← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 190

Sashe 29

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mama Har kan makeken Gadon Yusuf ta ZAunar da ita bayan Tayi mata addu"a da yar Nasiha ita da Yusuf kana Tayi musu Sallama Tace Zata tafi Yusuf yace zau kaita Gida tace ya Barshi, yayi Zamansa Sai dai yaki jinta Sai da ya rakata Har Bakin get yana mata Godiya kana ya koma Cikin Gida ita kuma ta gangara Zuwa Gida acikin Ranta Tana addu"am Allah yasa Sanadiyar Safiya Chanji mai Girma ya Faru a wannan Gidan
Tafiyanta ba Dadewa sai ga Munari ta Dawo mai Napep ya Sauketa ta Sauka ta Bashi kudinsa ta Buga get Iro ya leko ganinta yasa ya Bude mata karamar Kofar ta ahigo yana mata Sannu da zuwa Bakinsa Cike da gulmar Shigarsu Mama da Safiya da Fotowarta ita kadai sai dai bai samu Fuska ba a gajiye take Ga yunwa ga Wahalan makaranta.
Tana Shigowa Falon dakin Abba ta Wuce Direct ta iskeshi Yana Sallah Kanta ta Dafe ta fice Zuwa Dakinta tasan Ya Yuauf ya Dawo Tundaga Motarsa,Yau tayi Dare Tun Dazu suka Tashi Ta tsaya Amsan Note ne wajen Classrep dinsu,Sai kuma Data Fito Bata Samu Abun Hawa da Wuri ba.
Dakinta ta yada Zango,Tiolet ta wuce Tayi alwala Tazo Tayi Sallar Tana Idar ta Fito Zuwa Kitchen ta Duba Flaak taga Da akwai Ruwwn Zafi sai ta Samu karamin Mug,ta Zuba ta Fito Zuwa Saman Dinning ta Fara Hada Tea sai ga Yusuf ya Fito Kamar zai Fita Cikin Hanzari da Sauri ta saka baki ta Kira sunansa ya Juyo yana kallonta Kafin yace"Munari yaushe kika Dawo..?
Ta Dauko mug din ta Nufoshi Take Fadin"Yanzu..Na shiga wajem Abba naga yana Sallah..naga Motarka sai nayi Tunanin kana cikin Dakin ka ne..!
Yusuf yace"Yauwa..Gwara ma da kika Dawo..Gama Shan Tea din nan ki Shiga ki Zauna da Safiya..!
Munari ta kallesa Sakaka kafin tace"Wata Safiyan kuma Yaya..?
Kansa ya Dafe kafin yace"Kash..Is a Long Story..Atakaiche dai Matatacce Dazu aka Dauramana aure...Ayanzu hakama Tana Dakima..Ki Zauna da ita Zan je na Dawo..!
Munari mug din Hannunta ya kusa Subuce mata Cikin Mamaki tace"Anty Safiya ce matarka Ya yusuf..? Am so Comfused how Comes..?
Kai ya gyada kafin yace"Lilsiy..Ki bar wannan mganar zamu yi ta Daga Baya..Yanzu dai juz go..!
Munari tace"Oly..To dafa abinci zan Doramana kaga Tun Safe bana nan kuma Abba bai ci komai ba..!
Yusuf Daya kosa da mganarta ya kama Hanyar ficewa yana Fadin"Who tell u..?Zan yo mana Takeaway in zan Dawo..!
Munari tace"to ina shi Ya Imu..?
Karamin Tsaki yaja ya fice yana Fadin"Check him..In his Room mana..!
Daga Haka yafice Lokaci Daya yana Laluban key din Motarsa.
Tsalle Munari ta Dakata bata ma Tsaya Shan tea din ba ta maidashi Saman Dining ta Fada Dakin Abba ta Iakeshi ya Idar da Sallah yana Azkar Rumgumesa Tayi ta baya tana Murna da Ihu yana jinta yasan ta samu Labari Allah Sarki.
Shi Munari ta Tasa da Tambaya sai da ya gamayata yadda Yusuf ya gayamai da Abunda ya wakana,Munari Ta Washe baki ta Mike Tana Fadin"Wlh mu muna sonta Abba..Indai zata Zauna Damu..Zamu zameta komai da komai ko Abba..?
Kai ya gyada mata yana Jan Cashaba Lokaci Daya yana Fadin"Da yardan Allah..!
Ficewa Tayi tana Fadin"Abba Let me Met my Sister Inlow For d First time..!
Tafice ya Bita da kaallon Tsausayi Munari mai son Mutane ne ya Tabbata Batajin Dadin Zaman da sukeyi Daga ita sai yan"uwanta acikin Gidan nan

Safiya na Zaune inda Mama ta Zaunar da ita Har yusuf ya Fita ya barta bata Motsa ba Duk yace ga Tiolet nan ta Shiga Tayi Alwala Tazo tayi Sallah kafim ya Dawo ammh ta kasa Tashi Abubuea ne ke Dawomata Daki Daki.Na yarda auranta ya Faru kamar almara Allah Sarki mommy,ta Tuna Sadda take kuka tana Rike ta Tasan Laifin Abun su ne da Ta Mommy ce bazata bari ayi haka ba,Anfi karfinta ne Tuna Haka yasa ta Dauko Wayarta Dake Jikinta ZAta kira Mommy sai ta iske Missed call dinta ba adadi Jikinta na Rawa ta Bi bayan kiran,kira Daya taji an Daga kiran lokaci Daya Taji Muryan Tasleem da Mommy alokaci Daya suna Tambayanta ina ta Shige ne suna ta kiranta bata Daga ba.
Safiya taji kuka ya kawo mata Cikin kuka tace"Ina Gidansu Yusuf Mommy..Wayata Tana Silent Banji ba..!
Tasleem ta Saka kuka itama Tana Fadin"Anty Safiya..Nadawo naji Abunnda Abbu ya aikata Miki..Nayi kuka Mommy ma sai kuka take Kuma munso mu Boyoki Abu ya hana yace ba yanzu ba..!
Safiya na Sharan majina tace"Kada ki Damu Ina nan lafiya Safiya..Kuma Zaki zo inda nake Abbu zai barki kizo Insha Allahu..!
Tafada Tana Sharan kwallah kafin Tasleem din Tayi mgana Mommy ta karbe Wayan Tana Fadin"Safiya zan zo na Tafi Dake..Bazan yarda da wannan auran ba..!
Safiya na Zubar kwallah tace"A"a Momny kada ki yi abunda Abu zai Yimiki Abunda mu bazamu mu manta ba ....Kinsan Halinsa fa kiyi Hakuri Insha Allahu ba Mtsala..Gidan Maman Abokin Kaninsa suka kaini Ba Dadewa yusuf dun yazo ya Daukeni zuwa Gidansu ita Maman abokin Ta Rakoni zuwa Gidansu Yusuf din..Mommy kada ki Damu ki barni nayi Zaman aurena Abba mahaifin Su Yusuf yace min kamar ya nake garesa zai rikeni kamar yar daya Haifa ta Cikinsa..!
Mommy ta Sauke Numfashi kafin tace"Shikenan..Ammh bazan yarda ya aurar dake a wulakance ba..Sai na kwatan miki yancinki..Ki rika barin wayarki kusa Dake zamu Dinga kiranki..!
Ta Bude baki Zatayi mgana kenan Munari ta Shigo Dakin Tana Fadin"Hello Bhabi..!

*Shakira...*
3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

          *🅿�12*
Chapter 29 · 0% Book details