← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 134

Sashe 99

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta É—aga kanta ta kalleshi ta ce "Wai dan Allah me ka ce masa ya fasa?"

Raihan ya yi murmushi ya ce "Dubu É—arin da ya ce zai baki kuÉ—in aure, na bashi uku, na ce aje a mayar da wadda aka saka a kula da iyali na gida, ya bar mini ke, jikinsa na rawa ya bar mini ke, dama na gaya miki na fi kowa sonki" yayi maganar yana haÉ—a fuskar sa da ta ta yana murmushi.

"Cin hanci ka bashi dan ya bar maka ni, cin hanci ba kyau"

"A nan ya halarta" yayi maganar yana dariya.

Raihan na ƙoƙarin ɗaukar su zuwa wata duniyar, wayarsa ta fara vibrating, sunan mami ne a kan screen ɗin wayar, ya ɗaga tare da yin sallama.

"Raihan har ka fi ƙarfin ka zo in da nake ka gaishe ni ko?"

Ya san a rina, ya kwantar da ummi a jikinsa sannan ya ce "A'a ba haka bane mami, zan zo ne"

"Zaka zo sai yaushe? Har an yi ƙulle-ƙullen da zaka kasa zuwa ka gaisheni?"

"Mami, wallahi a gajiye nake ne sosai da sosai, na kira ki ma da safe baki ɗaga ba, but an ce mini gida haryanzu da mutane, na ce bari na ƙyale ki, sai da daddare, amma in sha Allah a satin nan dole na  na zo gaishe ki, na gaji ne sosai....

"Dalla rufe mini baki, nusari shashasha. Yaushe aka yi daren da gari zai waye?  Lallai lallai ka zo gida ina son ganinka, yarinyar nan safiyya ma na kwance babu lafiya duk saboda kai, kar ka bari ka fusata ni"

Raihan bai yi mamaki ba, ya san a rina, amma shi bai ga haÉ—in rashin lafiyar safiyya da shi ba, asibiti zai kai ta ko me zai yi mata? Kodayake ba abun mamaki bane ba idan mami na jin rigima.

"Shikenan mami, zan zo in sha Allah" sai dai tun da aka ambaci Safiyya, yana jin yadda bugun zuciyar ummi ya ƙaru a ƙirjinsa.

Ya saka hannu ya ɗagota, amma taƙi kallonsa.

"Sweetheart, an fara kiran sallar magariba, bari na yi alwala na tafi masallaci" ba ta kula shi ba, ta tashi ta nufi É—aki, ya bi bayanta da kallo, zubin manyan mata sosai.

A hankali ya ce 'Haba mami, is too early for that'.

Bai je kiran mami a ranar ba, dan ya san idan ya je da mutane a gidan, kuma sai ta yi wani abun da zata ci mutuncin ummi, a gaban mutane dan haka ya ƙi zuwa.

Kwanan ummi uku a gidan raihan, ta fara girkin abinci, sai dai rigimar raihan har mamaki take bata, baya zuwa ko ina sai salla, yana maƙale da ita kamar cingam, ga wani irin mugun kunyarsa da take ji, ta kasa sakewa da shi, kusan kullum cikin ƙorafin saka hijjabin nan yake, ta kasa daina yawo da hijjabi.

Kwana na ukun da daddare, Raihan ya je gida, sai da ya je wurin Hajiya yayi mata bangajiya, Alhaji dama baya nan, washegarin É—aurin aure ya tafi umara.

Sai dai cikin fargaba ya isa sashin mamin.

Ya tarar da ita ta hakimce, gefe ga Nihal a zaune, sai Safiyya da ke kwance a kan doguwar kujera.

Yana shiga suka gaishe shi, ya amsa musu, sannan ya je gaban mami ya risuna yana gaisheta.

"Sai yau Allah ya nufe ka da zuwa? Har ka sallami kanka na yi maka waya ka zo raihan amma ka ƙi"

"Ba ƙi na yi ba mami, wallahi bana iya zuwa ko ina, zirga-zirgar bikin nan na gaji ne wallahi"

"Uwar zirga-zirgar bikin, ka fito fili ka faɗi uban abun da ya hanaka fitar, na yi dana sanin cewa zan yi maka aure ina ganin mafita ce, ashe ruwan dafa kaina ne, ka kwaso bazawara da ta tafi ƙarfin ka, wallaahi ka shiga hankalinka, ka san abun da yake yi maka ciwo"

Ta din ga yi masa faɗa na babu gaira babu dalili, ƙarshe ta rufe da cewar, watanni uku ta bashi, yazo ya nemi auren Safiyya.

Ya ji ta da kunne kawai, ta gama ya ce zai tafi, ta ce ba zai tafi a lokacin ba.

Ummi kuwa na gida na ta duba agogo, dan be gaya mata zai je wani wuri ba.

Har ƙarfe goma saura shiru bai dawo ba, ta kasa jurewa ta kira wayarsa.

Bai ji nauyin mami da ke zaune tana kaɗa ƙafa cikin isa ba, ya ɗaga wayar ya ce "Hello dear".

"Ina ka tafi tsoro nake ji"

Yayi murmushi ya ce "Gani nan, babu dodo a gidan fa"

"Dan Allah ka yi sauri, tsoro nake ji sosai ko falo na kasa fita".

Mantawa yayi da mami a wurin, yayi dariya ya ce "To yi ta addu'a kan na dawo? Kin ci abinci ne?"

"A'a"

Ya ce "But you are not hungry ko?"

Ummi ta ce "Eh"

"Ok ki jirani, in sha Allah yanzu zan taho"

Muryar mami ta jiyo tana cewa "Zaka ajiye wayar nan ko sai na ci ubanka mara kunya" a rikice gaban ummi ya faÉ—i, ta kashe wayar ba ta san gidan ya je ba da ba zata kira shi ba.

Mami ta tashi ta shiga É—aki, raihan ya É—au mukullin motarsa ya fice da sauri.

Abun da raihan yayi, ba ƙaramin mamaki ya bawa mami ba, dan mugunta ta shirya yi, ta zaunar da shi har sha biyun dare, daga nan ta ce dare yayi ba zai fita ba sai da safe, bisa ga miyagun shawarwarin da Anty rakiya ta bata, sai dai abun da raihan ɗin yayi ya bata mamaki.

Ta din ga kiran wayarsa amma a kashe.

A bedroom ya tarar da ummi, kai da ganin ummi ka san a tsorace take, ya ajiye kayan hannunsa ya ce "Sorry dear, yi haƙuri"

"Ban haƙura ba" ta yi maganar cikin shagwaɓa.

"Yi haƙuri, ayi mini afuwa" ba ta nuna masa ta san in da ya je ba.

Ya cika cikinsa da abinci, yana ta yabonta tare da santin abincin.

Ya koma ya hana ummi sukuni, ya gama tara mata gajiya, suna kwance babu tsammani ta ji ya ce "Salma, me ki ka yi wa mijinki na farko ku ka rabu?"

Gyara kwanciyar ta tayi, ta ce "Meyasa ka tambayeni?"

Ya kalli fuskarta ya ce "Am just curious about it"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Labarin babu daÉ—i, auren huce takaici aka yi masa da ni, saura kwana uku aurensa, ba ya so na, ranar da ango ya tare a tsakar gida na kwana cikin ruwan sama, ba ya so na, tuntuni ni mummuna ce kuma ya rasa wadda yake so yayi niyyar aure. Auren watanni biyu ne dai bai kai uku ba ma, watanni mafi tashin hankali, marasa daÉ—in tunawa, na tozarta sosai a aurena na fari ko tunawa bana son yi" tayi maganar tana zubar da hawaye.

Ya rungumota jikinsa yana share mata hawayen, ya ce "Is ok, you are much more than special, ke ta daban ce, kuma ya yi wa kansa, ni kuma ya taimakeni irin sosai ɗin nan fa" yayi maganar yana ƙoƙarin zolayarta.

Da safe da ya kunna wayarsa, da kiran mami ya fara cin karo, ya ɗaga ta ƙare masa zagi tsaf, amma ko a jikinsa, shi kasancewar sa da ummi, mantar da shi komai yake yi. Duk da kunyarta har ta yi yawa.

Abu kamar wasa, raihan ya shafe sati biyu cirr a gida, ummi ba ta da aiki sai É—orawa da saukewa, abokan aikinsa su ka zo ummi ta yi musu girki, har da Æ´an china.

Raihan ba ya jin duk wanda zai zo gidansa, saboda matarsa ta iya girki.

Haka zalika ga rigimarsa da ba ta ƙarewa.

Gidan farida kuwa, tun da Allah ya sa ummi ta bar gidan, komai ya taɓarɓare, kausar mugun sok jiki, ba ta iya aikata komai, noor ce ma mai ƙoƙartawa, ita ma idan ta gaji, sai ta watsar da aikin ta ce ta gaji, idan aka tursasata kuma, tayi abun da ba a so.

Uban wankin da ummi ke yi musu, babu wanda zai yi yanzu, mopping gyaran É—aki, da kuma girki duk abubuwan sai a hankali, girkin ma ba daÉ—i yake yi ba.

Farida ta ce sai an samo Æ´ar aiki, dr. Ya ce babu mai kawo masa Æ´ar aiki, idan aka kawo ta kuwa sai dai ta din ga biyanta, babu yadda za ayi ga kausar a gida, ba aure ba karatu, ace an É—aukko Æ´ar aiki.

Dr. Ya kira ummi ya tambaye ta me take so ayi mata da kuÉ—in sadakinta, ta yi tunanin wata sana'ar, ya bata jari sauran ya cika ya saya mata kadara.

Ummi ta tuntuɓi raihan, amma ya ce a wannan lokacin, ba ta buƙatar sana'a a saya mata kadara kawai.

Duk yadda mami ta so yin abun da za ta ƙure raihan, ta shiga hakkin ummi, raihan sai ya zille, ta yi masa faɗa ta zage shi, ko a jikinsa.

Babban abun da ya ba ta takaici, bai wuce tana tsaka da duba saƙonni, ta ga raihan yayi status da special whats app ɗin sa, da ba kowa ne ya san shi da shi ba, galibi family ne kawai ke da lambar.

Hoton Ummi ya saka, tana zaune a kan dining, ta naÉ—e kanta da mayafin doguwar rigar jikinta
"My perfect woman, khairun nisa'i, Allah ya ƙara miki lafiya"

Ya sake rubuta "Goodnight Æ´ar aljannata"

A fili ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, bazawarar wannan mummunar"

Hankalin Safiyya ne ya koma kan mami, dan kuwa mami ta sanya safiyyan dawowa gidan da zama.

"Mami menene?"

Ta miƙa mata wayar, bayan ta nemo status ɗin raihan.

Gaban Safiyya ya faÉ—i, duk yadda ake koÉ—a munin ummi bai kai nan ba.

Mami ta din ga zage-zage, tana cewa an asirce mata É—a.

Sai da ta jera kwana biyu tana kiransa ya je tana nemansa, amma ya ce mata ai aiki yayi yawa a office, baya samun isasshen lokaci, alhalin rabonsa da office É—in tun saura sati biyu bikinsa.

Asabar ce suna baccin safe, kiran Alhaji ya tashe su, raihan ya É—auka cikin jin nauyinsa.

"Ango ka sha ƙamshi"

"Alhaji ka dawo kenan?"

"Eh na dawo, baka nema na ko?"

Raihan ya ce "Haba dai wane ni"

"To yaya Æ´ar tawa?"
Chapter 99 · 0% Book details