← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 190

Sashe 92

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da asuba gabadaya mazan suka tafi sallar asuba a masallaci,Imran yayi ta nuku nuku har sai da suka tafi suka barsa kana ya taho daga baya daman dasu ne bayasan jerawa yusuf daya san Halin dan kayansa bai ko bi ta kansa ba ganin jiyan bai yi wani barcin kirki ba Farkawa Goma sai yaji motsin Imran yana sakin Tsaki shidai bai bi ta kansa ba ya bararraje yana ta kwasan barcinsa Hankalinsa kwance. Da suka Hadu da Sagir a masallaci Yayi mamakin ganin Imran bai hada Sahu da Ahalinsa ba Layin baya yaje abunsa,kuma ana idar da Sallar shi ya Riga kowa ya fita,Fuskar nan a Hade kamar wanda aka aikomai da wani mumman sako da asuban Fari. Sagir ya tsaya sun gaisa da su Abba yaga Baffa Kabiru ya kara Jinjinama kansa Lalle su Imran din yan Dangine gaba da baya. Koda suka koma Gida Imran ya Shige Dakinsa ya kulle ya Haye gadonsa Yusuf dariya ta kamasa Daman duk Saurinsa kenan bai damu ba ya Shige Dakinsu Sadam suna Hira Abba ma Dakinsa suka Shige suka cigaba da Tattaunawa Tsakanin yan"uwan da suka Fito Daga Jini Daya sai Allah. Mata matan kuma suma suna Sallar asuba basu koma barci ba suka Fito zuwa Kitchen Safiya da Tawagar yan matanta Inteesar,Munari da Hafsah,Sai su Aneesa da Fareesatu da suka ce suma bazasu zauna ba,sai suka mikama Mazan nasu yaran nasu su kuma suka Fada Kitchen suka Fara Kokarin samar da abun karin safe da Wuri tunda akwai Tafiya agabansu. Ruwan Tea suka Fara Dafawa wanda yaji Citta da kayan kamshin Shayi sai Suka Fere dankali suka soya da kwai suka kuma yi pancake,Safiya ta bada Shawaran suyi kunu da kosai Saboda su Abba nan da nan kuwa daman Tana da garin kunun da Mommy ta aiko mata dashi,suna da Sauran Nama a Fridge da kayan ciki suka Hade su sukayi Ferfesu kada su bar gidan zuwa Dukku kafin su dawo ya Lalace. Soyan kosan ya zama na Karshe ne bayan sun gaggama komai,Safiya Da Aneesa suna tajera komai Cikin kololi ita kuma Fareesatu tana ta Jera Mug,da Filet filet da Fork iya adadin mutanen da zasu yi Amfani dashi. Inteesar da Munari da Hafsah sune ke wajen soyan kosan,inteesar na dagachan gefe saman Cabinet din kitchen din ta Haye daga Sama Sanye take da Rigar barcin munari doguwa mai Ruwan madara,mai taushi sai dai saboda Munari tafi ta kiba sai Rigar tayi mata yawa kadan karamin mayafi ne a saman kanta ta dan Ratayeshi. Hafsah ce ke gaban Kaskon Suya ita kuma Munari na ta faman buga Kullim kosan suna yi suna Hira Jefi Jefi. Ba wanda yaji Shigowarsa Saboda gabadayansu Hankalinsu nakan aiyukan da sukeyi ne kuma suna Hira kuma Dayake Sallamar nashi iya Saman lebensa ne ba wanda ya Jisa. Anty Safiya ce ta ganshi Lokacin Dayake Bude Fridge ya Dauko goran Ruwa mai Sanyi yana sanye da Jallabiya mai ruwan madara,wacce bata kai kasa ba sosai Fararan kafafuwansa masu cike da gargasa suna Waje ne. Ganin sun Hada ido da ita yasa yace mata"Ina kwana..! Yafada yana dan Daga idanuwansa yana Karema wadanda ke Kitchen din kallo ta kasan Idanuwansa. Safiya tayi mirmishi Lokaci Daya Tana Fadim"Lafiya lau Imran mun tashi Lafiya..? A saman lebensa ya amsa daidai Lokacin da suka Hada ido da Inteesar wacce ta Kuramai ido tana kallonsa cike da wani Shaukin da bata san dashi ba,Kowa ya juyo yana kallonsa ganin haka yasa Munari ta gaisheshi Hafsah ma haka su Aneesa ma suka gaisheshi ba domin ya isa ba sai Domin yana da kwarjini da cika Fuska uwa uba kuma Oga Imu ne da kansa ai baza ka jira sai ya gaisheka ba.. Tundaga gaisuwar Farko bai kara amaawa kowa ba ganin haka Inteesar taki gaisheshi,Sai ma wani lamgwabe kai datake yi tana kallonsa Shi kuma Gabansa ne ya Fadi ganin saman kirjinta yana waje ne,Kuma Rigar bata da wani kauri ga Shatin saman Nonuwanta nan ta waje Jikinsa ne yaji ya fara rawa yasa ya juya zai Bar Kitchen din dauke da goran Ruwan a Hannunsa. Daman Inteesar tana ta gefensa ta bangaran Fita ne,ita bata sani ba yazo fita sai ta zuro kafarta ta taba mai Cinyarsa da sauri ta janye tana kallonsa kankance idanuwansa yayi yana kallonta kafin yace cikin Sanyin Murya."Ke kin raina ni ko..?kowa ya gaisheni ammh ban dake ko..? Noke kai tayi tana yar dariya kafin tace"Ina kwana..!Mirmishi kadai yayi na gefen baki yana Ficewa Daga Kitchen din bai ce komai ba. Yana Fita Munari da Hafsah da suka ga komai suka Juyo suna kallon Inteesar dake Dariya kasa kasa suka kalli juna suna rike baki tana juyowa suka Hada ido da ita,Ganin yadda suke kallonta yasa ta bata rai ta wani Hura Hanci Dariya suka saka Harda Tafawa ita da Munari Hafsah tayi ma Munari Rada a kunni tana Fadin"Yarinyar nan akwai munafuncin datake Boye mana..! Hafsah tace"Barta..Kuma zasu dace da Masoya..! Suka kara Kyalkyacewa da Dariya Inteesae ta tsargu ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"Anty Safiya ga su Munari nan basa aikin da kika saka su suna ta Gulmana..! Anty Safiya ta waigo Tana Fadin"Kuyi dai ku gama lokaci yana tafiya..! Da toh suka amsa ita kuma Inteesar tana yi musu gwalo,su kuma suna ta Hararanta tana Dariya sama sama. Cikin Lokaci suka gama komai su Inteesar suka je sukayi wanka Domin sunce bazasu iya Karyawa basu yi wanka ba,jin haka yasa suma suka Shiga Domin yin wanka suyi ma yaransu kafin su Abba su fito. Karfe 9:00am na Safe kowa ya Hallara a Falon saboda Breakfast,An shimfida Katuwar Darduma anan Tsarkar falon su ka jera komai asamanta. Sai da kowa ya Hallara banda Imu,Har an fara karyawan Daddy ya Dago yana kallon Yusuf kafin yace"Ina Dan"uwa yake Yusuf..? Yusuf na Kurban Tea dinsa yace"Baffa yana Cikin dakinsa..! Ya kada kai yana Fadin"Meyasa bai fito ya karya ba..? Yusuf yace"Bai cika cin wani abu da Safe haka ba kila sai chan da Rana..! Kada kai kawai yayi bai ce komai ba Mami Asma"u na gefe aranta tace gwara hakan ma Domin Tun abunda ya faru jiya Tsagerancin yaron yayi mata Tsaye a saman kanta. Inteeesar dake gefen Hafsah zaune ta Dauko Wayarta ta Shiga Messages ta Turama Imu sako. "Ya imu kafito kayi breakfast..! Ba dadewa ya maido mata da amasa. "Bana jin yunwa..am ok..! Inteesar na ganin haka ta Turamai da Sauri. "Saboda ka cika cikinka da Hayakin Sigari ko Ya Imu..!? Sai da yadan jima kafin ya bata amsarta,Tama kasa cin kosan dake gabanta Hankalinta na kan wayarta. "Eh..! Kawai yace mata Mirmishi tayi tasan bazai mata karya ba Tunda yace Eh to yasha ne,sai ta Rubutamai. "Kana so ka mutu ne Ya Imu..? Da sauri ya maido mata amsa wannan karon. "Eh in na mutu Who care..!? Tana ganin haka sai da gabanta ya Fadi da Sauri ta Rubutamai. "Ni mana..Zan ta kuka nadaina cin abinci har nima na mutu..! Yana kwance ne yaga sakonta sai da ya Mike zaune yana sosa goshinsa afili ya Furta yarinyar nan akwai Rigima. Amsa ya bata da cewa"bazaki mutu ba..! Tana ganin haka da sauri ta maidamai da amsa. "Zan mutu mana indai kai ma ka Mutu na daina ganinka Ya Imu..! Sai da ya dade bai Bata amsa mata ba har ta Fara sarewa sai ga sakonsa ya Shigo "Wayace miki zan mutu yanzu..? Oya eat ur Food bana son shagwaba am not in d mood..! Tana ganin haka sai da tayi Mirmishi akallah dai tasakashi yayi mgana batayi kokarin kara Turamai komai ba sanin Tunda yace baya cikin Mood din bazai kara cemata komai ba Tana kallon Wayarta Tana Mirmishi ita kadai Hafsah data Tabo Munari Tun dazu suna ta kallonta ta dago suka Hada ido Hararansu tayi kafin ta Boye Wayarta cikin karamin Hijabin Dake Jikinta,Su kuwa me zasu yi in ba Dariya ba Har sai da kowa ya Juyo yana kallonsu Daddy dake lura da Inteesar tun dazu bataci komai ba sai Danna waya take yace"Intee ijiye wayar nan ki Karya..! Kanta a kasa tace"To Daddy..! Lokaci daya Tana Hararan su Hafdah dake mata Dariya kasa kasa. Basu wani bata Lokaci wajen Breakfast din ba,kowa ya tashi su Hafsah suka Tattara komai zuwa Kitchen suka fara wankewa,Su kuma su Anty Safiya suna ciki suna Shirya Tunda ance kowa ya shirya nan da 11am zasu dauki Hanya. Suna gama wanke wanken suka Gyara Kitchen din suka koma Daki Domin Shiryawa Munari ta kalli Inteesar Tana Fadin"Intee ya zamu yi da School yau..! Inteesar tace"Ya kuwa..? in mun dawo zamu yi covering din inda aka wucemu..!. Munari ta gyada kai alamun gamsuwa Inteesar ta kalleta tana fadin"Sai naje gidan Mama na Dauko kayana..! Munari tace"Basai ki saka nawa ba..!. Inteesar tace"A"a bazan iya ba sun min yawa salon na Dinga yawo aciki..! Hafsah ta saka Dariya ita da Munari Inteesar ta Hararesu bata kara cewa komai ba. Sai da ta jira su Munari suka Shirya tsab Munari ta Hada kayanta cikin karamar akwati kala Biyu da kayan barci Tunda basu san yaushe zasu dawo ba Inteesar tace su hada kayansu Waje daya Shiyasa suka Dauki akwatin kayan zuwa gidan su Mama su dauko na Inteesar su tsaya ta Shirya achan Tare da Umma suka Tafi zata leka yar"uwanta. Suna zuwa gidan Abun mamaki suka Iske Sagir shima cikin Shirinsa na Tafiya basu Shiga mamaki ba sai da sukaji Mama na fada musu Imran ne ya Kira Sagir yace su Shirya su tafi Dukku Tare. Umma dariya kawai tayi bata da tace akan Lamarin Imran ballatana Mama. A gurguje Inteeesar ta Shirya Cikin Riga da Sikat na wata atamfarta Codedubuwa mai kalan Blue da Fari sai tayi amfani da bakar jaka da Takalmi da mayafi baki ta Dauko Kayanta itama kala Biyu da kayan baeci sai kananun kayan da zata Bukata suka Hada kayansu Waje Daya suna Shirin fitowa Daddy ya Kira Umma yace su dawo ana Jiransu. Dole suka Fito da Sauri Sagir ya Tsaya Shagonsa yana sallama da yaransa,Su kuma suka tafi har da Mama data Yo musu Rakiya bakin kofar gida Tana ta addu"an Allah ya Kiyaye Hanya. Koda suka iso duk suna Haraban gidan ne,kowa cikin Shirin Tafiya Bangaram su Ya Basheer su Inteesar suka karisa suka gaishesu kana
Chapter 92 · 0% Book details