← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 190

Sashe 108

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haraban gidan suka iske su Abba Shida Daddy suna mgana suma sunci manya kayansu sun sha kyau sai Baffa Kabiru dake gefe yana amsa waya Khamis na kusa dashi shima wayar ce a Hannunsa yana ta Latsawa Suma sun yi Shiga mai kyau da Tsari. Tunda suka Fito Hankalinsu Abba ya koma kansu Zaratan SAmarin ya"yan nasu Imran duk ya Cinyesu akomai Kallo Daya zakayi mai kaga Tsabar Zati Haiba da kamala Uwa uba Kwarjini da wani baiwar Kyau da Allah yayi mai. Abba da Daddy baki suka Washe azuciyarsu suna Fadin Masha Allah ballatana Baffa Kabiru da Khamis da suka Saki baki suna kallon Imran Duk da bai saki Fuskarsa ba ko kadan ammh Kana kallonsa Zaka Tabbatar da wannan cikakken Namiji ne inda ake Kiran Maza masu sunan Maza. In bace maka akayi yana Busa Sigari ba akallo Farko bazaka taba yarda ba Saboda yadda kyansa ya Fito da kyakyawan Zati sukansu sun shaida Karyansu suce Sajida tafi karfin Imran Sai dai shi yafi karfinta ma sai dai in Akayi duba da abunda suke Dubawa din ba Domin wani abu ba. Har gaban Abba da Daddy Yusuf da Sagir suka Kaisa yana ta wani Fadin Rai Abba ya Dafa Kansa yana Sakn Mirmishin Farinciki Cikin Annushuwa yace"Allah Sarki Zuwaira Allah ya jikanki da Rahma ina ma Kina Raye yau kikazo kiga Imran din ki Zai zama Babban Mutum..! Gabadaya sai jikin kowa yayi sanyi jin kalaman Abba da kuma yadda Hawaye suka ciko Idanuwansa yayi Saurin maida su yana Jijjiga Kafadan Imran Lokaci Daya yana Fadin"Allah yayi maka albarka..! Daga saman Lebensa ya amsa da Ameen Hakama Daddy ya sakamai albarka ya amsa Kamar mai Ciwon baki. Sai Lokacin Khamis ya Kariso wajen ya bama Duka su Basheer hannu sukayi musabaha Daya Miko ma Imran sai ya Karkace kansa gefe kamar bai gansa ba Khamis ya karajin ya muzanta Da Sauri ya maida Hannunsa Bayaso wani Cikin su yaga wannan Tozarci da Imran ke nuna mai duk sanda ya Nemi wani Huldar Arziki ta Shiga Tsakaninsu. Koda Baffa Kabiru ya kariso Wajen Imran Saboda kada ya gaisheshi baya ya koma,kawai ya Saka Hannayensa Cikin Aljihun wandon Shaddar Dake jikinshi yana kallon kowa Daya bayan Daya yana jinsa yau din nan kamar bashi ba,Ga wadanan kayan Dake Jikinsa ba karamin Takuramai sukayi ba. Ganin Lokacin Sallah ya kusa ya saka duk sukayi alwala anan Haraban Gidan,Inna Maimunatu ta Fito musu da Botoci sukayi amfani dasu kana suka Rankaya zuwa masallacin Dake kusa dasu,Basheer da Sadam na Dauke da Dabino da goron da za"a Raba Kafin Daurin auran Imran kuwa Yusuf da Sagir na rike dashi kamar wani mai Laifi ransa ya baci da hakan ya Kallesu yana Fadin"Wai meye haka kuke wani Rirrikeni kamar wani Barawo..? Yafada yana kara Dakuna Fuska Sagir ne yace"Saboda munsan Halinka Za"a iya nemanka awajen Daurin auran nan a rasa..! Wani Mirmishin Takaichi ya saki kafin yace"Rubbish..Dilla Malamai ku Sakeni na Rantse da Allah in nayi niyyar Tafiya ba wanda ya isa ya Hanani..Daman bazan je ko"ina Saboda Abba Shi kadai ne yake iya Takama Ra"ayi Burki..So please let me go.Nasan abunda nakeyi.! Yafada Cikin bacin rai jin haka yasa Yusuf yace su sakeshi Tunda ya Fadi haka ba inda zashi sun sakeshi yana ta Hararansu kamar ya Dakesu haka yake ji ba karamin Cutar Rayuwarsa akayi ba wlh ayadda yake fama da kansa Din nan ace za"a kara Dauramai wani Nauyi..? Ina Wlh bazai Dauka ba su dai Daura auran ai Alhakin komai yana Hannunsa ne yaga ta yadda Zai zauna da wannan Shegiyar yarinyar mai kama da uwarta. Sai da aka idar da Sallar azahar kana aka kara Sanar da Daurin auran Daman kuma Tun safe Daddy yazo ya sanar da limamin masallacin akwai Daurin auran Jikokin Marigayi Alkali Hamisu Dukku. Mutane duk basu Tafi ba Daman masallacin ana cika sosai nan su Basheer suka tsshi suka Fara Rabon Dabino da Goro,suna gamawa aka Fara Gabatar da Neman aure Daddy shi ya Biya Sadakin Imran Naira Dubu Dari Cif,Baffa Kabiru ya Umarci Liman Daya bada auran Daddy shi ne Uban ango shi ya karbi Auran Sajida Kabir Hamisu Dukku Yayinda Daddy ya Karban ma D'ansa Imran Abubakar Malami auranta kan Sadaki Dubu Dari lagadan ba ajalan ba. Lokacin da aka Tabbatar da Daurin Auran sai da Imran yaji kansa ya Saramai Bakinciki kamar yayi kuka Babban Ci bayane ma ace an Taba Daura mai aure da wannan Yarinyar Har Abada bazai manta da wannan Ranar a Sahun Ranakun bakincikinsa ba. Bazai iya Zama acikin masallacin ba Shiyasa ya Fito ya saka Takalmi kenan sai ga Sagir ya Fito rikosa yayi ganin Mutane Tundaga Ciki suna ta gaisawa dasu Abba kowa na Wurga idon ganin Ango Yusuf ne ya Hangosu Daga Waje ya nunasa nan fa Mutane ke ta zuwa da sun zo suna kokarin mikama Imran Hannu sai ya Kara Hade rai ya Kauda kai Hannayensa na Goye a bayansa ko Fito dsu bai yi ba Sagir ya bari da karban Musaban yana kuma amsa Fatan Alherin dinsu. Da kafarsa yake zungurin Imran Wanda ya wani Dauke kai kamar ma baisan me ya aikata ba Mutane sun zata ma Sagir ne ango Imran abokinsa wasu Da dama sun tafi da Fadin kai Abokin angon nan bai da Fara"a Ko kadan shi kuma ko ajikinsa Domin tsayuwarsa a wajen ma ba karamin Takura bane ga Rayuwarsa yau Darajan Abba kadai akaci da ko Sama da kasa zasu hade bai ga Uban Daya isa yayi mai abunda akayimai yau ba. Gajiya da Zungurinsa da Sagir yake yayi ya Wurgamai Harara yana Fadin"Mallan Lafiya..? Kafa isheni ka mtsamin Kafin na Sauke bacin Raina akanka Wlh yanzu ka tsinci kanka cikin wannan Kwalbatin Dake gefenmu..! Imran ya Fada yana Nunamai kwalbatin da baki Sagir ya juya yana kallon Kwalbatin cike da kwata da Sauri ya matsa Yabar Kusa da Imran din Saninsa Wlh zai iya aikata Abunda ya Fada Mirmishin Fatan baki Imran ya saki Kafin murya kasa kasa yace"Better for u..! Hararansa Sagir yayi saboda yajisa Kafin yace"Kaifa baka da Mutumci Daman na sani..Kana ta wani cin mgani Gata Daada tayi maka ta aura maka wannan Santaleliyar Budurwa batare da ko sisinka ba ya kamata ma ka Gode mata ne ba wai kazo kana wani Daure Fuska kana wani yamutsa Fuska kamar kaga kashi ba..! Imran ya kallesa galala irin kallon Are u Mad..? Karkace kai yayi yana Fadin"Nace tamin gatan ne..?Ko Daadan Uwata ce..? Yafada yana Tsatsare Sagir da Mayun Idanuwansa Cikin mamaki Sagir yace"Ikon Allah Ita Daadan..? Cikin Takaichi ya saki karamin Tsaki yana Fadin"Eh ita ai ba uwata bace..Bani ta Haifa ba bata da wani iko akaina..Abba ne Da'nta meyassa shi batayimai gatan ba..? Ai naga shima bai da mata dashi tama wannan gatan bani ba..Kuma Duk Cikin Tarin Jikokinta sai ni ta Zaba..!Wato nine Maraya Uwata ta mutu Dole a Dinga Walagigi da Rayuwata to ban Dauka ba Wlh..Koda nayi Rashin Uwa baisa na Rasa kimata ba nasan Darajan kaina da Mutumcina saboda Haka ni Daada batamin gata ba wlh sai ma Kokarin Takurama Rayuwata Datayi kada ka kara cewa wai Daada tamin gata ni ban gani ba kai koma gatan tamin ban gode ba domin ban ce ina Bukata ba..! Ya Karishe Fada a Fusace kafin ya Tada Iska ya wuce Fuu kamar zai Bangaji Sagir yayi Saurin mtsawa yana Binsa da kallo kafin ya Girgiza kai yana Fadin"Kin auri aiki yarinya..Imram..Imran ba kanwar Lasa bane..! Fitowa kawai su Abba sukayi basu ga Imran ba Sagir yace ya wuce gida suma Daganan gidan suka Wuce Tare da wasu Mutane saboda Walimar da sukace zasu suyi. Suna zuwa Haraban gidan suka iske Imran na saman Motan Yusuf yana ta Busa Sigarinsa ya Cire Rigar jikinsa Daga shi sai Vest ya kwabe Hula wai ta Damesa,Sai da yaga Abba ne yaji kunyar Ya Saki Taban ta Fadi kasa ammh ko ganin Baffa Kabiru da Khamis ba sa ya Fasa Abunda yake yi ba,Baffa Kabiru da Khamis Takaichi Duk ya Cikasu na ganin irin Mijin da Sajida ta aura Mutum Har Mutum ammh ba kyan Hali haka Khamis ke Fada acikin Ranshi. Abba ne ya mikama Imran din hannunsa yace ya bashi Kwalin Sigarin da makunninta kafin ya Sabamai Dole baida yarda zai yi ya saka Hannu acikin Aljihun wandon Dake Jikinsa ya Dauko Duka ya Mikama Abba ya karba yana nuna ma Daddy,Kai kawai suka Kada acikin Ransu suna Fatan Allah ya gyara Kayanshi Domin shiriya tana wajen Allah ne. Ganin haka yasa Imran bai Tsaya ba ya Kwashi Rigarsa da Hulansa ya wuce Cikin Gida yana wannan Takun nasa na Sassarfa afalo yaci karo Dasu Basheer su Sagir gasu Inna Maimunatu suna ta Hayaniya jin an Daura auran Sadaf sadaf ya wuce kafin a gansa ya shige Dakin da suka Sauka shida Sagir ya Rufo kafa Gabadaya ya Kwabe wandon Jikinsa Da Vest din ya Rage dagashi sai Boxers ya haye gado ya kwanta bayan ya kunna Fanka Zafi duk ya ishesa Yana jin karkashin Zuciyarsa na wani kuna Bini Bini ya saki Tsaki kamar wani Tsaka. Achan Falo kuwa Tunda Labarin Daurin auran yazo Cikin Gida Mami Asma"u ta shige Daki tana ta Rizgan kuka yanzu Shikenan Tsagerin yaron nan yayi nasara akanta ina bazai yuyu ba Tunda aka nuna mata iyakarta itama sai ta nunama kowa nata iyakar Sai a Dauki Sajidan akaimai Tagani Indai Tana Raye ba wanda ya isa. Sai da taji kukanta ta gaji kana taje tayi wanka ta Shirya Fuskarnan duk ta Kumbura ba wanda yabi ta kanta su Umma duk suna Falo ana ta Hidima Bata ga ko Daya Daga Cikin ya"yanta ba,Sajida Tana Dakin Daada Umaima tana Tare dasu Munari Khamis kuma suna Haraban Gidan inda suke Walimar su nacin Abinci isu isu da sauran Mutane an Shimfida manyan Dardume suna zaune suna cin Abinci ga ababen sha nan Birjit sai wanda ka Zaba Imran ne kadai bashi a wajen kuma ba wanda ya Damu Dashi Sanin Halinsa. Bangaran Amarya Sajida kuwa tana jin Gudan Inna Maimunatu Tana Fadin an Daura aure taji wani sukuni Tare da Salama ya Shigeta,abaya kafin Taga Imran tasha Mafarkin yadda Kayattacen Bikinta zai bar Tarihi a Nageria sai dai ganin Imran da Faruwar komai ya Sauya
Chapter 108 · 0% Book details