← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 134

Sashe 57

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Saturday ce, dan haka ba su haÉ—u da raihan ba sai waya.

Da yamma Abdul ya É—auketa a motar da dr. Ya saya ya ajiye musu saboda zuwa makaranta ko unguwa.

Katafaren shago ne, na kayan kitchen da furnitures, manager wurin ya yi wa ummi tambayoyi, Abdul ya sanar masa ummi degree ne da ita, yanzu suna jiran result ne ma.

Manager yayi murna ganin tayi kalar haƙuri sosai da sosai.

Ya ce mata wurin sabon buÉ—ewa ne, dan haka salarynta dubu goma sha biyar ne.

Abdul ya raina dubu sha biyar, ya ce za su je su yi shawara, suna tafe yana mita, ya ce "Yaya ummi ki yi haƙuri, zan samo miki wani wurin in sha Allah, amma wane irin 15k kamar wasan yara"

"Dan Allah yaya Abdul ka barni ina so, ko dubu biyar ce zan yi"

Ya kalleta ya ce "Haba ummi, you are degree holder fa, kuma a cikin 15k har ki yi kuɗin mota da buƙatu?"

"Eh zan yi in sha Allah, Allah ya sanya mata albarka"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Amin, bari sai na kira su na gaya musu, na ji yaushe zaki fara zuwa"

"Yauwwa yaya Abdul, na gode sosai da sosai"

Yayi murmushi ya ce "Sai ka ce na baki kyautar wani abun, Allah ya taimaka".

Suka je gida tana ta tunanin da wa zata yi sharing wannan abun farincikin, na samun aiki, ita ba ƙawaye ba, kuma ba abokin hira ba, tayi tunanin ko ta gaya wa raihan, amma sai ta ga hakan kamar ta zaƙe, dan haka ta share shi bata gaya masa ba.

Ranar litinin, ta ga kiran wayar raihan ya zo su tafi, wanda ranar zata je ta yi sallama da Æ´an wurin aikinsu, ta fara zuwa wancan kanti na furnitures.

Tun da ta nufo motar yake kallonta, sannu a hankali, tafiyar ma cikin nutsuwa da yanga take yin ta.
Maimakon ta shiga ta zagaya ta in da yake zaune ta ce "Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau, ina shirin aikin?"

"Sai 9 zan je idan Allah ya kaimu, zan yi musu sallama, na samu aiki a wani sabon shago, MIKIYA GALLERY, can zan koma zuwa"

Yayi shiru yana kallon ta, ya ɗan rausayar da kai ya ce "Rashin muhimmancin nawa har ya kai abu ya faru ki ƙi gaya mini?".

"A'a ba haka bane ba, abun ne bai tabatta da wuri ba"

"Shikenan na gode, Allah ya taimaka" yayi maganar ransa a haÉ—e.

"Raihan haushi ka ji, walla....

"Shhhh, na fuskanci na fiye shishshigi, am sorry" yayi maganar yana kunna motar.

Ummi ta yi saroro ta kasa magana, ba ta son ace tayi laifi a rayuwarta, mussaman raihan da yake ta É—awainiya da ita, ba ta zaci za ji haushi ba.

"Matsa zan ja motata"

A hankali ta ja da baya, ya ja motar, yana kallonta ta mirror, ta tsaya kamar sokuwa tabi motar da kallo.

A hankali ya furta 'Lets see, if it will works'

Jiki a sanyaye ta din ga gudanar da al'amura ranar.

Ta je sabon wurin aikinta, sai dai hankalinta baya jikinta, ta din ga kiran wayar raihan, amma yaƙi ɗagawa.

Whats app ta koma, ta yi masa message nan ma bai amsa ba, sai dare sannan ya kirata.

"Raihan dan Allah ka yi haƙuri, ban san zaka ji haushi ba, ka yi haƙuri mana".

"Yaya ummi ba sai kin bani haƙuri ba, laifina ne da nake yi miki shishshigi, duk da yanayinki na rashin son mutane".

"A'a ba shishshigi ka ke yi mini ba, ka yi haƙuri mana"

Ya wani hura hanci ya ce "Ok, Allah ya taimaka".

Ta ce "Yauwwa na gode, zan din ga gaya maka abu idan ya faru"

Ya ce "Promise?"

"In sha Allah "

"To shikenan, abu na daɗi ko akasin haka, kar mu ɓoyewa juna"

Ummi ta ce "To"

"Good dear, gobe in Allah ya kaimu zan zo na ga wurin"

Tayi murmushi ta ce "To Allah ya kawo ka"

"Amin, goodnight" suka yi sallama tana jinjina daru irin na raihan.

Status take kallo, ta kai kan status ɗin raihan, yana tsaye a gym, ya tsaya a jikin mudubi yayi hoto, daga shi sai gajeren wando, ya ɗaga wani ƙarfe jijiyoyin jikinsa duk sun ɗaga, ga cikinsa ya rabu kashi shida
(six packs) ga ƙirjinsa kwance da gashi har saman cikin sa.

Tayi reply da "Babban mutum meye haka?"

"A ina?"

"Ka saka hotonka babu kaya, ba mutunci a haka, dan Allah ka cire"

Ya amsa mata da "Ai ni ba mace bane"

"Duk da haka, manya ba sa haka, a cire dan Allah 🙏"

Yana daga kwance yake murmushi, ya ce "To shikenan, an gama babbar yaya, in sha Allah ba zan sake sakawa ba".

"Yauwwa babban mutum, Allah ya yi albarka ya kula da rayuwarka"

"Amin ya rabb yayata, godiya nake Allah ya kula mini da ke"

"Amin tare da kai" ta ajiye wayar tana murmushi.

Washegari har shagon ya je ya tarar da ummi, sai dai ya ji daÉ—in ganinta a kauwwame a wuri É—aya, ba wani aiki take na wahala ba.

Ya samu wuri ya zauna suka gaisa da manager, ya hau yi wa ummi hira.

Da farko a É—an tsorace take, ko manager zai ce tayi laifi, amma yaga bai ce musu komai ba, har lokacin tasinta yayi, yana wurin.

Da suka fito ya kalleta ya ce "Wai nawa zasu din ga biyanki ne?"

Cikin murna ta ce "Dubu sha biyar duk wata"

"Me?"yayi maganar yana yatsune fuska.

"Dubu sha biyar" ta maimaita masa.

"Share-share zaki din ga yi ne? Ki zo ki wuni a dubu sha biyar, duk girman shagon nan dan son kai".

Ummi ta waiwaya ta ga babu wanda yake jin su ta ce "Kayi a hankali, dubu sha biyar ina laifi, da waye ya bani?".

"Degree holder da aikin dubu sha biyar a wata, me 15k zata yi miki a wata, mussman ku mata masu tsarabe-tsarabe, ni fa a wata data da katin waya na dubu ashirin nake sawa zuwa sama" Ummi ta buɗe baki tana kallon sa, saboda abun ya ɗaure mata kai, har ya kaita gida mita yake yi, yana nanata dubu sha biyar ta yi kaɗan, tayi masa shiru taƙi kula shi. Dan in dai shariya ce ummi ta ƙware a wannan fannin.

"Ni ki ka share ko, wato idan na gaji na yi shiru?" gyara zamanta tayi tana cigaba da kallon window.

A hankali ya ce "Miskili ka fi mahaukaci ban haushi".

***
Misalin ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare, raihan da mahaifinsu, chief accountant da sauran accountants mutum biyu, lawyoyin Alhaji Tahir su biyu, sai kuma manajojinsa, zaune a wani katafaren office, ko ina fitilu kamar rana, kowa gabansa da ruwa da lemo, gefe ga flask na shayi, gaba ɗayansu raihan ne kawai yaro a cikinsu.
Ɗaya bayan ɗaya kowa ya din ga gabatar da bayaninsa n shekara a kan ɓangaren da yake jagoranta.

Suka kammala tsaf, sannan raihan ya tashi, ya yi connecting system É—in sa da projector, ya fara bayanin abubuwan da ya tattara daga bayanan su, ribar da suka samu a shekarar, ya tabbattar wa da mahaifinsu duk sun bibiyi shige da ficen kuÉ—i na shekarar, kuma sun yi dai-dai da bayanan da abun da kowane accountant yayi presenting.
Ya ware harajin da zasu biya, na ciki da wajen Nigeria, ya ware kuɗin zakka, kuɗin abun da ake rabawa ma'aikata na riba bayan albashinsu, abubuwan da suke buƙata, kuɗin duk wani abu da ya shafi sadaka da makamantansu, da kuma kuɗin umara na mutum goma, kamar dai yadda Alhajin ya umarce shi.

Tafa masa Alhaji Tahir ya hau yi, ya ce "Ƙaraminsu babbansu, am so much proud of you, ban zaci zaka iya ƙoƙari haka ba, saboda na san aikin ba ƙarami bane".

Chief accountant ya ce "Ni kaina ya bani mamaki, yayi ƙoƙari sosai da sosai, na bi duk abubuwan da yayi, kamar dai yadda ka saba ne, yayi iya yin sa, kuma da alama zai kamanta adalci kamar dai kai, sai dai rigimamme ne"

Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce "Ai na san halin kayana" suka yi dariya baki É—aya.

Suka ƙarasa tattaunawa, da bibiyar abubuwan da Raihan ya gabatar, daga bisani Alhaji Tahir ya ce kowane ɓangare su rubuto abun da suke buƙata, na gyara ko makamancin haka, raihan zai duba, shi zai je hutun taƙaitaccen lokaci.

Duk suka gamsu da abubuwan da aka tattauna, tare da yi wa Alhaji Tahir addu'a saboda mutum ne mai farantawa ma'aikatansa, dan ya ce abokan nemansa ne, bayan iyalansa ba shi da sama da su.

Dirver ya É—auke su zuwa gida, a hanya raihan ya ce "Alhaji"

"Na'am babban mutum"

"Tsakani da Allah aikin nan da wahala, kuma ko murmurewa ban yi ba, ka ce a kawo mini duba wani abu, ni fa ban san komai ba, dan Allah a kaiwa su yaya sagir, gaba ɗaya ƴan kwanakin nan saboda aikin nan, ko bacci bana yi sosai" ranƙwashin da Alhajin yayi masa ne ya sa shi yin shiru yana kallon sa.

"Kana da nasibi a kan harkar kasuwanci raihan, amma wasa da shiririta sun yi maka yawa, da aikin kashe-kashen kuÉ—i, office zan baka a head branch, a din ga baka salary"

Cikin sangarta ya ce "A'a dan Allah, shagona fa da nake ta processing, ka fa bani jari rance, ka manta, kayana sun kusa zuwa fa".

"Na sani raihan, akwai abun da nake targeting ne"

Raihan ya ce "To, Allah ya taimaka, amma ba sai na sake duba wani abun ba ko? Kuma ba sai na yi maka aikin ba ko?".

"Sai fa ka yi, gara ma ka shirya"

Raihan ya kifa kansa ya ce "Wayyo mami, dama ban dawo kano ba"

Alhaji Tahir yayi dariya ya ce "Ko ina ka tafi, i know how to deals with you, Munnir ya sangarta ka, kashe kuÉ—i kawai ka iya, baka iya nema ba" yayi maganar yana murÉ—e masa kunne.

Raihan ya É—ago da sauri ya ce "Ka tambayeshi ka ji, na sayar da agoguna, na sayar da takalma, kuma na tara kuÉ—i"
Chapter 57 · 0% Book details