu Hafsah da Sajida da Munari Saboda Dangin Mahaifin Hafsah sun yi musu kara sosai,Dr Isa Argungun Yayi ma Alhaji Alhassan kara shi ya Nemar ma Khalil auran Sajida yayinda Baba Manu ya karban ma Sagir auran Cikin Kankanin Lokaci Aure ya kamallah yayinda Baffa Kabiru Shi ya Biyama Duka Zaratan Mazan Sadakin Dubu 200 ne. Nan da nan Masallacin ya Kaure da Hayaniyar fatan Alheri ana ta gaisawa da Mutane da angwayen da ba"a gane su Tunda Duka Shiga iri Daya sukayi Daganan Reception sukaje sukayi koda suka dawo har an Fara Lonching din Daman mata da Maza ne nan da nan kowa yaja Amaryansa Gefe,Imran mamaki Yaran ma suke bashi sai Wani Rawan kafa suke Saboda sun yi aure ba su Munarin ba Su Sagir din ba Shima Inteeear yaja Gefe suka kame afili ya Furta suma ai angwayen ne Dole suma su Cakare. Anci an sha an yi Rawa sosai Sagir da Khalil da Khamis sun kwaso Shoki Abunsu da matansu Imran na Gefe yana kallon Abun mamaki ko kunya Cikin yara Inteesar sai Fushi Take yi Tana so Ta shige aammh Imran yayi mata Jam ido Yace bai son Iskanci da Cikin nashi ne Zataje Tana Girgiza kuma sannan baya son Shirme ta barma yara Dole ta Hakura Tana Gefe Tana kallo sai dai sunje a manya yayyi kamar yadda Imran yake so sun yi manni kudi an sha Hotuna kamar ba Gobe Kowani Hoto Sai an gawayen sun Rike Imran anyi dashi dasu Amaran sai Dai Fuskarnan ba Fara"a ko kadan su Ya yusuf suna Gefe a Mtsayinsu na manya yayyi. Washegari Aka yi Walimar aure anan Haraban Gidan da Yammah,Ranar Litini kuma akayi Shirin mika Amarre Hafsah Kano Za"a kawota ita da Sajida Munari kuma Abuja zasu wuce ita da Khamis dasu Mami. Inna Bintalo Zata Bisu Abuja Inna Maimunatu zata je kano su Da su Umma Domin mikama Mama itama Gidan Auranta. Daganan Dukku Iyayen mazan sukayi Sallama da juna bayan Daada ta tarasu tayi ma Duka Ma"auratan Nasiha da zasu tafi harda Kukanta Domin Tana ganin kamar Kara Haduwarsu na Mutuwarta ne. Masu Tafiya Kano Duk Tare suka Dauki Hanya Wajen Motoci Goma Sajida Tayi kuka wajen Rabuwa da Mami da Baffa Kabiru da sauran yan"uwanta Munari ma Tasha kuka ita da Inteesar haka ta kamkame Abba Da ya Yusuf Harta da Imran sai da idonsa ya Sauya ya Rumgumeta yana Shafa kanta Daga Dukku Jirgi suka Hau zuwa Abuja Ita da Inna Bintalo dasu Mami. Suna isowa kano Mama aka Fara Rakawa Gidanta Shashenta Sai son barka Rakiyan Umma da maman nasara da Anty Uwani da Inna Kaltume Sajida kuma Mommy da Anty Saratu suka Tarbesu,Aranar suka Tafi Fagge ita da Khalil da Umma,sai Gobe zasu bi Jirgi zuwa Lagos Inteesar bata raka Ko Dayansu ba sai Hafsah,Ita da aka kaita Kusa Inna Maimunatu ta mikata Dakinta Tana ta kuka ba wanda suka kwana Kowa ya watse sauran baki suka koma gidan Abba wasu kuma Gidan ya Sadam suka koma suka kwana. Washegari Talata Kafin su Khalil su wuce sai da suka Biyo Tanan sukayi Sallama da yan"uwa Kafin su Dunguma Gabadaya aka Rakasu Filin Jirgi Zuwa Lagos Umma da inna Maimunatu ne zasu Raka Sajida sai yayar Mami Asma"u Guda Daya. Inteesar Tasha kuka Data Waiga ba Munari tana chan Abuja Allah Sarki Rayuwa Imran ne da suka koma Gida Yayi ta Lallashinta Tun aranar gabadaya Kowa ya watse aka bar